A A A A A

Rayuwa: [Yaron tallafi]


2 Korintiyawa 6:18
“Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama ʼyaʼyana, maza da mata, in ji Ubangiji Maɗaukaki.”

Yaƙub 1:27
Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne: a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.

Mattiyu 25:40
“Sarkin zai amsa, ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ʼyanʼuwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’

Yohanna 1:12-13
[12] Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ʼyaʼyan Allah— [13] ʼyaʼyan da aka haifa ba bisa hanyar ʼyan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.

Galatiyawa 4:4-5
[4] Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,[5] domin yǎ fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, don mu sami cikakken matsayin ʼyaʼya.

Romawa 8:14-17
[14] domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ʼyaʼyan Allah.[15] Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “Abba, Uba.”[16] Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ʼyaʼyan Allah ne.[17] In kuwa mu ʼyaʼya ne, to, mu magāda ne-magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.

Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc