A A A A A

Hali Mai Kyau: [Yarda]


1 Korintiyawa 5:11-13
[11] Sai dai na rubuta muku ne, don kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan'uwa, mai bi, in yana fasikanci, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan.[12] Ina ruwana da hukunta waɗanda ba namu ba? Ba waɗanda suke a cikin Ikkilisiya za ku hukunta ba?[13] Allah ne yake hukunta waɗanda ba namu ba. Ku kori mugun nan daga cikinku.

1 Yohanna 1:9
In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci.

1 Bitrus 3:8-9
[8] Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar 'yan'uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali'u.[9] Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.

Yohanna 3:16
“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.

Karin Magana 13:20
Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima. Yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.

Romawa 2:11
Domin kuwa, Allah ba ya nuna tara.

Romawa 5:8
Amma kuwa Allah yana tabbatar mana da ƙaunar da yake yi mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu.

Romawa 8:31
To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?

Romawa 14:1-2
[1] A game da wanda bangaskiya tasa rarrauna ce kuwa, ku karɓe shi hannu biyu biyu, amma ba a game da sukan ra'ayinsa ba.[2] Ga wani, bangaskiyarsa ta yardar masa cin kome, wanda bangaskiyarsa rarrauna ce kuwa, sai kayan gona kawai yake ci.

Ibraniyawa 10:24-25
[24] mu kuma riƙa kula da juna, ta yarda za mu ta da juna a tsimi mu mu yi ƙauna da aika nagari.[25] Kada mu bar yin taronmu, yadda waɗansu suke yi, sai dai mu ƙarfafa wa juna zuciya, tun ba ma da kuka ga ranar nan tana kusatowa ba.

Yohanna 6:35-37
[35] Yesu ya ce musu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada.[36] Na dai gaya muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.[37] Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.

Kolossiyawa 3:12-14
[12] Saboda haka, sai ku ɗauki halin tausayi, da kirki, da tawali'u, da salihanci, da haƙuri, idan ku zaɓaɓɓu ne na Allah, tsarkaka, ƙaunatattu,[13] kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe.[14] Fiye da waɗannan duka, ku ɗau halin ƙauna, wadda dukkan kammala take ƙulluwa a cikinta.

Mattiyu 5:38-42
[38] “Kun dai ji an faɗa, ‘Sakayyar ido, ido ne, sakayyar haƙori kuma haƙori ne.’[39] Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma.[40] In kuwa wani ya yi ƙararka da niyyar karɓe taguwarka, to, ka bar masa mayafinka ma.[41] In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma.[42] Kowa ya roƙe ka, ka ba shi, mai neman rance a wurinka kuwa, kada ka hana shi.”

Mattiyu 25:34-40
[34] Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.[35] Domin na ji yunwa, kun ba ni abinci. Na ji ƙishirwa, kun ba ni na sha. Na yi baƙunci, kun saukar da ni.[36] Na yi huntanci, kun tufasar da ni. Na yi rashin lafiya, kun ziyarce ni. Ina kurkuku, kun kula da ni.’[37] Sa'an nan ne masu adalci za su amsa masa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa muka cishe ka, ko kuwa da ƙishirwa muka shayar da kai?[38] A yaushe kuma muka gan ka baƙo muka sauke ka, ko kuwa huntu muka tufasar da kai?[39] Ko kuma a yaushe muka gan ka da rashin lafiya, ko a kurkuku muka kula da kai?’[40] Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’

Romawa 15:1-7
[1] To, mu da muke ƙarfafa, ya kamata mu ɗauki nauyin raunana, kada mu yi sonkai.[2] Kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai, don kyautata zamansa da kuma inganta shi.[3] Gama ko Almasihu ma bai yi sonkai ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zagin da waɗansu suka yi maka duk yā komo kaina.”[4] Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta shi ne domin a koya mana, domin mu ɗore a cikin sa zuciyar nan tamu ta wurin haƙuri da ta'aziyyar da Littattafai suke yi mana.[5] Allah mai ba da haƙuri da ta'aziyya, yă ba ku zaman lafiya da juna bisa halin Almasihu Yesu,[6] domin ku ɗaukaka Allah, Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma Ubansa, nufinku ɗaya, bakinku ɗaya.[7] Saboda haka ku karɓi juna da hannu biyu biyu, kamar yadda Almasihu ya karɓe ku hannu biyu biyu, domin a ɗaukaka Allah.

Romawa 14:10-19
[10] To, kai, me ya sa kake ganin laifin ɗan'uwanka? Kai kuma, me ya sa kake raina ɗan'uwanka? Ai, dukkanmu za mu tsaya a gaban kursiyin shari'ar Allah.[11] Domin a rubuce yake, “Na rantse da zatina, in ji Ubangiji, kowace gwiwa sai ta rusuna mini, Kowane harshe kuwa sai ya yabi Allah.”[12] Don haka kowannenmu zai faɗi abin da shi da kansa ya yi, a gaban Allah.[13] Saboda haka kada mu ƙara ganin laifin juna, gara mu ƙudura, don kada kowannenmu yă zama sanadin tuntuɓe ko faɗuwa ga ɗan'uwansa,[14] Na sani, na kuma tabbata, a tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake marar tsarki ga asalinsa, sai dai ga wanda ya ɗauke shi marar tsarki ne yake marar tsarki.[15] In kuwa cimarka tana cutar ɗan'uwanka, ashe, ba zaman ƙauna kake yi ba. Kada fa cimarka ta hallaka wannan da Almasihu ya mutu dominsa.[16] Saboda haka kada abin da ka ɗauka kyakkyawa ya zama abin zargi ga waɗansu.[17] Ai, Mulkin Allah ba ga al'amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.[18] Wanda duk yake bauta wa Almasihu ta haka, abin karɓa ne ga Allah, yardajje ne kuma ga mutane.[19] Don haka sai mu himmantu ga yin abubuwan da suke kawo salama, suke kuma kawo inganta juna.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010