A A A A A

Allah: [Albarka]


Luka ๖:๓๘
Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”

Mattiyu 5:4
“Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.

Filibbiyawa ๔:๑๙
Allahna kuma zai biya muku kowace bukatarku daga cikin yalwar ɗaukakarsa da take ga Almasihu Yesu.

Zabura 67:7
Allah ya sa mana albarka, Da ma dukan jama'a ko'ina su girmama shi.

Ƙidaya 6:24-25
[24] “Ubangiji ya sa muku albarka, ya kiyaye ku.[25] “Ubangiji ya sa fuskarsa ta haskaka ku, ya yi muku alheri.

Filibbiyawa ๔:๖-๗
[๖] Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.[๗] Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.

Yaƙub 1:17
Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

Irmiya 17:7-8
[7] “Mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, Wanda Ubangiji ne madogararsa.[8] Shi kamar itace ne wanda ake dasa a bakin rafi Wanda yake miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafin, Ba zai ji tsoron rani ba, Kullum ganyensa kore ne, Ba zai damu a lokacin fari ba, Ba zai ko fasa yin 'ya'ya ba.

Ishaya ๔๑:๑๐
Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.

Yohanna 1:16
Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri.

Farawa 22:16-17
[16] ya ce, “Na riga na rantse da zatina, tun da ka yi wannan, ba ka kuwa ƙi ba da tilon ɗanka ba,[17] hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,

Farawa 27:28-29
[28] Allah ya ba ka daga cikin raɓar sama, Daga cikin ni'imar ƙasa, Da hatsi a yalwace da ruwan inabi.[29] Bari jama'a su bauta maka, Al'ummai kuma su sunkuya maka. Za ka yi shugabancin 'yan'uwanka, Allah ya sa 'ya'yan mahaifiyarka su sunkuya maka. La'ananne ne dukan wanda ya la'anta ka, Albarkatacce ne dukan wanda ya sa maka albarka.”

Zabura 1:1-3
[1] Albarka ta tabbata ga mutumin da Ba ya karɓar shawarar mugaye, Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi, Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.[2] Maimakon haka, yana jin daɗin karanta shari'ar Allah, Yana ta nazarinta dare da rana.[3] Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama, Yakan ba da 'ya'ya a kan kari, Ganyayensa ba sa yin yaushi, Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.

Zabura 23:1-4
[1] Ubangiji makiyayina ne, Ba zan rasa kome ba.[2] Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa, Yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif.[3] Yana ba ni sabon ƙarfi. Yana bi da ni a hanyar da suke daidai kamar yadda ya alkawarta.[4] Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa, Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji, Gama kana tare da ni! Sandanka na makiyayi da kerenka Suna kiyaye lafiyata.

2 Samaʼila ๒๒:๓-๔
[๓] Allahna, shi ne kāriyata, Ina zaune lafiya tare da shi. Yana kāre ni kamar garkuwa, Yana tsare ni, ya kiyaye ni. Shi ne mai cetona.[๔] Na yi kira ga Ubangiji, Ya cece ni daga abokan gābana. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

1 Yohanna 5:18
Mun sani kowane haifaffen Allah ba ya yin zunubi, kasancewarsa haifaffen Allah ita takan kare shi. Mugun nan kuwa ba ta taɓa shi.

Zabura 138:7
Ko lokacin da nake tsakiyar wahala, Za ka kiyaye ni lafiya, Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata, Za ka kuwa cece ni da ikonka.

2 Korintiyawa ๙:๘
Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.

Filibbiyawa 4:7
Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010