A A A A A

Zunubai: [Ridda]


2 Tessalonikawa 2:3
Kada ku bar wani yǎ ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za ta zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka.

1 Timoti 4:1
Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa.

Ibraniyawa 3:12
Ku lura fa, ʼyanʼuwa, cewa kada waninku yǎ kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai.

Luka 8:13
Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya.

Ibraniyawa 6:4-6
[4] Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki,[5] waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa,[6] ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jamaʼa.

2 Bitrus 2:20-22
[20] In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijimu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko.[21] Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani saʼan nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su.[22] A kansu karin maganan nan gaskiya ce: “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”

Ibraniyawa 10:26-29
[26] Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya.[27] A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za ta cinye abokan gāban Allah.[28] Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku.[29] Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri?

2 Timoti 4:3-4
[3] Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji.[4] Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi.

Yohanna 15:6
Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yǎ bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone.

1 Timoti 4:1-2
[1] Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa.[2] Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca.

2 Bitrus 2:1
Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su-suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya.

Mattiyu 24:10-12
[10] A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,[11] annabawan ƙarya da yawa kuma za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.[12] Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za ta yi sanyi,

2 Bitrus 3:17
Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kun riga kun san wannan, sai ku zauna a faɗake don kada a ɗauke hankalinku ta wurin kuskuren marasa bin dokan nan har ku fāɗi daga matsayinku.

Yohanna 6:66
Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina binsa.

2 Bitrus 2:17
Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu.

1 Timoti 4:1-3
[1] Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa.[2] Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca.[3] Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya.

1 Korintiyawa 10:12
Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi!

Mattiyu 24:9-10
[9] “Saʼan nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan alʼummai za su ƙi ku saboda ni.[10] A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,

Mattiyu 26:14-16
[14] Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan-wanda ake kira Yahuda Iskariyot-ya je wurin manyan firistoci[15] ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin.[16] Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.

1 Timoti 1:19-20
[19] kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu.[20] Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo.

1 Yohanna 2:19
Sun fita daga cikinmu, ai, dā ma can ba namu ba ne. Don da a ce su namu ne, da sun kasance tare da mu; amma fitarsu ya nuna babu ko ɗaya daga cikinsu da yake namu.

Ibraniyawa 10:25-31
[25] Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna-tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.[26] Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya.[27] A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za ta cinye abokan gāban Allah.[28] Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku.[29] Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri?[30] Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama.” da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.”[31] Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.

Mattiyu 13:20-21
[20] Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a wuraren duwatsu kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, nan da nan kuwa yǎ karɓe ta da murna.[21] Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yǎ ja da baya.

1 Korintiyawa 9:27
Aʼa, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu waʼazi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

Ibraniyawa 6:4-8
[4] Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki,[5] waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa,[6] ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jamaʼa.[7] Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah.[8] Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin laʼana. A ƙarshe za a ƙone ta.

Ayyukan Manzanni 21:21
An sanar da su cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke zama a cikin Alʼummai cewa su juye daga Musa, kana kuma faɗa musu kada su yi wa ʼyaʼyansu kaciya ko su yi rayuwa bisa ga alʼadunmu.

Galatiyawa 5:4
Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi; kun fāɗi daga alheri.

1 Korintiyawa 6:9
Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku: Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ʼyan daudu,

Ibraniyawa 10:26
Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya.

Mattiyu 13:41
Ɗan Mutum zai aiki malaʼikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta.

2 Timoti 4:3
Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji.

2 Tessalonikawa 2:3-4
[3] Kada ku bar wani yǎ ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za ta zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka.[4] Zai yi gāba yǎ kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yǎ kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.

Yohanna 1:14
Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.

1 Timoti 4:10
(saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama), domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.

1 Bitrus 3:17
Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.

1 Tessalonikawa 2:3
Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba.

1 Timoti 4:2
Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca.

Markus 10:11
Ya amma ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki.

Luka 22:3-6
[3] Shaiɗan kuwa ya shiga cikin zuciyar Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun.[4] Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da maʼaikatan ʼyan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su.[5] Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi.[6] Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, saʼad da taro ba sa nan tare da shi.

Mattiyu 12:31-32
[31] Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba.[32] Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.

Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc