A A A A A

Coci: [Tsanantawa da Coci]


Ayyukan Manzanni 8:1
Shawul kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu koʼina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.

Mattiyu 5:44
Amma ina gaya muku: Ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku adduʼa,

2 Timoti 3:12
Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani.

Yohanna 15:20
Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa: ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma.

Ruʼuya ta Yohanna 2:10
Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yǎ gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.

Romawa 8:35
Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi?

Mattiyu 5:11
“Masu albarka ne ku saʼad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku, saboda ni.

Romawa 12:14
Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku laʼanta.

Yohanna 5:16
To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa.

Mattiyu 5:10-12
[10] Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu saboda adalci, gama mulkin sama nasu ne.[11] “Masu albarka ne ku saʼad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku, saboda ni.[12] Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa yana a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

2 Korintiyawa 12:10
Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a saʼad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.

Ayyukan Manzanni 13:50
Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka ta da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu.

Ayyukan Manzanni 7:52
An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi— 

Markus 4:17
Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya.

Galatiyawa 4:29
A lokacin nan, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙaʼidar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu.

Markus 10:30
saʼan nan yǎ kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, (na gidaje, da ʼyanʼuwa mata, da ʼyanʼuwa maza, da uwaye, da ʼyaʼya, da gonaki— amma tare da tsanani), a lahira kuma yǎ sami rai madawwami.

Mattiyu 13:21
Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yǎ ja da baya.

Ayyukan Manzanni 22:4
Na tsananta wa masu bin wannan Hanyar har ga mutuwarsu, ina kama maza da mata ina kuma jefa su cikin kurkuku,

Mattiyu 5:10
Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu saboda adalci, gama mulkin sama nasu ne.

Galatiyawa 6:12
Waɗanda suke son nuna bijinta a fili suna ƙoƙari su tilasta muku ku yi kaciya. Dalilin kaɗai da suke yin haka shi ne don gudun kada a tsananta musu saboda gicciyen Kiristi.

Luka 21:12
“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majamiʼu, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.

Markus 10:29-30
[29] Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ʼyanʼuwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ʼyaʼya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara,[30] saʼan nan yǎ kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, (na gidaje, da ʼyanʼuwa mata, da ʼyanʼuwa maza, da uwaye, da ʼyaʼya, da gonaki— amma tare da tsanani), a lahira kuma yǎ sami rai madawwami.

Romawa 8:35-37
[35] Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi?[36] Kamar yadda yake a rubuce cewa: “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini; an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”[37] Aʼa, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu.

Ayyukan Manzanni 11:19-21
[19] To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai.[20] Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Helenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu.[21] Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.

Ayyukan Manzanni 9:4-5
[4] Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawul, Shawul, don me kake tsananta mini?”[5] Shawul ya yi tambaya, ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.”

Galatiyawa 5:11
ʼYanʼuwa, da a ce har yanzu ina waʼazin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan.

Mattiyu 10:23
Saʼad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Israʼila, Ɗan Mutum zai zo.

Mattiyu 5:12
Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa yana a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

1 Timoti 1:13
Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya.

Mattiyu 5:11-12
[11] “Masu albarka ne ku saʼad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku, saboda ni.[12] Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa yana a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

Luka 11:49
Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa, ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’

1 Tessalonikawa 3:3-4
[3] don kada kowa yǎ raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan.[4] Gaskiyar ita ce, saʼad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani.

Ibraniyawa 11:36-38
[36] Waɗansu suka sha baʼa da bulala. Waɗansu kuwa suka sha ɗauri da sarƙa aka kuma jefa su cikin kurkuku.[37] Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci— [38] duniya ba ta ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka.

Yohanna 15:20-21
[20] Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa: ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma.[21] Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba.

Mattiyu 10:21-23
[21] “Ɗanʼuwa zai ci amanar ɗanʼuwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ʼyaʼya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.[22] Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.[23] Saʼad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Israʼila, Ɗan Mutum zai zo.

Mattiyu 24:8-10
[8] Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.[9] “Saʼan nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan alʼummai za su ƙi ku saboda ni.[10] A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,

Luka 21:12-19
[12] “Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majamiʼu, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.[13] Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su.[14] Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda da za ku kāre kanku.[15] Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.[16] Har iyayenku, da ʼyanʼuwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.[17] Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.[18] Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba.[19] Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.

1 Korintiyawa 4:8-13
[8] Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna-kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku![9] Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin ƙallo ga dukan duniya, ga malaʼiku da kuma mutane.[10] Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu![11] Har yǎ zuwa wannan saʼa, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida.[12] Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka laʼanta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre;[13] in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yǎ zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

Ibraniyawa 10:32-34
[32] Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, saʼad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala.[33] Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka.[34] Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau.

Ibraniyawa 11:33-38
[33] waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki,[34] suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe.[35] Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau saʼad da aka ta da matattu.[36] Waɗansu suka sha baʼa da bulala. Waɗansu kuwa suka sha ɗauri da sarƙa aka kuma jefa su cikin kurkuku.[37] Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci— [38] duniya ba ta ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka.

Ayyukan Manzanni 12:1-19
[1] Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu.[2] Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗanʼuwan Yohanna, da takobi.[3] Saʼad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bukin Burodi Marar Yisti.[4] Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shariʼa a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa.[5] Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da adduʼa ga Allah dominsa.[6] A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shariʼa, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, ɗaure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa.[7] Ba zato ba tsammani sai malaʼikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi, ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa.[8] Saʼan nan malaʼikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Malaʼikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.”[9] Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da malaʼikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani.[10] Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Saʼad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take malaʼikan ya bar shi.[11] Sai Bitrus ya dawo hankalinsa, ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki malaʼikansa yǎ cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”[12] Da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu uwar Yohanna, wanda ake kuma kira Markus, inda mutane da yawa suka taru suna adduʼa.[13] Bitrus ya ƙwanƙwasa ƙofar waje, sai wata mai aiki a gidan da ake kira Roda ta zo tǎ ji ko wane ne.[14] Da ta gane muryar Bitrus, ta cika da murna ta gudu ta koma ba tare da ta buɗe ƙofar ba, sai ta koma a guje ta ce da ƙarfi, “Ga Bitrus a bakin ƙofa!”[15] Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, malaʼikansa ne.”[16] Amma Bitrus ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe ƙofar suka kuma gan shi, sai suka yi mamaki.[17] Bitrus ya yi musu alama da hannunsa su yi shiru sai ya bayyana yadda Ubangiji ya fitar da shi daga kurkuku. Ya ce, “Ku gaya wa Yaƙub da kuma ʼyanʼuwa game da wannan,” saʼan nan ya tashi ya tafi wani wuri.[18] Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus.[19] Bayan Hiridus ya neme shi bai same shi ba, sai ya tuhumi masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su. Saʼan nan Hiridus ya tashi daga Yahudiya ya tafi Kaisariya ya kuma yi ʼyan kwanaki a can.

Ayyukan Manzanni 9:1-14
[1] Ana cikin haka, Shawul ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist[2] ya roƙe shi ya ba shi wasiƙu zuwa majamiʼun Damaskus, don in ya sami wani a wurin wanda yake bin wannan Hanya, ko maza ko mata, yǎ kama su a matsayin ʼyan kurkuku yǎ kai Urushalima.[3] Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.[4] Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawul, Shawul, don me kake tsananta mini?”[5] Shawul ya yi tambaya, ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.”[6] “Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.”[7] Mutanen da suke tafiya tare da Shawul suka rasa bakin magana; sun ji muryar amma ba su ga kowa ba.[8] Shawul ya tashi daga ƙasa, amma saʼad da ya buɗe idanunsa bai iya ganin wani abu ba. Saboda haka aka kama hannunsa aka yi masa jagora zuwa cikin Damaskus.[9] Kwana uku yana a makance, bai ci ba bai kuma sha kome ba.[10] A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi, ya ce, “Ananiyas!” Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.”[11] Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarsus mai suna Shawul, gama ga shi yana adduʼa.[12] Cikin wahayi ya ga wani mutum mai suna Ananiyas ya zo ya sa hannuwansa a kansa don ya sāke samun ganin gari.”[13] Ananiyas ya amsa, ya ce, “Ubangiji, na ji labarin mutumin nan sosai da kuma duk lahanin da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.[14] Ga shi kuma ya zo nan da izinin manyan firistoci, don ya kama duk wanda yake kiran bisa sunanka.”

Galatiyawa 1:13
Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta.

Ruʼuya ta Yohanna 2:8-10
[8] “Zuwa ga malaʼikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta: Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai.[9] Na san wahalarka da kuma talaucinka-duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majamiʼar Shaiɗan ne.[10] Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yǎ gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.

Ayyukan Manzanni 26:9-11
[9] “Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare.[10] Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, saʼad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuriʼata gāba da su.[11] Sau da dama nakan bi majamiʼa-majamiʼa, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.

1 Korintiyawa 4:12
Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka laʼanta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre;

Ayyukan Manzanni 12:1
Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu.

Filibbiyawa 3:6
wajen himma kuwa, ni mai tsananta wa ikkilisiya ne, wajen aikin adalci bisa ga tafarkin doka, ni marar laifi ne.

Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc