Instagram
English
A A A A A

Zunubai: [Tsinuwa]
Kolossiyawa 3:8
Amma yanzu sai ku yar da duk waɗannan ma, wato fushi, da hasala, da ƙeta, da yanke, da alfasha.

Kolossiyawa 4:6
A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.

Afisawa 4:29
Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.

Afisawa 5:4
Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don bai kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah.

Fitowa 20:7
“Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.

Yaƙub 1:26
In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.

Yaƙub 3:10
Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba!

Yaƙub 3:5-12
[5] Haka ma harshe yake, ga shi, ɗan ƙaramin abu ne, sai manyan fariya! Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake kunna wa babban jeji wuta![6] Harshe ma wuta ne fa! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata dukan jiki, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa Gidan Wuta ne yake zuga shi.[7] Don kuwa ana iya sarrafa kowace irin dabba, da tsuntsu, da masu jan ciki, da halittar ruwa, ɗan adam har yā sarrafa su ma,[8] amma ba ɗan adam ɗin da zai iya sarrafa harshe, ai, mugunta ne da ba ta hanuwa, a cike yake da dafi mai kashewa.[9] Da shi muke yabon Ubangiji Uba, da shi kuma muke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah.[10] Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba![11] Ashe, marmaro ɗaya ya iya ɓuɓɓugowa da ruwan daɗi da na zartsi ta ido guda?[12] Ya 'yan'uwana, ashe, ɓaure yana iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma, ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.

Firistoci 20:9
“Dukan wanda ya zagi mahaifinsa, ko mahaifiyarsa za a kashe shi, gama ya zagi mahaifinsa da mahaifiyarsa. Alhakin jininsa yana wuyansa.

Luka 6:28
Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu'a.

Mattiyu 5:22
Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.

1 Bitrus 3:10
Domin, “Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri, Sai ya kame bakinsa daga ɓarna, Ya kuma hana shi maganar yaudara.

Mattiyu 15:11
Ba abin da yake shiga mutum ta baka ne yake ƙazanta shi ba, abin da yake fita ta baka yake ƙazanta mutum.”

Karin Magana 18:21
Abin da ka faɗa ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karɓi sakamakon maganarka.

Zabura 109:17
Yana jin daɗin la'antarwa, ka sa a la'anta shi! Ba ya son sa albarka, ka sa kada kowa ya sa masa albarka!

Romawa 12:14
Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la'ance su.

2 Sarakuna 2:23-24
[23] Daga nan Elisha ya haura zuwa Betel. A hanya sai ga waɗansu samari sun fito daga cikin gari, suna yi masa eho, suna cewa, “Ka bar wurin nan, kai mai saiƙo.”[24] Elisha ya waiga, ya gan su, ya la'anta su da sunan Ubangiji. Sai waɗansu namomin jeji guda biyu suka fito daga cikin kurmi suka yayyage arba'in da biyu daga cikin samarin.

Mattiyu 15:10-11
[10] Ya kira taro ya ce musu, “Ku saurara, ku fahimta.[11] Ba abin da yake shiga mutum ta baka ne yake ƙazanta shi ba, abin da yake fita ta baka yake ƙazanta mutum.”

Yaƙub 3:8-10
[8] amma ba ɗan adam ɗin da zai iya sarrafa harshe, ai, mugunta ne da ba ta hanuwa, a cike yake da dafi mai kashewa.[9] Da shi muke yabon Ubangiji Uba, da shi kuma muke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah.[10] Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba!

Mattiyu 15:18-20
[18] Amma abin da ya fito ta baka, daga zuci yake, shi ne kuwa yake ƙazantar da mutum.[19] Don daga zuci mugayen tunani suke fitowa, kamar su kisankai, da zina, da fasikanci, da sata, da shaidar zur, da yanke.[20] Waɗannan suke ƙazantar da mutum. Amma a ci da hannu marar wanki ba ya ƙazantar da mutum.”

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010