English
A A A A A

Allah: [Albarka]

Luka 6:38
Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yǎ yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”

Mattiyu 5:4
Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu taʼaziyya.

Filibbiyawa 4:19
Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

Filibbiyawa 4:6-7
[6] Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe roƙenku ga Allah ta wurin adduʼa da roƙo, tare da godiya.[7] Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

Yaƙub 1:17
Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

Yohanna 1:16
Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka.

1 Yohanna 5:18
Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya yǎ cuce shi ba.

2 Korintiyawa 9:8
Allah kuwa yana da iko yǎ ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.

Filibbiyawa 4:7
Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc