A A A A A

Hali Mai Kyau: [Tsayawa]


2 Korintiyawa 12:21
Ina tsoro kada saʼad da na sāke zuwa, Allahna zai ƙasƙantar da ni a gabanku, kuma in yi baƙin ciki saboda waɗanda suka yi zunubi a dā, ba su kuma tuba daga aikin ƙazanta, da na fasikanci, da kuma lalata da suka sa kansu a ciki ba.

2 Timoti 2:22
Ka yi nesa da mugayen shaʼawace-shaʼawace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta.

Ayyukan Manzanni 15:20
A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini.

Kolossiyawa 3:5
Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo shaʼawa a zukatanku: fasikanci, ƙazanta, shaʼawa, muguwar shaʼawa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne.

Afisawa 5:3
Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da tsarkaka ba.

Galatiyawa 5:19
Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke: fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;

1 Korintiyawa 6:18-19
[18] Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne.[19] Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne;

1 Korintiyawa 7:2
Amma da yake fasikanci ya yawaita sosai, ya kamata kowane mutum yǎ kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.

1 Korintiyawa 10:13
Ba jarabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

1 Bitrus 2:11
Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da shaʼawace-shaʼawacen zunubin da suke yaƙi da ranku.

Ibraniyawa 13:4
Aure yǎ zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.

Yahuda 1:7
Haka ma, Sodom da Gomorra da kuma garuruwan da suke kewaye da su suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar shaʼawar jiki. Sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.

Mattiyu 5:8
Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.

Romawa 12:1
Saboda haka, ina roƙonku, ʼyanʼuwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah-wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.

Romawa 13:13
Bari mu tafiyar da alʼamuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba.

1 Tessalonikawa 4:3-4
[3] Nufin Allah ne a tsarkake ku: cewa ku guje wa fasikanci;[4] don kowannenku yǎ koya yadda zai kame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma,

Galatiyawa 5:19-21
[19] Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke: fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;[20] bautar gumaka da sihiri; ƙiyaya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya,[21] da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc