A A A A A

Arin: [Cin naman mutane]


Irmiya 19:9
Zan sa su ci naman 'ya'yansu mata da maza. Kowa zai ci naman maƙwabcinsa cikin damuwa a lokacin da za a kewaye su da yaƙi, zai sha wahala daga wurin abokan gābansa da waɗanda suke neman ransa.’

Ezekiyel 5:10
Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.

Firistoci 26:29
Za ku ci naman 'ya'yanku mata da na 'ya'yanku maza.

2 Sarakuna 6:28-29
[28] Me yake damunki?” Sai ta amsa, ta ce, “Wannan mace ta ce mini, in kawo ɗana mu ci yau, gobe kuma mu ci nata.[29] Sai muka dafa ɗana muka cinye. Kashegari kuwa na ce mata ta kawo ɗanta mu ci, amma sai ta ɓoye shi.”

Makoki 4:10
Mata masu juyayi, da hannuwansu Suka ɗauki 'ya'yansu, suka dafa, Suka zama musu abinci a lokacin halakar mutanena.

Makoki 2:20
Ya Ubangiji, ka duba, ka gani! Wane ne ka yi wa haka? Mata za su cinye 'ya'yansu da suke reno? Ko kuwa za a kashe firist da annabi A cikin Haikalin Ubangiji?

Maimaitawar Shariʼa 28:53-57
[53] Za ku ci naman 'ya'yanku, mata da maza, waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku, saboda irin tsananin kewayewar da magabtanku suka yi muku da yaƙi.[54] Nagarin mutum mai taushin zuciya wanda yake tare da ku, zai ƙi ɗan'uwansa, da matarsa, da 'ya'yansa da suka ragu,[55] domin kada ya ba wani daga cikinsu naman 'ya'yansa wanda yake ci, gama ba abin da ya rage masa saboda irin tsananin kewayewar garuruwanku da yaƙi wanda abokan gabanku suka kawo muku.[56] Matar kirki mai taushin zuciya wadda take tare da ku wadda ba za ta sa tafin ƙafarta a ƙasa ba saboda taushin zuciyarta da kyakkyawan halinta, za ta ƙi ƙaunataccen mijinta, da ɗanta, da 'yarta.[57] A ɓoye za ta ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da 'ya'yan da za ta haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da magabtanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.

Farawa 1:26-27
[26] Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.”[27] Haka nan fa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da ta mace ya halicce su.

2 Korintiyawa 5:8
Hakika muna da ƙarfin zuciya, mun kuma gwammace mu rabu da jikin nan, mu zauna a gun Ubangiji.

Luka 16:19-26
[19] “An yi wani mai arziki, mai sa tufafin jan alharini da farare masu ƙawa, yana shan daularsa a kowace rana.[20] An kuma ajiye wani gajiyayye a ƙofarsa, mai suna Li'azaru, wanda duk jikinsa miki ne.[21] Shi kuwa yana marmarin ya ƙoshi da suɗin mai arzikin nan. Har ma karnuka sukan zo suna lasar miyakunsa.[22] Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, mala'iku kuma suka ɗauke shi, suka kai shi wurin Ibraham. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.[23] Yana a cikin Hades yana shan azaba, sai ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a wurinsa.[24] Sai ya yi kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiko Li'azaru ya tsoma kan yatsarsa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.’[25] Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba.[26] Banda wannan ma duka, tsakaninmu da ku akwai wani gawurtaccen rami mai zurfi, zaunanne, don waɗanda suke son ƙetarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ƙetaro zuwa wurinmu daga can.’

Ruʼuya ta Yohanna 20:11-15
[11] Sa'an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace.[12] Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.[13] Sai teku ta ba da matattun da suke a cikinta, mutuwa da Hades kuma sun ba da matattun da suke a gare su, aka kuwa yi wa kowa shari'a gwargwadon aikin da ya yi.[14] Sa'an nan aka jefa mutuwa da Hades a tafkin nan na wuta. Wannan ita ce mutuwa ta biyu, wato, tafkin wuta.[15] Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a Littafin Rai ba, sai a jefa shi a tafkin nan na wuta.

Maimaitawar Shariʼa 28:53
Za ku ci naman 'ya'yanku, mata da maza, waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku, saboda irin tsananin kewayewar da magabtanku suka yi muku da yaƙi.

1 Korintiyawa 14:34-35
[34] Sai mata su yi shiru a cikin taron ikkilisiya, don ba a ba su izinin yin magana ba, sai dai su bi, kamar dai yadda Attaura ma ta ce.[35] In akwai wani abin da suke so su sani, to, sai su tambayi mazansu a gida, don abin kunya ne mace ta yi magana a cikin taron ikkilisiya.

Luka 1:37
Ba wata faɗar Allah da za ta kasa cika.”

Yohanna 1:1
Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne.

Maimaitawar Shariʼa 28:57
A ɓoye za ta ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da 'ya'yan da za ta haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da magabtanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.

1 Timoti 2:11-15
[11] Mace ta riƙa koyo da kawaici da matuƙar biyayya.[12] Ban yarda mace ta koyar, ko kuma ta yi iko da maza ba, sai dai ta zama shiru.[13] Ai, Adamu aka fara halitta, sa'an nan Hawwa'u.[14] Ba kuma Adamu aka yaudara ba, amma matar ce aka yaudara, har ta keta umarni.[15] Duk da haka kuwa, ta wurin haifar 'ya'ya sai ta kai ga kammala, muddin ta nace wa bangaskiya, da ƙauna, da zama a tsarkake, da kuma kamunkai.

1 Timoti 5:3-16
[3] Ka girmama gwauraye mata, waɗanda ba sa da mataimaka.[4] In wata gwauruwa tana da 'ya'ya ko jikoki, sai su koya, ya wajaba su fara nuna wa danginsu bautar Allah da suke yi, su kuma sāka wa iyayensu da alheri. Wannan abin karɓa ne a gun Allah.[5] Gwauruwa marar mataimaki kuwa, mai zaman kaɗaici, ta dogara ga Allah ke nan, tana nacewa ga roƙon Allah, tana addu'a dare da rana.[6] Amma wadda take zaman annashuwa kuwa, kamar matacciya take, ko da tana a raye.[7] Ka umarce su a game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi.[8] Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.[9] Kada a lasafta gwauruwa a cikin gwauraye, sai dai ta kai shekara sittin, ba ta yi aure fiye da ɗaya ba,[10] wadda ake yabo a kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi 'ya'ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke ƙafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari.[11] Amma kada ka lasafta gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu, a cikin gwaurayen, don in zuciyarsu ta kasa daurewa a game da wa'adin da suka yi da Almasihu, sai su so yin aure,[12] hukunci yā kama su ke nan, tun da yake sun ta da wa'adinsu na farko.[13] Banda haka kuma sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida gida. Ba ma kawai masu zaman banza za su zama ba, har ma sai su zama matsegunta, masu shishigi, suna faɗar abin da bai kamata ba.[14] Saboda haka, ina so gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu su yi aure, su haifu, su tafiyar da al'amuran gida, kada su ba magabci hanyar zarginmu.[15] Gama waɗansu ma har sun bauɗe, sun bi Shaiɗan.[16] Duk mace mai bi, da take da dangi gwauraye mata, sai ta taimake su, kada a nauwaita wa ikkilisiya, don ikkilisiyar ta samu ta taimaki gwauraye marasa mataimaka.

1 Korintiyawa 11:2-16
[2] Ina yaba muku ne don kuna tunawa da ni a cikin kowace harka, kuna kuma riƙe ka'idodin nan da kyau, daidai yadda na ba ku.[3] Amma fa ina so ku fahimci cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace kuwa mijinta ne, shugaban Almasihu kuma Allah ne.[4] Duk mutumin da ya yi addu'a ko ya yi annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa ke nan.[5] Amma duk matar da ta yi addu'a, ko ta yi annabci da kanta a buɗe, ta wulakanta shugabanta ke nan, duk ɗaya ne da an aske kanta ma.[6] In mace ta ƙi rufe kanta, to, sai ta sausaye gashinta. In kuwa abin kunya ne a yi wa mace sausaye ko kundumi, to, sai ta rufe kanta.[7] Namiji kam, bai kamata yă rufe kansa ba, tun da yake shi kamannin Allah ne, abin alfahari ga Allah kuma. Amma mace abar taƙamar namiji ce.[8] (Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba, amma matar daga jikin namiji take.[9] Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.)[10] Shi ya sa ya kamata mace ta rufe kanta, wato, alamar ikon namiji, saboda mala'iku.[11] Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba.[12] Wato, kamar yadda mace take daga namiji, haka namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke.[13] Ku kanku ku duba fa ku gani. Ya dace da mace ke nan ta yi addu'a ga Allah da kanta a buɗe?[14] Ashe, ko ɗabi'a ma ba ta nuna muku cewa namiji ya yi gizo, abin kunya ne ba?[15] In kuwa mace tana da gashi, ba alfarmarta ce ba? Gama don rufin kai ne aka yi mata gashin.[16] In kuwa wani yana da niyyar gardama, to, mu dai ba mu san wata al'ada ba, ikilisiyoyin Allah kuma haka.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010