Instagram
English
A A A A A

Allah: [Albarkar Kuɗi]


1 Samaʼila 2:7
Yakan sa waɗansu mutane su zama matalauta, Waɗansu kuwa attajirai. Yakan ƙasƙantar da waɗansu, Ya kuma ɗaukaka waɗansu.

2 Korintiyawa 8:9
Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.

3 Yohanna 1:2
Ya ƙaunataccena, ina addu'a kă sami zaman lafiya ta kowace hanya da kuma lafiya jiki, kamar yadda ruhunka yake a zaune lafiya.

Mai Hadishi 9:10
Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.

Galatiyawa 6:9
Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba.

Farawa 13:2
Yanzu Abram ya arzuta da dabbobi, da azurfa, da zinariya.

Hosiya 4:6
Mutanena sun lalace saboda jahilci. Tun da yake sun ƙi ilimi, Ni ma na ƙi ku da zaman firist ɗina. Tun da yake kun manta da umarnan Allahnka, Ni ma zan manta da 'ya'yanku.

Yaƙub 5:12
Amma fiye da kome, 'yan'uwana, kada ku rantse sam, ko da sama, ko da ƙasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. Sai dai in kun ce “I”, ya tsaya a kan “I” ɗin kawai, in kuwa kun ce “A'a”, ya tsaya a kan “A'a” ɗin kawai, don kada a hukunta ku.

Yohanna 6:12
Da suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka saura, kada kome ya ɓata.”

Luka 6:38
Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”

Luka 12:34
don kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”

Karin Magana 10:22
Albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba.

Karin Magana 11:14
Al'ummar da ba ta da masu ja mata gora, za ta fāɗi. Yawan mashawarta yake kawo zaman lafiya.

Karin Magana 19:17
Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.

Karin Magana 21:17
Sa kai cikin nishaɗi, wato shan ruwan inabi, da cin abinci mai tsada, ba zai bar ka ka tara dukiya ba.

Karin Magana 22:9
Ka zama mai hannu sake, ka riƙa ba matalauta abincinka, za a sa maka albarka saboda haka.

Karin Magana 28:22-27
[22] Mutum mai haɗama yana gaggawar samun dukiya, bai kuwa sani ba, ashe, fatara ce za ta same shi.[23] Wanda ya tsauta wa mutum zai sami yabo daga baya, fiye da wanda ya yi masa daɗin baki.[24] Wanda yake yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa sata, yana kuwa tsammani ba laifi ba ne, daidai da ɓarawo yake.[25] Mutum mai haɗama yana haddasa tashin hankali, amma wanda ya dogara ga Ubangiji zai sami wadar zuci.[26] Wanda yake dogara ga son zuciyarsa, wawa ne, amma wanda yake tafiya cikin hikima zai kuɓuta.[27] Wanda yake bayarwa ga matalauta, ba zai talauce ba, amma wanda bai kula da su ba, mutane da yawa za su la'ance shi.

Zabura 24:1
Duniya da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji ne, Duniya da dukan mazaunanta nasa ne.

Mattiyu 6:33
Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.

Mattiyu 23:23
“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na'ana'a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba.

Mattiyu 25:21
Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’

Romawa 13:8
Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari'a ke nan.

Karin Magana 3:9-10
[9] Ka girmama Ubangiji ta wurin miƙa masa hadaya daga mafi kyau na amfanin gonarka.[10] Idan ka yi haka rumbunanka za su cika da hatsi. Za ka sami ruwan inabi mai yawa, har ka rasa wurin da za ka zuba shi duka.

Zabura 121:1-2
[1] Na duba wajen duwatsu, Daga ina taimakona zai zo?[2] Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.

Markus 11:22-23
[22] Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku gaskata da Allah.[23] Hakika, ina gaya muku, kowa ya ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku’, bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata abin da ya faɗa zai auku, sai a yi masa shi.

Farawa 1:26-27
[26] Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.”[27] Haka nan fa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da ta mace ya halicce su.

2 Korintiyawa 9:6-8
[6] Abin la'akari fa, shi ne wanda ya yi ƙwauron yafa iri, gonarsa za ta yi masa ƙwauron amfani, wanda kuwa ya yafa a yalwace, sai ya girba a yalwace.[7] Sai kowa yă bayar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilastawa ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.[8] Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.

Luka 14:28-30
[28] Misali, in wani daga cikinku yana son gina soron bene, da fari ba sai ya zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba, ya ga ko yana da isassun kuɗi da za su ƙare aikin?[29] Kada ya zamana bayan da ya sa harsashin ginin, yă kasa gamawa, har duk waɗanda suka gani, su fara yi masa ba'a,[30] su riƙa cewa, ‘A! Ka ga mutumin nan ya fara gini, amma ya kasa gamawa!’

Luka 6:34-36
[34] In kuma sai ga waɗanda kuke tsammani za su biya ku ne kuke ba da rance, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma, sukan ba masu zunubi rance, don a biya su daidai.[35] Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.[36] Ku kasance masu tausayi kamar yadda Ubanku yake mai tausayi.”

Yaƙub 5:1-3
[1] To, ina masu arziki? Ku yi ta kuka da kururuwa saboda baƙin ciki iri iri da za su aukar muku.[2] Arzikinku mushe ne! Tufafinku kuma duk cin asu ne![3] Zinariyarku da azurfarku sun ɓāci ƙwarai, ɓācin nan nasu kuwa zai zama shaida a kanku, yă ci naman jikinku kamar wuta! Kun dai jibge dukiya a zamanin ƙarshen nan!

Farawa 12:1-20
[1] Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka fita daga ƙasarka, da danginka, da gidan mahaifinka zuwa ƙasar da zan nuna maka.[2] Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka.[3] Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la'anta waɗanda suka la'anta ka. Dukan al'umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”[4] Abram kuwa ya kama hanya bisa ga faɗar Ubangiji, Lutu kuma ya tafi tare da shi, Abram yana da shekara saba'in da biyar sa'ad da ya yi ƙaura daga Haran.[5] Abram kuwa ya ɗauki matarsa Saraya da Lutu, ɗan ɗan'uwansa, da dukan dukiyarsu, da dukan mallakarsu waɗanda suka tattara a Haran. Sa'ad da suka kai ƙasar Kan'ana,[6] Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan'aniyawa suke a ƙasar.[7] Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.[8] Ya zakuɗa daga nan zuwa dutsen da yake gabashin Betel, ya kafa alfarwarsa, Betel tana yamma, Ai tana gabas, a nan ya gina wa Ubangiji bagade, ya kira bisa sunan Ubangiji.[9] Abram kuwa ya ci gaba da tafiya, ya nufi zuwa wajen Negeb.[10] A lokacin nan ana yunwa a ƙasar. Sai Abram ya tafi Masar baƙunci, gama yunwa ta tsananta a ƙasar.[11] Sa'ad da yake gab da shiga Masar, ya ce wa matarsa, Saraya, “Na sani ke kyakkyawar mace ce,[12] lokacin da Masarawa suka gan ki za su ce, ‘Wannan matarsa ce,’ za su kashe ni, amma za su bar ki da rai.[13] Ki ce ke 'yar'uwata ce, domin dalilinki kome sai ya tafi mini daidai a kuma bar ni da raina.”[14] Sa'ad da Abram ya shiga Masar sai Masarawa suka ga matar kyakkyawa ce ƙwarai.[15] Da fādawan Fir'auna suka gan ta, sai suka yabe ta a gaban Fir'auna. Aka ɗauke ta aka kai ta gidan Fir'auna.[16] Saboda ita Fir'auna ya yi wa Abram alheri. Abram yana da tumaki, da takarkarai, da jakai maza, da barori mata da maza, da jakai mata, da raƙuma.[17] Sai Ubangiji ya wahalar da Fir'auna da gidansa da manya manyan annobai saboda matar Abram, Saraya.[18] Sai Fir'auna ya kirawo Abram, ya ce, “Mene ne wannan da ka yi mini? Don me ba ka faɗa mini ita matarka ce ba?[19] Don me ka ce ita 'yar'uwarka ce, har na ɗauke ta ta zama matata? To, ga matarka, ka ɗauke ta ka tafi.”[20] Fir'auna kuma ya umarci mutanensa a kan Abram, su raka shi da matarsa, da dukan abin da yake da shi.

Mattiyu 6:1-34
[1] “Ku yi hankali kada ibadarku ta zama ta ganin ido. Domin in kun yi haka, ba za ku sami sakamako wurin Ubanku da yake a Sama ba.[2] “Wato, in za ka yi sadaka, kada ka yi kwakwazo yadda munafukai suke yi a majami'u da kuma kan hanya don dai mutane su yabe su. Gaskiya nake faɗa muku, sun sami iyakar ladarsu ke nan.[3] Amma in kana yin sadaka, kada hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama yake yi,[4] domin sadakarka tă zama a asirce, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”[5] “In za ku yi addu'a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'u da kan hanya, wai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu.[6] Amma in za ka yi addu'a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu'a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.[7] “In kuwa kuna addu'a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al'ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu.[8] Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.[9] Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka, ‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama, A kiyaye sunanka da tsarki.[10] Mulkinka yă zo, A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.[11] Ka ba mu abincinmu na yau.[12] Ka gafarta mana laifofinmu, Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.[13] Kada ka kai mu wurin jaraba, Amma ka cece mu daga Mugun.’[14] Domin in kun yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku na Sama zai yafe muku.[15] In kuwa ba ku yafe wa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.”[16] “In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan.[17] Amma in kana azumi, ka shafa mai a ka, ka kuma wanke fuska,[18] don kada mutane su ga alama kana azumi, sai dai Ubanku da yake ɓoye ya gani. Ubanku kuma da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”[19] “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda ɓarayi kuma suke karyawa su yi sata.[20] Sai dai ku tara wa kanku dukiya a Sama, inda ba asu da tsatsa da za su ɓata, inda kuma ba ɓarayin da za su karya su yi sata.[21] Domin kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”[22] “Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka ma sai ya cika da haske.[23] In kuwa idonka da lahani, duk jikinka sai ya cika da duhu. To, in hasken da yake gare ka duhu ne, ina misalin yawan duhun!”[24] “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”[25] “Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba?[26] Ku dubi dai tsuntsaye. Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma tarawa a rumbuna, amma kuwa Ubanku na Sama na ci da su. Ashe, ko ba ku fi martaba nesa ba?[27] Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa?[28] To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi,[29] duk da haka ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba.[30] To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya![31] Don haka kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ ko, ‘Me za mu sha?’ ko kuwa, ‘Me za mu sa?’[32] Ai, al'ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka.[33] Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.[34] “Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe ta Allah ce. Wahalce-wahalcen yau ma sun isa wahala.”

Maimaitawar Shariʼa 28:1-68
[1] “Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuna aikata dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, to, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukan sauran al'umma.[2] Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, dukan albarkun nan za su sauko muku, su zama naku.[3] “Za ku zama masu albarka, ko kuna cikin gari, ko kuna cikin karkara.[4] “'Ya'yanku za su zama masu albarka, haka nan kuma amfanin gonakinku, da 'ya'yan dabbobinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da awakinku.[5] “Kwandunanku da makwaɓan za su yalwata ƙullunku.[6] “Da albarka za ku shiga, da albarka kuma za ku fita.[7] “Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.[8] “Ubangiji zai sa wa abin da yake cikin rumbunanku albarka da dukan aikin hannuwanku. Zai sa muku albarka a ƙasar da yake ba ku.[9] “Ubangiji zai sa ku zama tsattsarkar jama'arsa kamar yadda ya rantse muku, idan za ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa.[10] Dukan mutanen duniya za su gane ku na Ubangiji ne, za su ji tsoronku.[11] Ubangiji zai arzuta ku ƙwarai da 'ya'ya, da 'ya'yan dabbobi, da amfanin gona, a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba ku.[12] Ubangiji zai buɗe muku taskarsa ta sammai, don ya ba ƙasarku ruwa a kan kari, zai kuma sa albarka a kan dukan aikin hannuwanku. Al'ummai da yawa za su karɓi rance a wurinku, amma ku, ba za ku karɓi rance ba.[13] Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. Kullum ci gaba za ku yi, ba baya ba, idan kuka yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, in kun lura, kun yi aiki da su,[14] idan kuma ba ku kauce zuwa dama ko hagu daga maganar da na umarce ku da ita yau ba, wato don ku bi waɗansu gumaka, ku bauta musu.”[15] “Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ko kuwa ba ku lura kuka aikata umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartar da su yau ba, to, dukan waɗannan la'ana za su auko muku, su same ku.[16] “La'anannu za ku zama a gari da karkara.[17] “La'anannu ne kwandunanku da makwaɓan ƙullunku.[18] “La'anannu ne 'ya'yanku, da amfanin gonakinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da na awakinku.[19] “Da la'ana za ku shiga, da la'ana kuma za ku fita.[20] “Ubangiji zai aiko muku da la'ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni.[21] Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za ta manne muku, ta cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta.[22] Ubangiji zai buge ku da ciwon fuka, da zazzaɓi, da ciwon kumburi, da zafi mai tsanani, da fari, da burtuntuna, da fumfuna. Waɗannan za su yi ta damunku har ku lalace.[23] Samaniya da take bisa kanku za ta zama tagulla, ƙasar kuma da kuke a bisa kanta ta zama baƙin ƙarfe.[24] Ubangiji zai mai da ruwan sama na ƙasarku gāri da ƙura, zai zubo muku da shi daga sama har ku hallaka.[25] “Ubangiji zai sa abokan gabanku su rinjaye ku cikin yaƙi. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya.[26] Gawawwakinku za su zama abinci ga dukan tsuntsayen sama, da namomin duniya. Ba wanda zai kore su.[27] Ubangiji zai buge ku da marurai irin na Masar, da basur, da ƙazwa, da ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba.[28] Ubangiji kuma zai buge ku da ciwon hauka, da makanta, da rikicewar hankali.[29] Da tsakar rana za ku riƙa lalubawa kamar makaho, ba za ku yi arziki cikin ayyukanku ba. Za a riƙa zaluntarku, ana yi muku ƙwace kullum, ba wanda zai cece ku.[30] “Za ku yi tashin yarinya, wani ne zai kwana da ita. Za ku gina gida, wani ne zai zauna a ciki. Za ku dasa inabinku, wani ne zai girbe amfanin.[31] Za a yanka sanku a idonku, amma ba za ku ci ba. Za a ƙwace jakinku ƙiri ƙiri a idonku, ba za a mayar muku da shi ba. Za a ba magabtanku tumakinku, ba wanda zai cece ku.[32] A idonku za a ba da 'ya'yanku mata da maza ga wata al'umma dabam, za ku yi ta jin kewarsu, amma a banza, gama ba ku da ikon yin kome.[33] Mutanen da ba ku sani ba, su za su ci amfanin gonakinku da dukan amfanin wahalarku. Za a zalunce ku, a murƙushe ku kullum.[34] Abubuwan da idanunku za su gani za su sa ku zama mahaukata.[35] Ubangiji zai bugi gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai tun daga tafin ƙafarku har zuwa ƙoƙwan kanku.[36] “Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al'ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu.[37] Za ku zama abin ƙi, da abin karin magana, da abin habaici a cikin dukan mutane inda Ubangiji zai kora ku.[38] “Za ku shuka iri da yawa a gonakinku, amma kaɗan za ku girbe gama fara za su cinye.[39] Za ku dasa gonakin inabi, ku nome su, amma ba za ku sha ruwan inabin, ko ku tsinke 'ya'yan inabin ba, gama tsutsa za ta cinye shi.[40] Za ku sami itatuwan zaitun ko'ina cikin ƙasarku, amma ba za ku sami man da za ku shafa ba, gama 'ya'yan za su kakkaɓe.[41] Za ku haifi 'ya'ya mata da maza, amma ba za su zama naku ba, gama za a kai su bauta.[42] Ƙwari za su cinye dukan itatuwanku da dukan amfanin ƙasarku.[43] “Baƙin da suke tare da ku za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya baya.[44] Za ku karɓi rance a wurinsu, su ba za su karɓi rance a wurinku ba. Su za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya.[45] “Dukan waɗannan la'anoni za su auko muku, su bi ku, su same ku, har ku hallaka, domin ba ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ba ku kiyaye umarnai da dokoki da ya umarce ku da su ba.[46] Za su zama alama da abin mamaki a kanku da zuriyarku har abada.[47] Ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da murna da farin ciki ba, saboda dukan abin da ya ba ku a yalwace,[48] domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku.[49] Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba,[50] al'umma mai zafin hali, wadda ba ta kula da tsofaffi, ba ta kuma jin tausayin yara.[51] Za ta ci shanunku da amfanin ƙasarku har ku hallaka. Ba za ta bar muku hatsi ko ruwan inabi, ko mai, ko 'ya'yan shanunku, ko na tumaki da na awakinku ba, har ta lalatar da ku.[52] Za su kewaye garuruwanku da yaƙi, har dogayen garukanku, da kagaranku waɗanda kuke dogara gare su, su rurrushe. Za su kewaye garuruwan ƙasarku da yaƙi a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku.[53] Za ku ci naman 'ya'yanku, mata da maza, waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku, saboda irin tsananin kewayewar da magabtanku suka yi muku da yaƙi.[54] Nagarin mutum mai taushin zuciya wanda yake tare da ku, zai ƙi ɗan'uwansa, da matarsa, da 'ya'yansa da suka ragu,[55] domin kada ya ba wani daga cikinsu naman 'ya'yansa wanda yake ci, gama ba abin da ya rage masa saboda irin tsananin kewayewar garuruwanku da yaƙi wanda abokan gabanku suka kawo muku.[56] Matar kirki mai taushin zuciya wadda take tare da ku wadda ba za ta sa tafin ƙafarta a ƙasa ba saboda taushin zuciyarta da kyakkyawan halinta, za ta ƙi ƙaunataccen mijinta, da ɗanta, da 'yarta.[57] A ɓoye za ta ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da 'ya'yan da za ta haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da magabtanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.[58] “Idan ba ku lura, ku aikata dukan maganar dokokin nan da aka rubuta a wannan littafi ba, domin ku ji tsoron sunan nan mai ɗaukaka, mai kwarjini, wato sunan Ubangiji Allahnku,[59] to, Ubangiji zai aukar muku, ku da zuriyarku, da munanan masifu waɗanda ba su kawuwa, da mugayen cuce-cuce marasa warkewa.[60] Sai ya sāke kawo muku cuce-cuce irin na Masar, waɗanda kuka ji tsoronsu, za su kuwa manne muku.[61] Har yanzu kuma Ubangiji zai kawo muku kowace irin cuta, da kowace irin annoba, waɗanda ba a ambace su a littafin dokokin nan ba, har ku hallaka.[62] Ko da yake kuna da yawa kamar taurarin sama, za ku zama 'yan kaɗan, domin ba ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku ba.[63] Kamar yadda Ubangiji ya ji daɗi ya arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku, haka nan kuma zai ji daɗi ya lalatar da ku, ya hallaka ku. Za a fitar da ku daga ƙasar da za ku shiga, ku mallaka.[64] “Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba.[65] Ba za ku sami zaman lafiya wurin waɗannan al'ummai ba, ko tafin ƙafarku ma ba zai sami wurin hutawa ba. Ubangiji kuma zai sa fargaba a zuciyarku, ya sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu.[66] Kullum ranku zai kasance da damuwa, za ku zauna da tsoro dare da rana, kuna tsoron abin da zai sami ranku.[67] Da safe za ku ce, ‘Da ma maraice ne.’ Da maraice kuma za ku ce, ‘Da ma safiya ce,’ saboda tsoron da yake a zuciyarku, da abubuwan da idanunku suke gani.[68] Ubangiji zai komar da ku Masar cikin jiragen ruwa, ko da yake na ce ba za ku ƙara tafiya can ba. Can za ku sayar da kanku bayi mata da maza, amma ba wanda zai saye ku.”

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010