A A A A A

Rayuwa: [Tsufa]


1 Timoti 5:8
Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.

2 Korintiyawa 4:16
Saboda haka ba mu karai ba, ko da yake jikinmu na mutuntaka yana ta lalacewa, duk da haka, ruhunmu a kowace rana sabunta shi ake yi.

Maimaitawar Shariʼa 32:7
“Ku fa tuna da kwanakin dā, Ku yi tunani a kan shekarun tsararraki, Ku tambayi mahaifanku, su za su faɗa muku, Ku tambayi dattawanku, su kuma za su faɗa muku,

Maimaitawar Shariʼa 34:7
Musa ya yi shekara ɗari da ashirin sa'ad da ya rasu. Idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuma bai ragu ba.

Mai Hadishi 7:10
Kada ka yi tambaya, cewa me ya sa zamanan dā suka fi na yanzu? Gama wannan tambaya ba ta hikima ba ce.

Fitowa 20:12
“Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

Farawa 6:3
Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.”

Farawa 25:8
Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama'arsa, waɗanda suka riga shi.

Ishaya 40:29
Yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya.

Ishaya 46:4
Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku, Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura. Ni na halice ku zan kuwa lura da ku, Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”

Ayuba 5:26
Haka kai ma za ka rayu, har ka tsufa da kyakkyawan tsufa.

Ayuba 12:12-20
[12] “Tsofaffi suna da hikima, Amma Allah yana da hikima da iko. Tsofaffi suna da tsinkaya, Amma Allah yana da tsinkaya da ikon aikatawa.[13] ***[14] Sa'ad da Allah ya rurrushe, wa zai iya sāke ginawa? Wa kuma zai iya fitar da mutumin da Allah ya sa a kurkuku?[15] Akan yi fari sa'ad da Allah ya hana ruwan sama, Rigyawa takan zo sa'ad da ya kwararo ruwa.[16] Allah mai iko ne a kullum kuwa cikin nasara yake Da macuci, da wanda aka cutar, duk ƙarƙashin ikon Allah suke.[17] Yakan mai da hikimar masu mulki wauta, Yakan mai da shugabanni marasa tunani.[18] Yakan tuɓe sarakuna ya sa su kurkuku.[19] Yakan ƙasƙantar da firistoci da mutane masu iko.[20] Yakan rufe bakin waɗanda aka amince da su. Yakan kawar da hikimar tsofaffi.

Ayuba 32:7
Na ce wa kaina, ‘Ya kamata kwanaki su yi magana, Yawan shekaru kuma su koyar da hikima.’

Yowel 2:28
“Bayan wannan zan zubo Ruhuna a kan jama'a duka, 'Ya'yanku mata da maza za su iyar da saƙona, Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai, Samarinku za su ga wahayi da yawa.

Firistoci 19:32
“Ku girmama tsofaffi ku darajanta su, gama kuna tsorona. Ni ne Ubangiji.

Filemon 1:9
duk da haka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu,

Zabura 71:9
Yanzu da na tsufa, kada ka yashe ni, Yanzu da ƙarfina ya ƙare kuma, kada ka rabu da ni!

Zabura 71:18
Yanzu da na tsufa, na kuma yi furfura, Kada ka rabu da ni, ya Allah! Ka kasance tare da ni sa'ad da nake shelar ikonka da ƙarfinka ga mutanen dukan zamanai masu zuwa.

Zabura 73:26
Kwanyata da jikina za su raunana, Amma Allah ne ƙarfina, Shi nake so har abada!

Zabura 90:10-12
[10] Tsawon kwanakin ranmu duka a ƙalla shekara ce saba'in, In kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne. Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaru Suke kawo mana, damuwa ce da wahala, Nan da nan sukan wuce, Tamu da ƙare.[11] Wa ya san iyakar ikon fushinka? Wa ya san irin tsoron da hasalarka za ta kawo?[12] Ka koya mana mu sani ranmu na ɗan lokaci ne, Domin mu zama masu hikima.

Zabura 91:16
Zan ba su tsawon rai lada, Hakika kuwa zan cece su.”

Karin Magana 17:6
Tsofaffi suna fāriya da jikokinsu, kamar yadda samari suke alfarma da iyayensu maza.

Karin Magana 20:29
Ƙarfin samari abin darajantawa ne, furfurar tsofaffi abar girmamawa ce.

Karin Magana 23:22
Ka kasa kunne ga mahaifinka, gama da ba dominsa ba, da ba ka, sa'ad da mahaifiyarka ta tsufa ka nuna mata godiyarka.

Zabura 37:35
Na ga wani mugu, azzalumi, Ya fi kowa tsayi, Kamar itacen al'ul na Lebanon,

1 Tarihi 29:28
Sa'an nan ya rasu da kyakkyawan tsufa, cike da shekaru, da arziki, da daraja. Ɗansa Sulemanu kuma ya gāji sarautarsa.

1 Sarakuna 3:14
Idan za ka yi mini biyayya ka kuma kiyaye dokokina, da umarnaina kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, to, zan ba ka tsawon rai.”

Zabura 103:5
Ya cika raina da kyawawan abubuwa, Don in zauna gagau, Ƙaƙƙarfa kamar gaggafa.

Titus 2:3
Haka kuma, manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke, ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyar da kyakkyawan abu,

1 Timoti 5:1-2
[1] Kada ka tsauta wa dattijo, sai dai ka roƙe shi kamar mahaifinka. Samari kuma ka ɗauke su kamar 'yan'uwanka,[2] tsofaffi mata kuma kamar uwayenka, 'yan mata kuwa kamar 'yan'uwanka, da matuƙar tsarkaka.

Zabura 71:8-9
[8] Ina yabonka dukan yini, Ina shelar darajarka.[9] Yanzu da na tsufa, kada ka yashe ni, Yanzu da ƙarfina ya ƙare kuma, kada ka rabu da ni!

Filibbiyawa 3:20-21
[20] Mu kuwa 'yan Mulkin Sama ne, daga can ne kuma muke ɗokin zuwan Mai Ceto, Ubangiji Yesu Almasihu,[21] wanda zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, ya mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka, da ikon nan nasa na sarayar da dukkan abubuwa a gare shi.

Ishaya 46:3-4
[3] “Ku kasa kunne gare ni ku zuriyar Yakubu, Dukanku, mutanena da kuka ragu. Ina ta lura da ku tun daga lokacin da aka haife ku.[4] Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku, Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura. Ni na halice ku zan kuwa lura da ku, Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”

Zabura 92:12-15
[12] Adalai za su yi yabanya Kamar itatuwan giginya, Za su yi girma kamar itatuwan al'ul na Lebanon.[13] Za su zama kamar itatuwan da aka daddasa a Haikalin Ubangiji, Suna ta yabanya a Haikalin Allahnmu.[14] Waɗanda suke yin 'ya'ya da tsufansu, A kullum kuwa kore shar suke, Suna da ƙarfinsu kuma.[15] Wannan ya nuna Ubangiji adali ne, Shi wanda yake kāre ni, Ba kuskure a gare shi.

Mai Hadishi 12:1-7
[1] Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin samartakarka kafin mugayen kwanaki da shekaru su zo, da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu.”[2] Wato lokacin da rana, da haske, da wata, da taurari za su duhunta, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙar da ruwa.[3] A lokacin nan hannuwanka da suke kāre ka, za su yi makyarkyata, ƙafafunka za su rasa ƙarfi. Haƙora kaɗan za su ragu a bakinka. Idanunka za su duhunta.[4] Bakinka a rufe yake, haƙora ba su tauna abinci. Muryar tsuntsu za ta farkar da kai. Ba za ka iya jin muryar mawaƙa ba.[5] Sa'an nan za ka ji tsoron hawan tudu, tafiya kuma za ta yi maka wuya. Gashin kanka zai furfurce. Za ka ja jikinka. Ba sauran sha'awar mace. Daga nan sai kabari, masu makoki kuwa su yi ta kai da kawowa a kan tituna.[6] Hakika, ka tuna da Mahaliccinka kafin igiyar azurfa ta katse, ko tasar zinariya ta fashe, ko tulu ya fashe a bakin rijiya, ko igiya ta tsinke a bakin tafki,[7] sa'an nan turɓaya ta koma ƙasa kamar a dā, ruhu kuma ya koma wurin Allah wanda ya ba da shi.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010