A A A A A

Arin: [Alkohol]


1 Bitrus 4:3
Denn es ist genug, daß wir die vergangene Zeit des Lebens zugebracht haben nach heidnischem Willen, da wir wandelten in Unzucht, Lüsten, Trunkenheit, Fresserei, Sauferei und greulichen Abgöttereien.

1 Timoti 5:23
A nan gaba ba ruwa kaɗai za ka sha ba, sai dai ka sha ruwan inabi kaɗan saboda cikinka, da kuma yawan laulayinka.

Mai Hadishi 9:7
Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da fara'a, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.

Afisawa 5:18
Kada kuma ku bugu da giya, hanyar masha'a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu,

Karin Magana 20:1
Ruwan inabi da barasa sukan sa ka ka yi ta tā da murya, ka zama wawa. Wauta ce mutum ya bugu.

Karin Magana 23:31
Kada ka bar ruwan inabi ya jarabce ka, ko da yake ja wur yake, har kana iya ganin kanka a cikin ƙoƙon, yana kuwa da kyan gani sa'ad da kake motsa shi.

Romawa 13:13
Mu tafiyar da al'amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa, ko fasikanci da fajirci, ko jayayya da kishi ba.

Karin Magana 31:4-5
[4] Bai dace ba, ya Lamuwel, bai dace ba ko kaɗan, sarakuna su sha ruwan inabi, ko masu mulki su yi marmarin barasa,[௫] don kada su sha su manta da doka, su kuma kauce wa gaskiya a shari'ar waɗanda aka zalunta.

Zabura 104:14-15
[14] Kakan sa ciyawa ta yi girma don shanu, Tsire-tsire kuma don amfanin mutum, Saboda haka mutum zai iya shuka amfanin gona,[15] Don ya yi ruwan inabin da zai sa shi farin ciki, Ya sami man zaitun wanda zai sa shi fara'a, Da abincin da zai ba shi ƙarfi.

1 Korintiyawa 10:23-24
[23] “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne suke ingantawa ba.[24] Kada kowa ya nemi ya kyautata wa kansa, sai dai ya kyautata wa ɗan'uwansa.

Ishaya 62:8-9
[8] Ubangiji ya yi alkawari mai ƙarfi, Ta wurin ikonsa kuwa zai cika shi. “Hatsinku ba zai ƙara zama abincin abokan gābanku ba, Baƙi ba za su ƙara shanye ruwan inabinku ba.[9] Amma ku da kuka shuka hatsin kuka kuma girbe shi, Za ku ci abinci, ku yi yabon Ubangiji! Ku da kuka lura da itatuwan inabi kuka tara su, Za ku sha ruwan inabi a filayen Haikalina.”

Galatiyawa 5:19-21
[19] Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci, da aikin lalata, da fajirci,[20] da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya,[21] da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina faɗakar da ku kamar yadda na faɗakar da ku a dā, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba.

1 Korintiyawa ௯:௧௯-௨௩
[௧௯] Ko da yake ni ba bawan kowa ba ne, na mai da kaina bawan kowa, domin in rinjayi mutane masu yawa.[௨௦] Ga Yahudawa, sai na zama kamar Bayahude, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda Shari'a take iko da su, sai na zama kamar wanda Shari'a take iko da shi, ko da yake ba Shari'a take iko da ni ba, domin in rinjayi waɗanda Shari'a take iko da su ne.[௨௧] Ga marasa Shari'a kuwa, sai na zama kamar marar Shari'a, ba cewa ba wata shari'ar Allah da take iko da ni ba, a'a, shari'ar Almasihu na iko da ni, domin in rinjayi marasa Shari'a ne.[௨௨] Ga raunana, sai na zama kamar rarrauna domin in rinjayi raunana. Na zama kowane irin abu ga ko waɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu.[௨௩] Na yi wannan ne duk saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.

Romawa 14:15-21
[15] In kuwa cimarka tana cutar ɗan'uwanka, ashe, ba zaman ƙauna kake yi ba. Kada fa cimarka ta hallaka wannan da Almasihu ya mutu dominsa.[16] Saboda haka kada abin da ka ɗauka kyakkyawa ya zama abin zargi ga waɗansu.[17] Ai, Mulkin Allah ba ga al'amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.[18] Wanda duk yake bauta wa Almasihu ta haka, abin karɓa ne ga Allah, yardajje ne kuma ga mutane.[19] Don haka sai mu himmantu ga yin abubuwan da suke kawo salama, suke kuma kawo inganta juna.[20] Kada ka rushe aikin Allah saboda abinci kawai. Hakika dukan abu mai tsarki ne, amma mugun abu ne mutum yă zama sanadin tuntuɓe ga wani, ta wurin abin da yake ci.[21] Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan'uwanku yin tuntuɓe.

Yohanna 2:3-11
[3] Da ruwan inabi ya gaza, uwar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”[4] Yesu ya ce mata, “Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.”[5] Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.”[6] A wurin kuwa akwai randuna shida na dutse a ajijjiye, bisa ga al'adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce na cin wajen tulu shida shida.[7] Sai Yesu ya ce musu, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal.[8] Sa'an nan ya ce musu, “To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka kai.[9] Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), ya yi magana da ango,[10] ya ce, “Kowa, ai, kyakkyawan ruwan inabi yakan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa'an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!”[11] Wannan ce mu'ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.

Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010