Instagram
English
A A A A A

Coci: [Diakoni]
1 Timoti 3:1-13
[1] Ga wata tabbatacciyar magana: In wani ya sa zuciyarsa a kan zama mai kula da ikkilisiya, yana marmarin yin aiki mai daraja ne.[2] To, dole mai kula da Ikkilisiya yǎ kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa,[3] ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba.[4] Dole yǎ iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yǎ kuma tabbata cewa ʼyaʼyansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace.[5] (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?)[6] Kada yǎ zama sabon tuba, in ba haka zai zama mai girmankai yǎ kuma fāɗa cikin irin hukuncin da ya fāɗo wa Iblis.[7] Dole kuma yǎ kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada yǎ zama abin kunya yǎ kuma fāɗa cikin tarkon Iblis.[8] Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba.[9] Dole su riƙe asirin bangaskiya su kuma kasance da lamiri mai tsabta.[10] Dole a fara gwada su tukuna; saʼan nan in ba a sami wani abin zargi game da su ba, sai su shiga aikin masu hidima.[11] A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome.[12] Dole mai hidimar ikkilisiya yǎ zama mijin mace guda dole kuma yǎ iya tafiyar da ʼyaʼyansa da kuma iyalinsa da kyau.[13] Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu.

Filibbiyawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus da Timoti, bayin Kiristi Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu a Filibbi, tare da masu kula da Ikkilisiya da kuma masu hidima:

Ayyukan Manzanni 6:1-7
[1] A waɗannan kwanaki, saʼad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan da suke Helenawa a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum.[2] Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba.[3] ʼYanʼuwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki[4] mu kuwa mu mai da halinmu ga yin adduʼa da kuma hidimar maganar Allah.”[5] Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci.[6] Suka gabatar da waɗannan mutane wa manzanni, waɗanda kuwa suka yi adduʼa, suka ɗibiya hannuwansu a kansu.[7] Saboda haka maganar Allah ta yaɗu. Yawan almajirai a Urushalima kuwa ya yi saurin ƙaruwa, firistoci masu yawa kuma suka zama masu biyayya ga wannan bangaskiya.

Romawa 16:1
Ina gabatar muku da ʼyarʼuwarmu Fibi, baranyar ikkilisiya a Kenkireya.

Titus 1:7
Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yǎ zama marar aibi-ba mai girmankai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba.

Ayyukan Manzanni 6:3
ʼYanʼuwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki

Yohanna 8:32
Saʼan nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ʼyantar da ku.”

Afisawa 4:11
Shi ne ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu waʼazi, waɗansu kuma su zama fastoci da malamai.

Ayyukan Manzanni 20:28
Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.

Yohanna 6:54
Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.

Markus 6:3
Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗanʼuwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ʼyanʼuwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.

1 Korintiyawa 12:28
A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, saʼan nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, saʼan nan kuma masu magana da harsuna iri iri.

Galatiyawa 1:19
Ban ga wani a ciki sauran manzanni ba--sai dai Yaƙub ɗanʼuwan Ubangiji.

Ibraniyawa 13:17
Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.

Yohanna 3:3-5
[3] Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”[4] Nikodimus ya yi tambaya, ya ce, “Yaya za a haifi mutum saʼad da ya tsufa? Hakika ba zai sāke koma sau na biyu cikin cikin mahaifiyarsa don a haife shi ba!”[5] Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.

Ibraniyawa 12:14
Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji.

Ayyukan Manzanni 6:4
mu kuwa mu mai da halinmu ga yin adduʼa da kuma hidimar maganar Allah.”

1 Timoti 3:1-7
[1] Ga wata tabbatacciyar magana: In wani ya sa zuciyarsa a kan zama mai kula da ikkilisiya, yana marmarin yin aiki mai daraja ne.[2] To, dole mai kula da Ikkilisiya yǎ kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa,[3] ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba.[4] Dole yǎ iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yǎ kuma tabbata cewa ʼyaʼyansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace.[5] (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?)[6] Kada yǎ zama sabon tuba, in ba haka zai zama mai girmankai yǎ kuma fāɗa cikin irin hukuncin da ya fāɗo wa Iblis.[7] Dole kuma yǎ kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada yǎ zama abin kunya yǎ kuma fāɗa cikin tarkon Iblis.

1 Timoti 2:12
Ban ba mace izini ta koyar ko ta yi mulki a kan namiji ba; sai dai ta zauna shiru.

Ayyukan Manzanni 14:23
Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da adduʼa da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi.

1 Timoti 5:17
Dattawan da suka bi da alʼamuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu waʼazi ne da kuma koyarwa.

Ibraniyawa 13:7
Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.

Titus 1:8
A maimakon haka dole yǎ zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse.

1 Bitrus 5:2
Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula-ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima;

Titus 1:6
Dole dattijo yǎ kasance marar aibi, mijin mace guda, mutumin da ʼyaʼyansa masu bi ne waɗanda kuma ba a san su da lalata ko rashin biyayya ba.

1 Timoti 5:22
Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki.

Titus 1:5
Dalilin da ya sa na bar ka a Kirit shi ne don ka daidaita abubuwan da suka rage da ba a kammala ba, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, yadda na umarce ka.

Galatiyawa 4:19
Ya ku ʼyaʼyana ƙaunatattu, waɗanda nake sāke shan zafin naƙuda saboda ku, sai ran da Kiristi ya kahu a cikinku,

Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc