A A A A A


Bincika

Ayyukan Manzanni 24:2
Saʼad da aka shigo da Bulus, sai Tertullus ya shiga kai ƙararsa a gaban Felis yana cewa: “Mun daɗe muna zaman lafiya a ƙarƙashinka, hangen nesanka kuma ya kawo gyare-gyare a wannan ƙasa.


Romawa 12:16
Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girmankai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.


Romawa 12:18
Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.


1 Korintiyawa 7:15
Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne.


Filibbiyawa 2:20
Ba ni da wani kamarsa, wanda yake da ainihin shaʼawa a zaman lafiyarku.


Filibbiyawa 4:2
Ina roƙon Yuwodiya ina kuma roƙon Sintike, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.


1 Tessalonikawa 5:3
Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za ta auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.


1 Tessalonikawa 5:13
Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.


Ibraniyawa 12:14
Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji.


3 Yohanna 1:2
Abokina ƙaunatacce, ina adduʼa ka sami zaman lafiya domin kome yǎ yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya.


Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc