A A A A A

Alamomin lissafi: [Lamba 10]


1 Sarakuna ౭:౨౩
Huram kuma ya yi kewayayyiyar babbar kwatarniya ta zubi da tagulla. Faɗinta kamu goma ne, tsayinta kuwa kamu biyar, da'irarta kuma kamu talatin ne.

Ƙidaya 11:11
Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Don me ka wahalar da bawanka? Me ya sa ban sami tagomashi a gare ka ba, da ka jibga wahalar dukan mutanen nan a kaina?

Maimaitawar Shariʼa 1:11
Ubangiji Allah na kakanninku ya riɓa yawanku har sau dubu, ya sa muku albarka yadda ya alkawarta muku!

Firistoci 20:13
Duk mutumin da ya kwana da namiji kamar yadda namiji yake kwana da mace, su biyu ɗin, sun yi aikin ƙazanta, za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu.

1 Korintiyawa 6:9-11
[9] Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,[10] ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah.[11] Waɗansunku ma dā haka suke, amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.

1 Korintiyawa ౧౦:౧౩
Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma a game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.

Romawa 1:20
Gama tun daga halittar duniya al'amuran Allah marasa gănuwa, wato ikonsa madawwami, da allahntakarsa, sun fahimtu sarai, ta hanyar abubuwan da aka halitta kuma ake gane su. Saboda haka mutane sun rasa hanzari.

Filibbiyawa ౪:౧౯
Allahna kuma zai biya muku kowace bukatarku daga cikin yalwar ɗaukakarsa da take ga Almasihu Yesu.

Zabura 55:22
Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji, Zai kuwa taimake ka, Ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.

2 Timoti ౩:౧౬
Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci,

Luka 23:34
Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri'a a kansu.

Farawa 1:31
Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai. Ga maraice, ga safiya, kwana na shida ke nan.

Zabura ౧౦౪:౯
Ka ƙayyade masa kan iyaka da ba zai taɓa ƙetarewa ba, Don kada ya sāke rufe duniya.

Farawa 6:12
Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.

Farawa 7:20
Ruwa ya bunƙasa bisa duwatsu ya yi musu zara da ƙafa ashirin da biyar.

Farawa 8:5-9
[5] Ruwa ya yi ta raguwa har wata na goma. A ran ɗaya ga wata na goma, sai kawunan duwatsu suka ɓullo.[6] A ƙarshen kwana arba'in Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi,[7] sai ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har lokacin da ruwan ya ƙafe a duniya.[8] Sai kuma ya aiki kurciya ta gani ko ruwa ya janye,[9] amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi.

Farawa 9:11
Na kafa alkawarina da ku. Daɗai ba za a ƙara hallaka talikai duka da ruwa ba, ba kuma za a ƙara yin Ruwan Tsufana da zai hallaka duniya ba.”

Maimaitawar Shariʼa 11:11
Amma ƙasar da za ku haye ku mallaka, ƙasa ce ta tuddai da kwaruruka wadda ruwan sama yake shayar da ita.

Luka 11:11
Wane uba ne a cikinku, da ɗansa zai roƙe shi [gurasa, ya ba shi dutse? Ko ya roƙe shi] kifi, ya ba shi maciji?

Ƙidaya 1:11
Amma ba a rubuta Lawiyawa tare da sauran kabilai ba,

Yoshuwa 1:11
“Ku shiga zango, ku umarci jama'a, ku ce, ‘Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.’ ”

1 Korintiyawa ౬:౯
Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,

Yohanna 1:8
Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.

Ƙidaya 10:29
Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamadayane, surukinsa, “Muna kan hanya zuwa wurin da Ubangiji ya ce zai ba mu, ka zo tare da mu, za mu yi maka alheri, gama Ubangiji ya alkawarta zai yi wa Isra'ila alheri.”

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010