Instagram
English
A A A A A

Mala'iku da Aljannu: [Mala'iku Masu Tsaro]


1 Korintiyawa 4:9
Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin ƙallo ga dukan duniya, ga malaʼiku da kuma mutane.

1 Yohanna 4:1
Abokaina ƙaunatattu, kada ku gaskata kowane ruhu, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya.

Ayyukan Manzanni 8:26
To wani malaʼikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar-hanyar hamada-da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.”

Ayyukan Manzanni 12:15
Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, malaʼikansa ne.”

Kolossiyawa 2:18
Kada ku yarda wani yǎ ɓata ku, cewa shi wani abu ne don ya ga wahayi. Irin mutumin nan yakan nuna ƙasƙancin kai na ƙarya, yǎ kuma ce yana yi wa malaʼiku sujada. Irin mutumin nan yana kumbura kansa ba dalili, sai son zuciya irin na halin mutuntaka.

Ibraniyawa 1:14
Ashe, dukan malaʼiku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?

Ibraniyawa 13:2
Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa malaʼiku hidima, ba da saninsu ba.

Yahuda 1:6-9
[6] Malaʼikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba amma suka bar gidansu kuwa-waɗannan ne fa ya tsare a duhu, ɗaure da dawwamammun sarƙoƙi saboda hukunci a babbar Ranan nan.[7] Haka ma, Sodom da Gomorra da kuma garuruwan da suke kewaye da su suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar shaʼawar jiki. Sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.[8] Haka kuma dai, waɗannan masu mafarki suna ƙazantar da jikunansu, suna ƙin ikon masu mulki suna kuma ɓata sunan talikan sararin sama.[9] Amma ko Mikaʼilu babban shugaban malaʼiku, saʼad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi karambanin kawo zargin ɓatan suna a kansa ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yǎ tsauta maka!”

Luka 16:22
“Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma malaʼiku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.

Mattiyu 18:10
“Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku malaʼikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.

Ruʼuya ta Yohanna 5:11
Sai na duba na kuma ji muryar malaʼiku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan.

Ruʼuya ta Yohanna 19:10
Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ʼyanʼuwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”

Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc