A A A A A

Hali Mai Kyau: [Kulawa]


1 Timoti ௫:௪
In wata gwauruwa tana da 'ya'ya ko jikoki, sai su koya, ya wajaba su fara nuna wa danginsu bautar Allah da suke yi, su kuma sāka wa iyayensu da alheri. Wannan abin karɓa ne a gun Allah.

1 Timoti 3:15
don in ya zamana na yi jinkiri, za ka san irin zaman da ya kamata a yi a jama'ar Allah, wadda take ita ce Ikkilisiyar Allah Rayayye, jigon gaskiya da kuma ginshiƙinta.

Yohanna 8:32
Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta 'yanta ku.”

Ruʼuya ta Yohanna 17:5
A goshinta kuma an rubuta wani sunan asiri, “Babila mai girma, uwar karuwai, uwar abubuwa masu banƙyama na duniya.”

Yaƙub 1:27
Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.

Yohanna 6:54
Duk wanda suke cin naman jikina, yake kuma shan jinina, yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.

Markus 6:3
Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi.

Yohanna 14:6
Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.

Farawa 1:1-7
[1] A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya,[2] duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen.[3] Allah ya ce, “Bari haske ya kasance,” sai kuwa ya kasance.[4] Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu,[5] ya ce da hasken, “Yini,” duhu kuwa, “Dare.” Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan.[6] Allah ya ce, “Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu.”[7] Allah kuwa ya yi sarari, ya kuma raba tsakanin ruwayen da suke ƙarƙashin sararin da ruwayen da suke birbishin sararin. Haka nan kuwa ya kasance.

1 Timoti 5:8
Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.

Galatiyawa 1:19
Amma ban ga ko ɗaya a cikin sauran manzanni ba, sai dai Yakubu ɗan'uwan Ubangiji.

Malaki 1:11
“Mutane daga kowaɗanne sassa na duniya za su girmama ni. Ko'ina za su ƙona mini halattacciyar hadaya, gama dukansu za su girmama ni,” in ji Ubangiji Mai Runduna.

Farawa 2:7
Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.

Yohanna 3:3-5
[3] Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”[4] Nikodimu ya ce masa, “Ƙaƙa za a haifi mutum bayan ya tsufa? Wato, ya iya komawa a cikin uwa tasa ta sāke haifo shi?”[5] Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.

Ibraniyawa 12:14
Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, ku kuma zama a tsarkake, in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji.

Ruʼuya ta Yohanna 17:18
Matar nan da ka gani kuwa, ita ce babban birnin da yake mulkin sarakunan duniya.”

Mattiyu 16:18
Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba.

Farawa 1:1
A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya,

Fitowa 15:3
Ubangiji mayaƙi ne, Yahweh ne sunansa.

Ruʼuya ta Yohanna 17:9
Fahimtar wannan abu kuwa, sai a game da hikima. Wato, kawuna bakwai ɗin nan tuddai ne guda bakwai, waɗanda matar take a zaune a kai.

Filibbiyawa 4:6-7
[6] Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.[7] Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.

Galatiyawa 4:19
Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har Almasihu ya siffatu a zuciyarku!

1 Bitrus 3:15
Sai dai ku girmama Almasihu a zukatanku da hakikancewa, shi Ubangiji ne. Kullum ku zauna a shirye ku ba da amsa ga duk wanda ya tambaye ku dalilin begen nan naku, amma fa da tawali'u da bangirma.

Ruʼuya ta Yohanna 17:1
Sai ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai masu tasoshin nan bakwai, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka hukuncin da za a yi wa babbar karuwar nan, wadda take zaune a bisa ruwa mai yawa,

Mattiyu 18:15-18
[15] “In ɗan'uwanka ya yi maka laifi, sai ka je, ka gaya masa laifinsa, kai da shi, ku kaɗai. In ya saurare ka, to, kā maido da ɗan'uwanka ke nan.[16] In kuwa bai saurare ka ba, sai ka tafi da mutum ɗaya ko biyu, don a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.[17] In kuma ya ƙi sauraronsu, sai ka shaida wa ikilisiya. In kuma har ya ƙi sauraron ikilisiyar, ka maishe shi kamar bare, ko mai karɓar haraji.”[18] “Hakika, ina gaya muku, kome kuka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome kuka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne.

Afisawa 1:22-23
[22] Allah kuma ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikon Almasihu, ya kuma ba da shi ga Ikkilisiya ya zama Kai mai mallakar abu duka.[23] Ikkilisiya ita ce jikin Almasihu, cikar mai cika dukkan abu.

Afisawa 5:23
Don miji shi ne shugaban matarsa, kamar yadda Almasihu yake shugaban Ikkilisiya, wato, jikinsa, shi kansa kuma shi ne Mai Ceton jikin.

Ayyukan Manzanni 4:32
To, duk taron da suka ba da gaskiya kuwa nufinsu ɗaya ne, ra'ayinsu ɗaya, ba kuma waninsu da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, sai dai kome nasu ne baki ɗaya.

1 Korintiyawa 1:10
Na roƙe ku 'yan'uwa, saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, cewa dukanku bakinku yă zama ɗaya, kada wata tsaguwa ta shiga a tsakaninku, sai dai ku haɗa kai, kuna da nufi ɗaya, ra'ayinku ɗaya.

Yohanna 12:48
Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai hukunta shi, maganar da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe.

Yohanna 14:28
Kun dai ji na ce muku zan tafi, in kuma dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni.

Ibraniyawa 1:14
Ashe, dukan mala'iku ba ruhohi masu hidima ba ne, waɗanda Allah yakan aika, don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?

Mattiyu 18:10
“Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara. Ina gaya muku, mala'ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin Sama.[

Afisawa 6:12
Ai, famarmu ba da 'yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu.

Yohanna ٣:١٦
“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.

Yohanna ١٧:١٧
Ka tsarkake su cikin gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya.

Ruʼuya ta Yohanna 2:9
“ ‘Na san tsananin da kake sha, da talaucinka (amma bisa ga hakika kai mawadaci ne), na kuma san yanken da waɗansu suke yi maka, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, jama'ar Shaiɗan ne.

Zabura 68:5
Allah, wanda yake zaune a tsattsarkan Haikalinsa, Yana lura da marayu, yana kuwa kiyaye gwauraye, Wato matan da mazansu suka mutu.

Zabura 146:9
Yakan kiyaye baƙi waɗanda suke zaune a ƙasar. Yakan taimaki gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu. Yakan lalatar da dabarun mugaye.

Galatiyawa 2:10
Sai dai kuma suna so mu tuna matalauta, wannan kuwa ko dā ma ina da himmar yi ƙwarai.

Romawa 3:23
gama 'yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010