A A A A A

Muguwar Hali: [Cin zalin mutum]


1 Yohanna 2:9
Kowa ya ce yana a cikin haske, yana kuwa ƙin ɗan'uwansa, ashe, a duhu yake har yanzu.

1 Yohanna 3:15
Kowa da yake ƙin dan'uwansa, mai kisankai ne. Ƙun kuwa sani ba mai kisankan da yake da rai madawwami a zauna tare da shi.

2 Timoti 1:7
Ai, Allah ba halin tsoro ya ba mu ba, hali mai ƙarfi ne, mai ƙauna, da kuma kamunkai.

Maimaitawar Shariʼa 31:6
Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”

Afisawa 4:29
Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.

Afisawa 6:12
Ai, famarmu ba da 'yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu.

Firistoci 19:18
Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko ya yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji.

Mattiyu 5:11
“Albarka tā tabbata gare ku sa'ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni.

Karin Magana 17:9
Idan kana so mutane su so ka, ka riƙa yafe musu sa'ad da suka yi maka laifi. Mita takan raba abuta.

Karin Magana 22:10
Ka rabu da mutum mai fāriya, mai gardama, mafaɗaci, hatsaniya za ta ƙare.

Karin Magana 24:16
Ko sau nawa amintaccen mutum ya faɗi, ba abin damuwa ba ne, gama a ko yaushe zai sāke tashi, amma masifa takan hallaka mugaye.

Zabura 138:7
Ko lokacin da nake tsakiyar wahala, Za ka kiyaye ni lafiya, Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata, Za ka kuwa cece ni da ikonka.

Romawa 2:1
Saboda haka ba ka da wata hujja, kai mutum, ko kai wane ne da kake ganin laifin wani. A yayin da kake ganin laifin wani, ai, kanka kake hukunta wa, don ga shi, kai mai ganin laifin wani, kai ma haka kake yi.

Romawa 12:18-19
[18] In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.[19] Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Domin a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.”

Romawa 12:20-21
[20] Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.”[21] Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.

Luka 6:27-28
[27] “Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri.[28] Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu'a.

Mattiyu 5:44-45
[44] Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu'a,[45] domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.

Ishaya 41:11-13
[11] “Su waɗanda suke fushi da ku, ku jama'ata, Za a ƙasƙantar da su su ji kunya. Waɗanda suke faɗa da ku kuwa za su mutu.[12] Za ku neme su, amma ba za ku same su ba, Wato waɗanda suke gāba da ku. Waɗanda suka kama yaƙi da ku, Za su shuɗe daga duniya.[13] Ni ne Ubangiji Allahnku, Na ƙarfafa ku, na kuwa faɗa muku, ‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.’ ”

Mattiyu 5:38-41
[38] “Kun dai ji an faɗa, ‘Sakayyar ido, ido ne, sakayyar haƙori kuma haƙori ne.’[39] Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma.[40] In kuwa wani ya yi ƙararka da niyyar karɓe taguwarka, to, ka bar masa mayafinka ma.[41] In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma.

Zabura 34:12-18
[12] Kuna so ku ji daɗin rai? Kuna son tsawon rai da farin ciki?[13] To, ku yi nisa da mugun baki, Da faɗar ƙarairayi.[14] Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri, Ku yi marmarin salama, ku yi ƙoƙarin samunta.[15] Ubangiji yana lura da adalai, Yana kasa kunne ga koke-kokensu,[16] Amma yana ƙin masu aikata mugunta, Saboda haka har mutanensu sukan manta da su.[17] Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne, Yakan cece su daga dukan wahalarsu.[18] Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010