A A A A A

Arin: [Karya Zuciya]


1 Korintiyawa 13:7
Ƙauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da bangaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali, da jimiri a cikin kowane hali.

1 Bitrus 5:7
Ku jibga masa dukan taraddadinku, domin yana kula da ku.

1 Samaʼila 16:7
Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”

2 Korintiyawa 5:7
domin zaman bangaskiya muke yi, ba na ganin ido ba.

2 Korintiyawa 12:9
amma ya ce mini, “Alherina yā isa, domin ta wajen rashin ƙarfi ake ganin cikar ikona.” Saboda haka sai ma in ƙara yin alfarma da raunanata da farinciki fiye da na da, domin ikon Almasihu ya zauna a tare da ni.

Ibraniyawa 13:5
Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kansa ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.”

Ishaya 6:1
A shekarar da sarki Azariya ya rasu na ga Ubangiji. Yana zaune a kursiyinsa a Sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika Haikali.

Ishaya 41:10
Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.

Ishaya 57:15
Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.

Irmiya 29:11
Gama na san irin shirin da na yi muku, ni Ubangiji na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya.

Yohanna 3:16
“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.

Yohanna 12:40
“Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu, Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci, Har su juyo gare ni in warkar da su.”

Yohanna 14:1
“Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.

Yohanna 14:27
Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro.

Yohanna 16:33
Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”

Luka 24:38
Sai ya ce musu, “Don me kuka firgita, kuke kuma tantama a zuciyarku?

Markus 11:23
Hakika, ina gaya muku, kowa ya ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku’, bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata abin da ya faɗa zai auku, sai a yi masa shi.

Mattiyu 5:8
“Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah.

Mattiyu 11:28
Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku.

Karin Magana 3:5
Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani.

Zabura 34:18
Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.

Zabura 51:17
Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah, Zuciya mai ladabi da biyayya, Ba za ka ƙi ba, ya Allah.

Zabura 55:22
Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji, Zai kuwa taimake ka, Ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.

Zabura 147:3
Yakan warkar da masu karyayyiyar zuciya, Yakan ɗaure raunukansu.

Ruʼuya ta Yohanna 21:4
zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.”

Romawa 8:28
Mun kuma sani al'amura duka suna aikatawa tare, zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, wato, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa.

Romawa 12:2
Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.

Karin Magana 4:23
Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja.

Karin Magana 3:5-6
[5] Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani.[6] A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.

1 Korintiyawa 6:19-20
[19] Ashe, ba ku sani ba, jikinku Haikali ne na Ruhu Mai Tsarki wanda yake a zuciyarku, wanda kuka kuma samu a gun Allah? Ai, ku ba mallakar kanku ba ne.[20] Sayenku aka yi da tamani. To, sai ku ɗaukaka Allah da jikinku.

Filibbiyawa 4:6-7
[6] Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.[7] Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.

Mattiyu 11:28-30
[28] Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku.[29] Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali'u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.[30] Domin bautata sassauƙa ce, kayana kuma marar nauyi ne.”

Zabura 34:1-22
[1] Zan yi godiya ga Ubangiji kullayaumin, Faufau ba zan taɓa fasa yabonsa ba.[2] Zan yabe shi saboda abin da ya yi, Da ma dukan waɗanda suke da tawali'u su kasa kunne, su yi murna![3] Ku yi shelar girman Ubangiji tare da ni, Mu yabi sunansa tare![4] Na yi addu'a ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini, Ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.[5] Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna, Ba za su ƙara ɓacin rai ba.[6] Marasa galihu suka yi kira gare shi, ya kuwa amsa. Ya cece su daga dukan wahalarsu.[7] Mala'ikansa yana tsaron waɗanda suke tsoron Ubangiji, Ya cece su daga hatsari.[8] Ku gane da kanku yadda Ubangiji yake da alheri! Mai farin ciki ne mutumin da ya sami kwanciyar rai a wurinsa![9] Ku yi tsoron Ubangiji ku jama'arsa duka, Masu tsoronsa suna da dukan abin da suke bukata.[10] Har zakoki sukan rasa abinci su ji yunwa, Amma masu biyayya ga Ubangiji, Ba abu mai kyau da sukan rasa.[11] Ku zo, ku abokaina, ku kasa kunne gare ni, Zan koya muku ku ji tsoron Ubangiji.[12] Kuna so ku ji daɗin rai? Kuna son tsawon rai da farin ciki?[13] To, ku yi nisa da mugun baki, Da faɗar ƙarairayi.[14] Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri, Ku yi marmarin salama, ku yi ƙoƙarin samunta.[15] Ubangiji yana lura da adalai, Yana kasa kunne ga koke-kokensu,[16] Amma yana ƙin masu aikata mugunta, Saboda haka har mutanensu sukan manta da su.[17] Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne, Yakan cece su daga dukan wahalarsu.[18] Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.[19] Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa, Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.[20] Ubangiji yakan kiyaye shi sosai, Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da zai karye ba.[21] Mugunta za ta kashe mugu, Waɗanda suke ƙin adalai za a hukunta su.[22] Ubangiji zai fanshi bayinsa, Waɗanda suka tafi wurinsa neman mafaka Za a bar su da rai.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010