Instagram
English
A A A A A

Muguwar Hali: [Gunaguni]
Zabura 144:14
Ka sa shanunmu su hayayyafa, Kada su yi ɓari ko su ɓace. Ka sa kada a ji kukan damuwa a kan titunanmu!

Nehemiya 8:1
Dukan jama'a suka taru wuri ɗaya a filin Ƙofar Ruwa, suka faɗa wa Ezra, magatakarda, ya kawo Attaura ta Musa wanda Ubangiji ya ba Isra'ilawa.

Ishaya 24:11
Mutane za su tsaya a tituna, suna ihu, suna neman ruwan inabi. Farin ciki ya ƙare har abada, ya ƙare a ƙasar.

Irmiya 14:2
“Yahuza tana makoki, Ƙofofin biranenta suna lalacewa, Mutanenta suna kwance a ƙasa, suna makoki, Urushalima tana kuka da babbar murya.

Karin Magana 23:29
Wa ake yi wa kaito? Wa yake da baƙin ciki? Wane ne mafaɗaci? Wa yake yin gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan ido?

Filibbiyawa 4:6-7
[6] Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.[7] Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010