A A A A A

Muguwar Hali: [Cin amana]


Mattiyu 27:3-4
[3] Saʼad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin.[4] Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.” Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”

Mattiyu 6:14-15
[14] Gama in kuna yafe wa mutane saʼad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku.[15] Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.

Markus 11:25
A duk lokacin da kuke tsaye cikin adduʼa, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yǎ gafarta muku zunubanku.

Mattiyu 7:12
Saboda haka, cikin kome ku yi wa waɗansu abin da kuke so su yi muku, gama wannan shi ne duk abin Doka da Annabawa sun kunsa.

Ibraniyawa 4:15
Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana-duk da haka bai yi zunubi ba.

Romawa 3:23
gama duka su yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah,

Tsonga Bible 1989
© Bible Society of South Africa. All rights reserved