Instagram
English
A A A A A

Zunubai: [Addini]


1 Korintiyawa 10:13-14
[13] Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma a game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.[14] Saboda haka, ya ƙaunatattuna, ku guji bautar gumaka.

1 Yohanna 2:16
Don kuwa duk abin da yake duniya, kamar su sha'awa irin ta halin mutuntaka, da sha'awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne.

1 Korintiyawa 15:33
Kada fa a yaudare ku! “Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.”

Yaƙub 4:7
Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku.

1 Korintiyawa 6:12
“Dukan abubuwa halal ne a gare ni,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Abu duka halal na a gare ni,” amma ba zan zama bawan kome ba.

1 Bitrus 5:10
Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku.

Zabura 50:15
Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”

Romawa 5:3-5
[3] Banda haka ma, har muna taƙama da shan wuyarmu, da yake mun sani shan wuya take sa jimiri,[4] jimiri kuma yake sa ingataccen hali, ingataccen hali kuma yake sa sa zuciya,[5] ita sa zuciyar nan kuwa ba ta sāce iska faufau, domin Allah ya kwarara ƙaunarsa a zukatanmu, ta wurin Ruhu Mai Tsarki da aka ba mu.

1 Korintiyawa 6:9-11
[9] Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,[10] ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah.[11] Waɗansunku ma dā haka suke, amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.

Titus 2:12
yana koya mana mu ƙi rashin bin Allah da mugayen sha'awace-sha'awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyar nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah,

Yaƙub 1:2-3
[2] Ya ku 'yan'uwana, duk sa'ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai.[3] Domin kun san jarrabawar bangaskiyarku takan haifi jimiri.

Ibraniyawa 4:15-16
[15] Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.[16] Saboda haka, sai mu kusaci kursiyin Allah na alheri da amincewa, domin a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari.

Yohanna 3:16-17
[16] “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.[17] Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.

Filibbiyawa 4:13
Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafa ni.

Zabura 95:8
“Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba, Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.

Mattiyu 6:13
Kada ka kai mu wurin jaraba, Amma ka cece mu daga Mugun.’

Mattiyu 26:41
Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010