A A A A A

Alamomin lissafi: [Lamba 8]


Ruʼuya ta Yohanna 13:18
Wannan abu sai a game da hikima. Duk mai basira ya ƙididdige lambar dabbar nan, don lamba ce ta wani mutum, lambar kuwa ɗari shida ce da sittin da shida.

Maimaitawar Shariʼa 6:4
“Ku ji, ya Isra'ilawa, Ubangiji shi ne Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

Firistoci 20:13
Duk mutumin da ya kwana da namiji kamar yadda namiji yake kwana da mace, su biyu ɗin, sun yi aikin ƙazanta, za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu.

1 Korintiyawa 6:9-11
[9] Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,[10] ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah.[11] Waɗansunku ma dā haka suke, amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.

Ruʼuya ta Yohanna 11:2-3
[2] amma kada ka auna harabar Haikalin, ka ƙyale ta, domin an ba da ita ga al'ummai, za su tattake tsattsarkan birnin nan har wata arba'in da biyu.[3] Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.”

Firistoci 20:27
“Namiji ko macen da yake da mabiya ko maita, sai a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu, alhakin jininsu yana kansu.”

Maimaitawar Shariʼa 18:10-12
[10] Kada a tarar da wani daga cikinku wanda zai sa 'yarsu ko ɗansu ya wuce ta tsakiyar wuta, ko mai duba, ko mai maita, ko mai bayyana gaibi, ko mai sihiri,[11] ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha'ani da matattu.[12] Ubangiji yana ƙyamar mai yin waɗannan abubuwa. Saboda waɗannan ayyuka masu banƙyama shi ya sa Ubangiji Allahnku yake korar waɗannan al'ummai a gabanku.

2 Sarakuna 21:6
Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa ya kuma aikata sihiri, ya yi dūba. Ya yi ma'amala da masu mabiya da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.

Mika 5:12
Zan kawar da maita daga ƙasarku, Ba za ku ƙara samun bokaye ba.

Ishaya 47:12
Ki riƙe dukan sihirinki, da makarunki, da layunki, Kina amfani da su tun kina ƙarama. Watakila za su yi miki wani taimako, Watakila kya iya tsoratar da abokan gāba.

Ayyukan Manzanni 8:11-24
[11] Sai suka mai da hankali gare shi, don ya daɗe yana ta ba su al'ajabi da sihirinsa.[12] Amma da suka gaskata bisharar da Filibus ya yi a kan Mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Almasihu, duka aka yi musu baftisma mata da maza.[13] Har Saminu da kansa ma ya ba da gaskiya, bayan an yi masa baftisma kuma ya manne wa Filibus. Ganin kuma ana yin mu'ujizai da manyan al'ajibai, ya yi mamaki ƙwarai.[14] To, da manzannin da suke Urushalima suka ji Samariyawa sun yi na'am da Maganar Allah, suka aika musu da Bitrus da Yahaya.[15] Su kuwa da suka iso, suka yi musu addu'a don su sami Ruhu Mai Tsarki,[16] domin bai sauko wa ko wannensu ba tukuna, sai dai kawai an yi musu baftisma ne da sunan Ubangiji Yesu.[17] Sai suka ɗora musu hannu, suka kuwa sami Ruhu Mai Tsarki.[18] To, da Saminu ya ga, ashe, ta ɗora hannun manzanni ne ake ba da Ruhun, sai ya miƙa musu kuɗi,[19] ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iko, don kowa na ɗora wa hannu, yă sami Ruhu Mai Tsarki.”[20] Amma Bitrus ya ce masa, “Ku hallaka, kai da kuɗinka, don ka zaci da kuɗi ne za ka sami baiwar Allah![21] Ba ruwanka da wannan al'amari sam, don zuciyarka ba ɗaya take ba a gaban Allah.[22] Saboda haka sai ka tuba da wannan mugun aiki naka, ka roƙi Ubangiji ko a gafarta maka abin da ka riya a zuciyarka.[23] Domin na ga kai tushen ɗaci ne, kana kulle a cikin mugunta.”[24] Sai saminu ya amsa ya ce, “Ku roƙar mini Ubangiji kada ko ɗaya daga cikin abin da kuka faɗa ya aukar mini.”

Farawa 1:24-31
[24] Allah kuwa ya ce, “Bari duniya ta fid da masu rai bisa ga irinsu, shanu, da abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu.”[25] Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.[26] Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.”[27] Haka nan fa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da ta mace ya halicce su.[28] Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya.”[29] Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da tsaba da yake bisa fuskar dukan duniya, da kowane itacen da yake da ƙwaya cikin 'ya'yansa su zama abincinku.[30] Na ba da kowane irin ɗanyen tsiro domin ci, ga kowace irin dabbar da take duniya, da kowane irin tsuntsun da yake sararin sama, da kowane irin abin da yake rarrafe bisa duniya, da dai iyakar abin da yake numfashi.” Haka nan ya kasance.[31] Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai. Ga maraice, ga safiya, kwana na shida ke nan.

1 Korintiyawa 6:9
Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,

Yohanna 1:8
Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.

Ruʼuya ta Yohanna 4:6-8
[6] A gaban kursiyin kuwa akwai wani abu kamar bahar na gilas, garau yake kamar ƙarau. Kewaye da kursiyin kuma, ta kowane gefensa, da waɗansu rayayyun halitta guda huɗu, masu idanu ta ko'ina, gaba da baya.[7] Rayayyiyar halittar farko kamar zaki take, ta biyu kuma kamar ɗan maraƙi, ta uku kuma da fuska kamar ta mutum, ta huɗu kuma kamar juhurma yana jewa.[8] Su rayayyun halittan nan huɗu kuwa, kowaccensu tana da fikafikai shida, jikinsu duk idanu ne ciki da waje, dare da rana kuwa ba sa daina waƙa, suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Ubangiji Allah Maɗaukaki, Shi ne a dā, shi ne a yanzu, shi ne kuma a nan gaba!”

Farawa 3:15
Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”

Ruʼuya ta Yohanna 13:5
An kuwa ba dabbar nan baki, tana fariya da maganganun saɓo, aka kuma yardar mata ta zartar da iko, har wata arba'in da biyu.

Fitowa 7:11
Fir'auna kuwa ya kirawo shahararrun malamai, da masu sihiri, su kuma su yi haka ta wurin sihirinsu na Masarawa.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010