A A A A A

Rayuwa: [Yaron tallafi]


1 Samaʼila 1:27
Na roƙi Ubangiji wannan yaro, Ubangiji kuwa ya biya mini bukatata da na roƙa a gare shi.

2 Korintiyawa 6:18
In kasance Uba a gare ku, Ku kuma ku kasance 'ya'yana, maza da mata, In ji Ubangiji Maɗaukaki.”

Maimaitawar Shariʼa 10:18
Yakan yi wa marayu da gwauraye na gaske shari'a da adalci. Yana ƙaunar baƙo, yakan ba shi abinci da sutura.

Hosiya 14:3
Assuriya ba za ta cece mu ba, Ba kuwa za mu hau dawakai ba. Ba za mu kuma ƙara ce da aikin hannuwanmu, ‘Kai ne Allahnmu,’ ba. A wurinka ne maraya yakan sami jinƙai.”

Ishaya 40:31
Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako Za su ji an sabunta ƙarfinsu. Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa, Sa'ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba, Sa'ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.

Yaƙub 1:27
Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.

Irmiya 29:11
Gama na san irin shirin da na yi muku, ni Ubangiji na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya.

Mattiyu 25:40
Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’

Karin Magana 13:12
Idan ba bege, sai zuciya ta karai, amma muradin da ya tabbata zai cika ka da sa zuciya.

Zabura 82:3
Ku kāre hakkin talakawa da na marayu, Ku yi adalci ga matalauta, Da waɗanda ba su da mataimaki.

Zabura 146:9
Yakan kiyaye baƙi waɗanda suke zaune a ƙasar. Yakan taimaki gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu. Yakan lalatar da dabarun mugaye.

Zabura 68:5-6
[5] Allah, wanda yake zaune a tsattsarkan Haikalinsa, Yana lura da marayu, yana kuwa kiyaye gwauraye, Wato matan da mazansu suka mutu.[6] Yakan ba waɗanda suke da kewa gida, su zauna a ciki, Yakan fitar da 'yan sarƙa ya kai su 'yanci mai daɗi, Amma 'yan tawaye za su zauna a ƙasar da ba kowa a ciki.

Karin Magana 31:8-9
[8] “Ka yi magana domin bebaye, domin kuma hakkin dukan waɗanda ba su da wani mataimaki.[9] Ka yi magana dominsu, ka yi shari'ar adalci, ka kiyaye hakkin matalauta da masu bukata.”

Yohanna 1:12-13
[12] Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah,[13] wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.

Galatiyawa 4:4-5
[4] Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari'a,[5] domin ya fanso waɗanda suke a ƙarƙashin Shari'a, a mai da mu a matsayin 'ya'yan Allah.

Romawa 8:14-17
[14] Duk waɗanda Ruhun Allah yake bishe su, su ne 'ya'yan Allah.[15] Ai, ruhun da kuka samu ba na bauta ba ne, har da za ku koma zaman tsoro. A'a, na zaman 'ya'ya ne, har muna kira, “Ya Abba! Uba!”[16] Ruhu da Kansa ma, tare da namu ruhu suna yin shaida, cewa mu 'ya'yan Allah ne.[17] In kuwa 'ya'ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.

Zabura 10:14-18
[14] Amma kana gani, kana kuma lura da masu shan wuya, da masu ɓacin rai, Koyaushe kuma a shirye kake ka yi taimako. Mutum wanda ba shi da mai taimako yakan danka kansa gare ka, Gama kullum kakan taimaki masu bukata.[15] Ka karya ikon mugaye, masu mugunta, Ka hukunta su saboda muguntarsu, Har hukuncinsu ya cika sarai.[16] Ubangiji sarki ne har abada abadin, Arna kuma za su ɓace daga ƙasarsa.[17] Za ka saurara ga addu'o'in masu kaɗaici, ya Ubangiji, Za ka ba su ƙarfin hali.[18] Za ka ji koke-koken waɗanda ake zalunta da na marayu, Ka yi shari'ar da za su ji daɗi, Domin kada 'yan adam su ƙara haddasa wata razana.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010