A A A A A

Muguwar Hali: [Fushi]


Afisawa 4:26-31
[26] “Cikin fushinku kada ku yi zunubi”: Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi,[27] kada kuma ku ba wa Iblis dama.[28] Wanda yake sata, yǎ daina sata, dole kuma yǎ yi aiki, yǎ yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yǎ sami abin da zai iya raba da masu bukata.[29] Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za ta zama da amfani ga masu jinta.[30] Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa.[31] Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da fushi, faɗa da ɓata suna, tare da kowace irin ƙeta.

Yaƙub 1:19-20
[19] ʼYanʼuwana ƙaunatattu, ku lura da wannan: Ya kamata kowa yǎ kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,[20] gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so.

Kolossiyawa 3:8
Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku.

Yaƙub 4:1-2
[1] Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba shaʼawace-shaʼawacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne?[2] Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba.

Mattiyu 5:22
Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗanʼuwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗanʼuwansa ‘Raka,  ’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.

Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc