Instagram
English
A A A A A

Allah: [Kuzo Kamar Yadda Kuke]


Mattiyu 11:27-30
[27] Kowane abu Ubana ne ya mallakar mini. Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa.[28] Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku.[29] Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali'u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.[30] Domin bautata sassauƙa ce, kayana kuma marar nauyi ne.”

Yohanna 6:63-65
[63] Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai.[64] Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi.[65] Sai ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku, ba mai iya zuwa gare ni, sai ko Uba ya yardar masa.”

Mattiyu 11:28
Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku.

Ishaya 1:18
Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al'amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu.

Ishaya 55:1-3
[1] Ubangiji ya ce, “Duk mai jin ƙishi ya zo, Ga ruwa a nan! Ku da ba ku da kuɗi ku zo, Ku sayi hatsi ku ci! Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara, Ba za ku biya kome ba![2] Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba? Don me za ku ɓad da albashinku, amma kuna ta shan yunwa? Ku kasa kunne gare ni, ku yi abin da na faɗa, Za ku sha daɗin abinci mafi kyau duka.[3] “Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai! Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.

Mattiyu 15:7-9
[7] Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce,[8] ‘Al'ummar nan a baka kawai suke girmama ni, Amma a zuci nesa suke da ni.[9] A banza suke bauta mini, Don ka'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’ ”

Markus 10:13-16
[13] Suna kawo masa waɗansu yara ƙanana domin ya taɓa su, sai almajiransa suka kwaɓe su.[14] Da Yesu ya ga haka, sai ya ji haushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne.[15] Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na'am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”[16] Sai Yesu ya rugume su, yana ɗora musu hannu, yana sa musu albarka.

Yaƙub 4:6-8
[6] Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali'u alheri.”[7] Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku.[8] Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.

2 Korintiyawa 5:17
Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ne, tsohon al'amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo.

Yohanna 5:24
Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.

Romawa 12:1-2
[1] Don haka ina roƙonku 'yan'uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.[2] Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.

Ibraniyawa 12:1
Saboda haka, tun da taron shaidu masu ɗumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu yar da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya ɗafe mana, mu kuma yi tseren nan da yake gabanmu tare da jimiri,

Firistoci 25:44
Amma a kan bayi mata da maza da kuke so ku samu, kwa iya sayensu daga al'ummar da yake kewaye da ku.

Zabura 32:8-10
[8] Ubangiji ya ce, “Zan koya maka hanyar da za ka bi, Zan koya maka, in kuma ba ka shawara.[9] Kada ka zama wawa kamar doki ko alfadari, Wanda dole sai da linzami, da ragama za a sarrafa shi, Sa'an nan yă yi maka biyayya.”[10] Tilas ne mugu yă sha wahala, Amma masu dogara ga Ubangiji, Madawwamiyar ƙaunarsa tana kiyaye su.

Ishaya 29:13
Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun ce suna mini sujada, amma kalmominsu ba su da ma'ana, zukatansu kuma suna wani wuri dabam. Addininsu ba wani abu ba ne, sai dai dokoki ne da ka'idodin mutane da suka haddace.

Yohanna 5:40
Duk da haka, kun ƙi zuwa wurina ku sami rai.

Yohanna 6:44-45
[44] Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.[45] A rubuce yake cikin littattafan annabawa cewa, ‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni.

Yohanna 7:37-39
[37] A ranar ƙarshe ta idin, wato babbar ranar, sai Yesu ya tsaya, ya ɗaga murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa yă zo gare ni yă sha.[38] Duk mai gaskatawa da ni, kamar yadda Nassi ya ce, ‘Daga zuciyarsa ne kogunan ruwan rai za su gudana.’ ”[39] To, wannan shi ne ya faɗa game da Ruhu, wanda masu gaskatawa da shi za su karɓa, domin har yanzu ba a ba da Ruhu ba, saboda ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna.

Ibraniyawa 4:14-16
[14] To, tun da yake muna da Babban Firist mai girma, wanda ya ratsa sammai, wato Yesu Ɗan Allah, sai mu tsaya a kan abin da muka bayyana yarda a gare shi.[15] Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.[16] Saboda haka, sai mu kusaci kursiyin Allah na alheri da amincewa, domin a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari.

Ruʼuya ta Yohanna 22:16-17
[16] “Ni Yesu, na aiko mala'ikana a gare ka, da wannan shaida saboda ikilisiyoyi. Ni ne tsatson Dawuda, da zuriyarsa, Gamzaki mai haske.”[17] Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.

Yohanna 6:37
Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.

Ruʼuya ta Yohanna 22:17
Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.

Ishaya 13:6-8
[6] Ku yi ihu saboda shan azaba, ranar Ubangiji ta yi kusa. Ranar da Mai Iko Dukka zai kawo hallaka.[7] Hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.[8] Dukansu za su firgita, azaba za ta ci ƙarfinsu kamar mace wadda take shan azabar naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu za su cika da kunya.

Ruʼuya ta Yohanna 12:9
Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.

Filibbiyawa 1:6
Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu.

Ruʼuya ta Yohanna 21:4
zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.”

Ibraniyawa 10:19-22
[19] Saboda haka, ya 'yan'uwa, tun da muke da amincewar shiga Wuri Mafi Tsarki, ta wurin jinin Yesu,[20] ta wurin sabuwar hanya, rayayyiya wadda ya buɗe mana ta labulen nan, wato jikinsa,[21] da yake kuma muna da Firist mai girma, mai mulkin jama'ar Allah,[22] sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa.

Yowel 2:32
Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, Akwai waɗanda suke a Dutsen Sihiyona da Urushalima Da za su tsira, Waɗannan da Ubangiji ya zaɓa za su tsira.”

Zabura 104:9
Ka ƙayyade masa kan iyaka da ba zai taɓa ƙetarewa ba, Don kada ya sāke rufe duniya.

Farawa 6:12
Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.

Farawa 8:9
amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi.

Farawa 9:11
Na kafa alkawarina da ku. Daɗai ba za a ƙara hallaka talikai duka da ruwa ba, ba kuma za a ƙara yin Ruwan Tsufana da zai hallaka duniya ba.”

Farawa 7:20
Ruwa ya bunƙasa bisa duwatsu ya yi musu zara da ƙafa ashirin da biyar.

Farawa 8:5
Ruwa ya yi ta raguwa har wata na goma. A ran ɗaya ga wata na goma, sai kawunan duwatsu suka ɓullo.

Karin Magana 31:30
Kayan tsari da jamali duk banza ne, amma mace mai tsoron Ubangiji, ita ce abar yabo.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010