Instagram
English
A A A A A

Arin: [Cin naman mutane]


2 Korintiyawa ৫:৮
Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji.

Luka 16:19-26
[19] “An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu launin shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum.[20] A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne.[21] Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.[22] “Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma malaʼiku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.[23] A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa.[24] Sai ya yi masa kira, ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’[25] “Amma Ibrahim, ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami taʼaziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.[26] Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’

Ruʼuya ta Yohanna 20:11-15
[11] Saʼan nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu.[12] Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shariʼa bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai.[13] Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shariʼa bisa ga abin da ya aikata.[14] Saʼan nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutan nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu.[15] Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutan nan.

1 Korintiyawa 14:34-35
[34] ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi.[35] In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace ta yi magana a cikin ikkilisiya.

Luka 1:37
Gama ba abin da zai gagari Allah.”

Yohanna 1:1
Tun fara farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.

1 Timoti 2:11-15
[11] Ya kamata mace ta riƙa koyo cikin natsuwa da cikakkiyar biyayya.[12] Ban ba mace izini ta koyar ko ta yi mulki a kan namiji ba; sai dai ta zauna shiru.[13] Gama Adamu ne aka fara halitta, saʼan nan Hawwaʼu.[14] Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi.[15] Amma mata Za ta sami ceto za su sami ceto ta wurin haihuwa-in suka ci gaba cikin bangaskiya, ƙauna da kuma tsarki tare da halin sanin ya kamata.

1 Timoti 5:3-16
[3] Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi.[4] Amma in gwauruwa tana da ʼyaʼya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.[5] Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za ta sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da adduʼoʼi dare da rana gare shi don taimako.[6] Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai.[7] Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi.[8] In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.[9] Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta,[10] aka kuma san ta sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ʼyaʼya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.[11] Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama saʼad da shaʼawar jikinsu ta kāsa ɗaurewa game da waʼadin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure.[12] Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko.[13] Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga zirga gida gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba.[14] Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ʼyaʼya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna.[15] Waɗansu dai sun riga sun ɓaude sun bi Shaiɗan.[16] In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata ta taimake su, kada ta bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.

1 Korintiyawa 11:2-16
[2] Ina yabonku saboda kuna tunawa da ni a cikin kowane abu, kuna kuma riƙe da koyarwar, yadda na ba ku.[3] To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne.[4] Kowane namijin da ya yi adduʼa ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa.[5] Duk macen da ta yi adduʼa ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta-ya zama kamar an aske kanta ke nan.[6] In mace ba ta so ta rufe kanta, to, sai ta aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace ta yanke ko ta aske gashinta, to, sai ta rufe kanta.[7] Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.[8] Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji.[9] Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.[10] Don haka, saboda wannan, da kuma saboda malaʼiku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta.[11] Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba.[12] Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake.[13] Ku kanku duba mana: Ya yi kyau mace ta yi adduʼa ga Allah da kanta a buɗe?[14] Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi,[15] amma in mace tana da dogon gashi, ai, daraja ce a gare ta. Gama an ba ta dogon gashi saboda rufe kanta ne.[16] In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata alʼada-haka ma ikkilisiyoyin Allah.

Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc