A A A A A


Bincika

Mattiyu 1:1
Tarihin da aka rubuta game da asalin Yesu Kiristi ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim:


Mattiyu 1:16
Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi.


Mattiyu 1:18
Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance: An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf, amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


Mattiyu 1:21
Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi zai ceci mutanensa daga zunubansu.”


Mattiyu 1:25
Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.


Mattiyu 2:1
Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima


Mattiyu 3:13
Sai Yesu ya zo daga Galili ya je Urdun don Yohanna yǎ yi masa baftisma.


Mattiyu 3:15
Yesu ya amsa, ya ce, “Bari yǎ zama haka yanzu; ya dace mana mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Saʼan nan Yohanna ya yarda.


Mattiyu 3:16
Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa.


Mattiyu 4:1
Saʼan nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada domin Iblis yǎ gwada shi.


Mattiyu 4:4
Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ba da burodi kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’ ”


Mattiyu 4:7
Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa: ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”


Mattiyu 4:10
Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake: ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’ ”


Mattiyu 4:12
Da Yesu ya ji labari cewa an sa Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili.


Mattiyu 4:17
Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara waʼazi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”


Mattiyu 4:18
Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ʼyanʼuwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗanʼuwansa Andarawus. Suna jefa taru a tafki, gama su masunta ne.


Mattiyu 4:19
Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.”


Mattiyu 4:21
Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ʼyanʼuwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗanʼuwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya tarunsu. Yesu ya kira su,


Mattiyu 4:22
nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.


Mattiyu 4:23
Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majamiʼunsu, yana waʼazin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane.


Mattiyu 7:28
Saʼad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa,


Mattiyu 8:3
Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtace!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.


Mattiyu 8:4
Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.”


Mattiyu 8:5
Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako.


Mattiyu 8:7
Yesu ya ce masa, “Zan je in warkar da shi.”


Mattiyu 8:10
Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Israʼila da bangaskiya mai girma haka ba.


Mattiyu 8:13
Saʼan nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.


Mattiyu 8:14
Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi.


Mattiyu 8:18
Da Yesu ya ga taron mutane kewaye da shi, sai ya ba da umarni a ƙetare zuwa ɗayan hayin tafkin.


Mattiyu 8:20
Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama kuma suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”


Mattiyu 8:22
Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”


Mattiyu 8:24
Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.


Mattiyu 8:31
Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”


Mattiyu 8:34
Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yǎ bar musu yanki.


Mattiyu 9:1
Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya ƙetare ya zo garinsa.


Mattiyu 9:2
Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu ɗana, an gafarta maka zunubanka.”


Mattiyu 9:4
Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku?


Mattiyu 9:9
Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.


Mattiyu 9:10
Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma “masu zunubi” suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa.


Mattiyu 9:12
Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.


Mattiyu 9:15
Yesu ya amsa, ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, saʼan nan za su yi azumi.


Mattiyu 9:19
Yesu ya tashi ya tafi tare da shi, haka ma almajiransa.


Mattiyu 9:22
Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, “Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke,” Nan take macen ta warke.


Mattiyu 9:23
Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya,


Mattiyu 9:27
Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!”


Mattiyu 9:30
sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, “Ku lura kada wani yǎ san wani abu game da wannan.”


Mattiyu 9:32
Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana.


Mattiyu 9:35
Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majamiʼunsu, yana waʼazin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.


Mattiyu 10:4
Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.


Mattiyu 10:5
Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa: “Kada ku je cikin Alʼummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa.


Mattiyu 11:1
Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yǎ koyar yǎ kuma yi waʼazi a garuruwan Galili.


Mattiyu 11:4
Yesu ya amsa, ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani:


Mattiyu 11:7
Saʼad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna: “Me kuka je ƙallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne?


Mattiyu 11:20
Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba.


Mattiyu 11:25
A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara.


Mattiyu 12:1
A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci.


Mattiyu 12:10
a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”


Mattiyu 12:14
Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.


Mattiyu 12:15
Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu,


Mattiyu 12:22
Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari.


Mattiyu 12:25
Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.


Mattiyu 12:46
Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ʼyanʼuwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi.


Mattiyu 13:1
A ranan nan sai Yesu ya fita daga gida ya je ya zauna a bakin tafkin.


Mattiyu 13:24
Yesu ya ba su wani misali: “Mulkin sama yana kama da wani da ya shuka iri mai kyau a cikin gonarsa.


Mattiyu 13:34
Yesu ya faɗa wa taron dukan waɗannan abubuwa cikin misalai; bai faɗa musu kome ba, sai tare da yin amfani da misalai.


Mattiyu 13:51
Yesu ya tambaye, su ya ce, “Kun gane dukan waɗannan abubuwa?” Suka amsa, “I.”


Mattiyu 13:53
Saʼad da Yesu ya gama ba da waɗannan misalai, sai ya ci gaba daga can.


Mattiyu 13:57
Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”


Mattiyu 14:1
A lokacin nan sarki Hiridus ya ji labarin Yesu,


Mattiyu 14:12
Almajiran Yohanna suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne. Saʼan nan suka je suka gaya wa Yesu.


Mattiyu 14:13
Saʼad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa.


Mattiyu 14:14
Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.


Mattiyu 14:16
Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.”


Mattiyu 14:22
Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yǎ sallami taron.


Mattiyu 14:25
Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.


Mattiyu 14:27
Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”


Mattiyu 14:29
Ya ce, “Zo.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu.


Mattiyu 14:31
Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”


Mattiyu 14:35
Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a koʼina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu


Mattiyu 15:1
Saʼan nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce,


Mattiyu 15:3
Yesu ya amsa, ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda alʼadarku?


Mattiyu 15:10
Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane.


Mattiyu 15:16
Yesu ya tambaye, su ya ce, “Har yanzu ba ku gane ba ne?


Mattiyu 15:21
Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon.


Mattiyu 15:23
Yesu bai ce mata uffan ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta ta tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.”


Mattiyu 15:28
Saʼan nan Yesu ya amsa, ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ʼYarta kuwa ta warke nan take.


Mattiyu 15:29
Yesu ya tashi daga nan ya bi ta gefen Tekun Galili. Saʼan nan ya haura gefen wani dutse ya zauna.


Mattiyu 15:32
Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya.”


Mattiyu 15:34
Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?” Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ʼyan ƙananan kifaye.”


Mattiyu 15:39
Bayan Yesu ya sallami taron, sai ya shiga jirgin ruwa ya tafi wajajen Magadan.


Mattiyu 16:1
Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo don su gwada Yesu ta wurin neman yǎ nuna musu wata alama daga sama.


Mattiyu 16:4
Wannan mugu da mazinacin zamani yana neman wani abin banmamaki, amma ba wata alamar da za a nuna wa wannan zamani sai dai ta Yunana.” Sai Yesu ya bar su ya tafi abinsa.


Mattiyu 16:6
Yesu ya ce musu, “Ku yi hankali, ku yi taka tsantsan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”


Mattiyu 16:8
Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba?


Mattiyu 16:13
Saʼad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?”


Mattiyu 16:17
Yesu ya amsa, ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama.


Mattiyu 16:21
Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yǎ tafi Urushalima yǎ sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.


Mattiyu 16:23
Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin alʼamuran Allah, sai dai alʼamuran mutane.”


Mattiyu 16:24
Saʼan nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bin na, dole yǎ ƙi kansa, yǎ ɗauki gicciyensa, yǎ bi ni.


Mattiyu 17:1
Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗanʼuwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai.


Mattiyu 17:3
Nan take sai ga Musa da Eliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.


Mattiyu 17:4
Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku--ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Eliya.”


Mattiyu 17:7
Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”


Mattiyu 17:8
Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.


Mattiyu 17:9
Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”


Mattiyu 17:11
Yesu ya amsa, ya ce, “Tabbatacce, Eliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa.


Mattiyu 17:17
Yesu ya amsa, ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurin kai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”


Mattiyu 17:18
Yesu ya tsauta wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.


Mattiyu 17:19
Saʼan nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?”


Mattiyu 17:24
Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?”


Mattiyu 17:25
Ya amsa ya ce “I, yana biya.” Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, “Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji-daga wurin ʼyaʼyansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?”


Mattiyu 17:26
Bitrus ya amsa, ya ce, “Daga wurin waɗansu.” Yesu ya ce masa, “Wato, an ɗauke wa ʼyaʼyan ke nan.”


Mattiyu 18:1
A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Wane ne mafi girma a mulkin sama?”


Mattiyu 18:21
Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗanʼuwana saʼad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?”


Mattiyu 18:22
Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau sabaʼin da bakwai.


Mattiyu 19:1
Saʼad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai ya bar Galili, ya tafi yankin Yahudiya a ɗaya gefen Urdun.


Mattiyu 19:8
Yesu ya amsa, ya ce, “Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko.


Mattiyu 19:11
Yesu ya ce, “Ba kowa ba ne zai yarda da wannan magana, sai dai waɗanda aka yarda musu.


Mattiyu 19:13
Saʼan nan aka kawo yara ƙanana wurin Yesu don yǎ ɗibiya musu hannuwansa, yǎ kuma yi musu adduʼa. Amma almajirai suka tsauta wa waɗanda suka kawo su.


Mattiyu 19:14
Yesu ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne.”


Mattiyu 19:16
To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”


Mattiyu 19:17
Yesu ya amsa, ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”


Mattiyu 19:18
Mutumin ya yi tambaya, ya ce, “Waɗanne?” Yesu ya amsa, ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya,


Mattiyu 19:21
Yesu ya amsa, ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Saʼan nan ka zo, ka bi ni.”


Mattiyu 19:23
Saʼan nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yǎ shiga mulkin sama.


Mattiyu 19:26
Yesu ya dube su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.”


Mattiyu 19:28
Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, saʼad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilai goma sha biyu na Israʼila shariʼa.


Mattiyu 20:17
To, da Yesu yana haurawa zuwa Urushalima, sai ya ja almajiran nan goma sha biyu gefe, ya ce musu,


Mattiyu 20:20
Sai mahaifiyar ʼyaʼyan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ʼyaʼyanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yǎ yi mata wani abu.


Mattiyu 20:22
Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?” Suka amsa, “Za mu iya.”


Mattiyu 20:23
Yesu ya ce musu, “Hakika za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”


Mattiyu 20:25
Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Alʼummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko.


Mattiyu 20:29
Saʼad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi.


Mattiyu 20:30
Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”


Mattiyu 20:32
Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”


Mattiyu 20:34
Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.


Mattiyu 21:1
Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma iso Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu,


Mattiyu 21:6
Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su.


Mattiyu 21:7
Suka kawo jakar da ɗan, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu.


Mattiyu 21:10
Saʼad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?”


Mattiyu 21:11
Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”


Mattiyu 21:12
Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai.


Mattiyu 21:16
Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da yaran nan suke faɗi?” Yesu ya amsa, ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa, “ ‘Daga leɓunan yara da jarirai ka shirya wa kanka yabo’?”


Mattiyu 21:21
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku’, sai yǎ faru.


Mattiyu 21:23
Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?”


Mattiyu 21:24
Yesu ya amsa, ya ce, “Ni ma zan yi muku tambaya guda. In kuka ba ni amsa, ni ma zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.


Mattiyu 21:27
Saboda haka suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Sai ya ce, “Ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”


Mattiyu 21:31
“Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.


Mattiyu 21:42
Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi ba cewa: “ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi ne ya zama dutsen kusurwar gini. Ubangiji ne ya aikata wannan, kuma abin mamaki ne a idanunmu’?


Mattiyu 21:45
Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake.


Mattiyu 22:1
Yesu ya sāke yi musu magana da misalai, yana cewa:


Mattiyu 22:18
Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?


Mattiyu 22:29
Yesu ya amsa, ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba.


Mattiyu 22:34
Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru.


Mattiyu 22:37
Yesu ya amsa, ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’


Mattiyu 22:41
Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su,


Mattiyu 23:1
Saʼan nan Yesu ya ce wa taron mutane da kuma almajiransa:


Mattiyu 24:1
Yesu ya bar haikali ke nan, yana cikin tafiya saʼad da almajiransa suka zo wurinsa don su ja hankalinsa ga gine-ginen haikali.


Mattiyu 24:2
Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.”


Mattiyu 24:3
Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?”


Mattiyu 24:4
Yesu ya amsa: “Ku lura fa, kada wani yǎ ruɗe ku.


Mattiyu 26:1
Saʼad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa,


Mattiyu 26:4
suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.


Mattiyu 26:6
Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu,


Mattiyu 26:10
Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.


Mattiyu 26:17
A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya, “Ina kake so mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”


Mattiyu 26:19
Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.


Mattiyu 26:20
Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun.


Mattiyu 26:23
Yesu ya amsa, ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni.


Mattiyu 26:25
Saʼan nan Yahuda, wanda zai bashe shi, ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa, ya ce, “I, kai ne.”


Mattiyu 26:26
Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”


Mattiyu 26:31
Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya sabili da ni, gama a rubuce yake cewa: “ ‘Zan bugi makiyayin, tumakin garken kuwa za su fasu.’


Mattiyu 26:34
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”


Mattiyu 26:36
Saʼan nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi adduʼa.”


Mattiyu 26:49
Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Saʼan nan ya yi masa sumba.


Mattiyu 26:50
Yesu ya amsa, ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.” Saʼan nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi.


Mattiyu 26:51
Ganin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne.


Mattiyu 26:52
Sai Yesu ya ce, masa, “Mai da takobinka kube, gama duk masu zare takobi, a takobi za su mutu.


Mattiyu 26:55
A wannan lokaci sai Yesu ya ce wa taron, “Ina jagorar wani tawaye ne, da kuka fito da takuba da kuma sanduna don ku kama ni? Kowace rana ina zama a filin haikali ina koyarwa, ba ku kuwa kama ni ba.


Mattiyu 26:57
Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru.


Mattiyu 26:59
Sai manyan firistoci da ʼyan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.


Mattiyu 26:62
Saʼan nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”


Mattiyu 26:63
Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai: Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”


Mattiyu 26:64
Sai Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka: Nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”


Mattiyu 26:69
To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu Bagalile.”


Mattiyu 26:71
Saʼan nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”


Mattiyu 26:75
Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.


Mattiyu 27:1
Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu.


Mattiyu 27:3
Saʼad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin.


Mattiyu 27:11
Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce, “I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.”


Mattiyu 27:14
Amma Yesu bai ce uffan game da ko ɗaya daga cikin zargin da suka yi masa ba. Har gwamna ya yi mamaki ƙwarai.


Mattiyu 27:17
Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su, ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku: Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?”


Mattiyu 27:18
Don ya san saboda kishi ne suka ba da Yesu a gare shi.


Mattiyu 27:20
Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu.


Mattiyu 27:22
Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?” Duka suka ce, “A gicciye shi!”


Mattiyu 27:26
Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, saʼan nan ya ba da shi a gicciye.


Mattiyu 27:27
Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, saʼan nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi.


Mattiyu 27:37
Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, “WANNAN SHI NE YESU SARKIN YAHUDAWA.”


Mattiyu 27:46
Wajen saʼa ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani” — wanda yake nufi, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”


Mattiyu 27:48
Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yǎ sha.


Mattiyu 27:50
Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.


Mattiyu 27:53
Suka firfito daga kaburbura, saʼan nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.


Mattiyu 27:54
Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizan ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”


Mattiyu 27:55
Akwai mata da yawa a can, suna ƙallo daga nesa. Sun bi Yesu tun daga Galili, suna masa hidima.


Mattiyu 27:57
Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne.


Mattiyu 27:58
Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yǎ ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi.


Mattiyu 28:5
Malaʼikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne.


Mattiyu 28:9
Kwaram, sai ga Yesu ya gamu da su, ya ce, “Gaisuwa.” Sai suka zo kusa da shi, suka rungumi ƙafafunsa, suka yi masa sujada.


Mattiyu 28:10
Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku tafi ku gaya wa ʼyanʼuwana, su tafi Galili. A can za su gan ni.”


Mattiyu 28:16
Saʼan nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu.


Mattiyu 28:18
Sai Yesu ya zo wurinsu, ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.


Markus 1:1
Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah.


Markus 1:9
A lokacin, Yesu ya zo daga Nazaret na Galili, Yohanna kuwa ya yi masa baftisma a Urdun.


Markus 1:10
Da Yesu yana fitowa daga ruwan, sai ya ga sama ya buɗe, Ruhu kuma yana saukowa a kansa kamar kurciya.


Markus 1:14
Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah.


Markus 1:16
Yayinda Yesu yake tafiya a gaɓar Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗanʼuwansa Andarawus, suna jefa taru cikin tafkin, domin su masunta ne.


Markus 1:17
Yesu ya ce, “Ku zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.”


Markus 1:21
Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majamiʼa ya fara koyarwa.


Markus 1:24
“Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai-Mai Tsarki nan na Allah!”


Markus 1:25
Yesu ya tsauta masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!”


Markus 1:30
Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita.


Markus 1:32
A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu.


Markus 1:34
Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.


Markus 1:35
Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi adduʼa.


Markus 1:38
Yesu ya amsa, ya ce, “Mu je wani wuri dabam-zuwa ƙauyukan da suke kusa-don in yi waʼazi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.”


Markus 1:41
Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin, ya ce, “Na yarda, ka tsabtace!”


Markus 1:43
Yesu ya sallame shi nan take, da gargaɗi mai ƙarfi, cewa,


Markus 1:45
A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga koʼina.


Markus 2:1
Bayan ʼyan kwanaki, da Yesu ya sāke shiga Kafarnahum, sai mutane suka ji labarin zuwansa gida.


Markus 2:4
Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa.


Markus 2:5
Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, an gafarta zunubanka.”


Markus 2:8
Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, “Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa?


Markus 2:13
Yesu ya sāke tafiya bakin tafkin. Taro mai yawa ya zo wurinsa, sai ya fara koya musu.


Markus 2:14
Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi.


Markus 2:15
Yayinda Yesu yake cin abincin dare a gidan Lawi, sai masu karɓar haraji da “masu zunubi” da yawa, suka zo suka ci tare da shi da almajiransa, gama akwai mutane da yawa da suka bi shi.


Markus 2:17
Da jin wannan, Yesu ya ce musu, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”


Markus 2:18
To, almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, sai waɗansu mutane suka zo suka tambayi Yesu, suka ce, “Yaya almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, amma almajiranka ba sa yi?”


Markus 2:19
Yesu ya amsa, ya ce, “Yaya abokan ango za su yi azumi, saʼad da yana tare da su? Ai, ba za su yi ba, muddin yana tare da su.


Markus 2:23
Wata ranar Asabbaci, Yesu yana ratsa gonakin hatsi, sai almajiransa da suke tafiya tare da shi, suka fara kakkarya waɗansu kan hatsi.


Markus 3:2
Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci.


Markus 3:3
Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.”


Markus 3:4
Sai Yesu ya tambaye su, ya ce, “Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci: a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?” Amma suka yi shiru.


Markus 3:6
Sai Farisiyawa suka fita, suka fara ƙulla shawara da mutanen Hirudus yadda za su kashe Yesu.


Markus 3:7
Yesu da almajiransa suka janye zuwa tafkin, taro mai yawa kuwa daga Galili ya bi shi.


Markus 3:13
Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa.


Markus 3:19
da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.


Markus 3:20
Sai Yesu ya shiga wani gida, taro kuma ya sāke haɗuwa, har shi da almajiransa ma ba su sami damar cin abinci ba.


Markus 3:23
Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai, ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan?


Markus 3:31
Sai mahaifiyar Yesu tare da ʼyanʼuwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki yǎ kira shi.


Markus 4:1
Har wa yau, Yesu ya fara koyarwa a bakin tafki. Domin taron da yake kewaye da shi mai girma ne sosai, sai ya shiga cikin jirgin ruwa, ya zauna a cikin a tafkin, dukan mutanen kuwa suna a gaɓar ruwan.


Markus 4:9
Sai Yesu ya ce, “Duk mai kunnen ji, yǎ ji.”


Markus 4:13
Sai Yesu ya ce musu, “Ba ku fahimci wannan misali ba? Yaya za ku fahimci wani misali ke nan?


Markus 4:33
Da misalai da yawa irin waɗannan, Yesu ya yi magana da su, daidai yadda za su iya fahimta.


Markus 4:38
Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?”


Markus 5:2
Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi.


Markus 5:6
Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa.


Markus 5:7
Ya yi ihu da babbar murya, ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!”


Markus 5:8
Domin Yesu ya riga ya faɗa masa, cewa, “Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!”


Markus 5:9
Sai Yesu ya tambaye shi, ya ce, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa, ya ce, “Sunana Legiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.”


Markus 5:10
Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yǎ kore su daga wurin.


Markus 5:12
Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.”


Markus 5:15
Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro.


Markus 5:17
Sai mutane suka roƙi Yesu yǎ bar yankinsu.


Markus 5:18
Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yǎ bi shi.


Markus 5:19
Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.”


Markus 5:20
Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.


Markus 5:21
Da Yesu ya sāke ƙetarewa cikin jirgin ruwa zuwa ɗaya hayen tafkin, sai taro mai yawa ya taru kewaye da shi yayinda yake a bakin tafkin.


Markus 5:22
Sai ɗaya a cikin masu mulkin majamiʼa, wanda ake kira Yayirus ya zo wurin. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa a gabansa,


Markus 5:24
Sai Yesu ya tafi tare da shi. Babban taron kuma ya bi shi, suna ta matsinsa a kowane gefe.


Markus 5:27
Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa,


Markus 5:30
Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, “Wa ya taɓa rigata?”


Markus 5:32
Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yǎ ga wa ya taɓa shi.


Markus 5:35
Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majamiʼa, suka zo suka ce, “Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam.”


Markus 5:36
Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majamiʼar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”


Markus 5:38
Da suka iso gidan mai mulkin majamiʼar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa.


Markus 6:1
Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa.


Markus 6:4
Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ʼyanʼuwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.”


Markus 6:6
Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu. Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.


Markus 6:14
Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a koʼina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.”


Markus 6:30
Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar.


Markus 6:34
Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.


Markus 6:39
Saʼan nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa.


Markus 6:45
Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yǎ sallami taron.


Markus 6:47
Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai.


Markus 6:54
Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu.


Markus 7:1
Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu.


Markus 7:5
Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin alʼadun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa ‘marasa tsabta’?”


Markus 7:14
Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa, ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan.


Markus 7:19
Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, saʼan nan kuma yǎ fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.)


Markus 7:24
Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yǎ sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba.


Markus 7:26
Macen kuwa Baheleniya ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yǎ fitar da aljani da yake jikin diyarta.


Markus 7:27
Yesu ya ce mata, “Da farko, bari ʼyaʼya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.”


Markus 7:31
Sai Yesu ya bar wajajen Taya, ya bi ta Sidon har zuwa Tekun Galili da kuma cikin yankin Dekafolis.


Markus 7:33
Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin.


Markus 7:36
Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi.


Markus 8:1
A kwanakin nan wani taro mai girma ya taru. Tun da yake ba su da abin da za su ci, sai Yesu ya kira almajiransa, ya ce,


Markus 8:5
Sai Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Burodi guda nawa kuke da su?” Suka ce, “Bakwai.”


Markus 8:11
Farisiyawa suka zo suka fara yin wa Yesu tambayoyi. Don su gwada shi, sai suka nemi yǎ nuna musu wata alama daga sama.


Markus 8:15
Yesu ya gargaɗe su, ya ce, “Ku yi hankali, ku kuma lura da yistin Farisiyawa da na Hiridus.”


Markus 8:17
Da ya gane abin da suke tattaunawa, sai Yesu ya tambaye su, ya ce, “Don me kuke zancen rashin burodi? Har yanzu ba ku gane ko fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne?


Markus 8:22
Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yǎ taɓa shi.


Markus 8:23
Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi, ya ce, “Kana iya ganin wani abu?”


Markus 8:25
Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai.


Markus 8:26
Yesu ya sallame shi gida, ya ce, “Kada ka shiga cikin ƙauyen. ”


Markus 8:27
Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan da suke kewaye da Kaisariya Filibbi. A hanya ya tambaye su, ya ce, “Wa, mutane suke ce da ni?”


Markus 8:30
Yesu ya gargaɗe su kada su gaya wa kowa kome a kansa.


Markus 8:33
Amma da Yesu ya juya ya dubi almajiransa, sai ya tsauta wa Bitrus, ya ce, “Tashi daga nan Shaiɗan! Ba ka da alʼamuran Allah a zuciyarka, sai na mutane.”


Markus 9:2
Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu.


Markus 9:4
Eliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.


Markus 9:5
Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku-ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Eliya.”


Markus 9:8
Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu.


Markus 9:9
Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.


Markus 9:12
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya, Eliya zai zo da fari, yǎ kuma mayar da dukan abubuwa. Don me kuma aka rubuta cewa, dole Ɗan Mutum yǎ sha wahala sosai, kuma a ƙi shi?


Markus 9:15
Nan take da dukan mutanen suka ga Yesu, sai suka cika da mamaki, suka ruga da gudu don su gai da shi.


Markus 9:19
Yesu ya ce, “Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.”


Markus 9:20
Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa.


Markus 9:21
Yesu ya tambayi mahaifin yaron, ya ce, “Tun yaushe yake haka?” Ya ce, “Tun yana ƙarami.


Markus 9:23
Yesu ya ce, “In za ka iya? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”


Markus 9:25
Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsauta wa mugun ruhun, ya ce, “Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.”


Markus 9:27
Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa ya tashi tsaye.


Markus 9:28
Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?”


Markus 9:30
Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yǎ san inda suke ba,


Markus 9:35
Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun, ya ce, “In wani yana so yǎ zama na fari, dole yǎ zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”


Markus 9:39
Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take yǎ faɗi wani abu mummuna game da ni.


Markus 10:1
Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba.


Markus 10:5
Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka.


Markus 10:10
Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan.


Markus 10:13
Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yǎ taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su.


Markus 10:14
Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.


Markus 10:17
Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa, ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?”


Markus 10:18
Yesu ya amsa, ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari sai Allah kaɗai.


Markus 10:21
Yesu ya kalle shi da ƙauna, ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Saʼan nan ka zo ka bi ni.”


Markus 10:23
Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!”


Markus 10:24
Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “ʼYaʼyana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah!


Markus 10:27
Yesu ya kalle su, ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.”


Markus 10:29
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ʼyanʼuwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ʼyaʼya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara,


Markus 10:32
Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna binsa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi.


Markus 10:38
Yesu ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya shan kwaf da zan sha, ko a yi muku baftisma da baftismar da aka yi mini?”


Markus 10:39
Suka ce, “Za mu iya.” Yesu ya ce musu, “Za ku sha kwaf da zan sha, kuma yi muku baftisma da aka yi mini,


Markus 10:42
Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin alʼummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko.


Markus 10:46
Sai suka iso Yeriko. Saʼad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa, (wato, Ɗan Timawus), yana zaune a gefen hanya yana bara.


Markus 10:47
Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, “Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”


Markus 10:49
Yesu ya tsaya, ya ce, “Ku kira shi.” Sai suka kira makahon suka ce, “Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka.”


Markus 10:50
Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu.


Markus 10:51
Yesu ya tambaye shi, ya ce, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce, “Rabbi, ina so in sami ganin gari.”


Markus 10:52
Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.


Markus 11:1
Saʼad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa,


Markus 11:6
Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su.


Markus 11:7
Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa.


Markus 11:11
Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.


Markus 11:12
Washegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa.


Markus 11:15
Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru,


Markus 11:21
Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka laʼanta, ya yanƙwane!”


Markus 11:22
Yesu ya amsa, ya ce, “Ku gaskata da Allah.


Markus 11:27
Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa.


Markus 11:29
Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.


Markus 11:33
Don haka, suka amsa wa Yesu cewa, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”


Markus 12:13
Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hirudus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa.


Markus 12:15
Mu biya ko kada mu biya?” Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya, ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.”


Markus 12:17
Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.” Suka yi mamakinsa ƙwarai.


Markus 12:24
Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah?


Markus 12:28
Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi, ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?”


Markus 12:29
Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan: ‘Ya ku Israʼila, ku saurara, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.


Markus 12:34
Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya.


Markus 12:35
Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya, ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne?


Markus 12:38
Saʼad da Yesu yake koyarwa, ya ce, “Ku lura da malaman dokoki. Sukan so yin tafiya a manyan riguna, a kuma dinga gaishe su a wuraren kasuwanci.


Markus 12:41
Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin baitulmalin haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa.


Markus 12:43
Yesu ya kira almajiransa wurinsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin baitulmalin nan ya fi na sauran dukan.


Markus 13:2
Yesu ya amsa, ya ce, “Ka ga dukan manyan gine-ginen nan? Ba wani dutse a nan, da za a bari kan wani da ba za a rushe ba.”


Markus 13:3
Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce,


Markus 13:5
Sai Yesu ya ce musu: “Ku lura fa kada wani yǎ ruɗe ku.


Markus 14:1
To, Bikin Ƙetarewa da kuma Bikin Burodi Marar Yisti kuwa sun rage kwana biyu a yi, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suna neman wani dalilin kawai su kama Yesu, su kashe.


Markus 14:6
Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni.


Markus 14:10
Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun, ya je wajen manyan firistoci don yǎ bashe Yesu a gare su.


Markus 14:12
A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga alʼada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu yi maka shirin cin Bikin Ƙetarewa?”


Markus 14:16
Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.


Markus 14:17
Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun.


Markus 14:22
Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”


Markus 14:27
Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce, cewa: “ ‘Zan bugi makiyayin tumaki, tumakin kuwa za su warwatse.’


Markus 14:30
Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau-I, da daren nan-kafin zakara yǎ yi cara sau biyu kai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.”


Markus 14:32
Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi adduʼa.”


Markus 14:45
Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu, ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba.


Markus 14:46
Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi.


Markus 14:48
Yesu ya ce, “Ina jagoran wani tawaye ne da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni?


Markus 14:51
Wani saurayin da ba ya sanye da kome sai rigar lilin, yana bin Yesu. Da suka yi ƙoƙarin kama shi,


Markus 14:53
Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru.


Markus 14:55
Manyan firistoci da dukan ʼyan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba.


Markus 14:60
Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu, ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?”


Markus 14:61
Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba. Babban firist ya sāke tambayarsa, ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”


Markus 14:62
Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”


Markus 14:67
Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”


Markus 14:72
Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa, cewa: “Kafin zakara yǎ yi cara sau biyu: za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.


Markus 15:1
Da sassafe, sai manyan firistoci tare da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka ɗaure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus.


Markus 15:2
Bilatus ya yi tambaya, ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”


Markus 15:5
Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.


Markus 15:10
Don ya san saboda kishi ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.


Markus 15:11
Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.


Markus 15:15
Don son yǎ faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, saʼan nan ya ba da shi a gicciye.


Markus 15:16
Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya.


Markus 15:22
Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai.)


Markus 15:34
A daidai saʼa ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” Wanda yake nufin, “Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?”


Markus 15:36
Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yǎ sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Eliya zai zo yǎ saukar da shi.”


Markus 15:37
Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.


Markus 15:39
Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”


Markus 15:43
Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.


Markus 15:44
Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu.


Markus 16:1
Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu.


Markus 16:6
Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi.


Markus 16:9
Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta.


Markus 16:11
Da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su gaskata ba.


Markus 16:12
Daga baya Yesu ya bayyana a wani kamanni dabam ga biyunsu, lokacin da suke tafiya a ƙauye.


Markus 16:14
Bayan haka, Yesu ya bayyana ga Sha Ɗayan, yayinda suke cin abinci. Ya tsauta musu a kan rashin bangaskiyarsu, da yadda suka ƙi gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi.


Markus 16:19
Bayan Ubangiji Yesu ya yi musu magana, sai aka ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zauna a hannun dama na Allah.


Luka 1:31
Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu.


Luka 2:21
A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da malaʼika ya ba shi kafin a yi cikinsa.


Luka 2:27
Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Saʼad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da alʼadar Doka ta bukaci,


Luka 2:41
Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa.


Luka 2:42
Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga alʼada.


Luka 2:43
Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba.


Luka 2:52
Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.


Luka 3:21
Saʼad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin adduʼa, sai sama ya buɗe,


Luka 3:23
To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa saʼad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne, ɗan Heli,


Luka 4:1
Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada,


Luka 4:4
Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ba da burodi kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”


Luka 4:8
Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”


Luka 4:12
Yesu ya amsa, ya ce, “An ce: ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”


Luka 4:14
Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu koʼina a ƙauyuka.


Luka 4:23
Yesu ya ce musu, “Tabbatace, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ”


Luka 4:29
Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa,


Luka 4:34
“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai--Mai Tsarki na Allah!”


Luka 4:35
Yesu ya tsawata masa da ƙarfin cewa, “Yi shiru! Ka fita daga cikinsa!” Sai aljanin ya fyaɗa mutumin da ƙasa a gabansu duka, saʼan nan ya fita, ya bar shi ba wani rauni.


Luka 4:38
Yesu ya fita daga majamiʼar, ya tafi gidan Siman. Surukar Siman kuwa tana fama da zazzaɓi mai tsanani, sai suka roƙi Yesu yǎ taimake ta.


Luka 4:40
Rana tana fāɗuwa, sai mutane suka yi ta kawo wa Yesu dukan waɗanda suke da cuta iri-iri, sai ya ɗibiya wa kowannensu hannuwansa, ya warkar da su.


Luka 4:42
Da gari yana wayewa, sai Yesu ya je inda ba kowa. Mutane suka yi ta nemansa, da suka zo inda yake, sai suka yi ƙoƙari su hana shi barinsu.


Luka 5:1
Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah,


Luka 5:8
Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu, ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!”


Luka 5:10
Yaƙub da Yohanna, ʼyaʼyan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.”


Luka 5:12
Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi, ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtace ni.”


Luka 5:13
Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin, ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.


Luka 5:14
Sai Yesu ya umarce shi, ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.”


Luka 5:16
Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yǎ yi adduʼa.


Luka 5:18
Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu.


Luka 5:19
Da suka ga babu hanyar da za su yi bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu.


Luka 5:20
Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Aboki, an gafarta maka zunubanka.”


Luka 5:22
Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya, ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku?


Luka 5:27
Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.”


Luka 5:29
Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su.


Luka 5:31
Yesu ya amsa musu, ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.


Luka 5:34
Yesu ya amsa, ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su?


Luka 6:1
A wata ranar Asabbaci, Yesu yana bi ta gonakin hatsi, sai almajiran suka fara kakkarya kan hatsi suna murjewa a hannuwansu suna ci.


Luka 6:3
Yesu ya amsa musu, ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi, saʼad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa ba?


Luka 6:5
Sai Yesu ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum ne Ubangijin Asabbaci.”


Luka 6:6
A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majamiʼa yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye.


Luka 6:7
Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa.


Luka 6:8
Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.” Sai ya tashi ya tsaya.


Luka 6:9
Yesu ya ce musu, “Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci: a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?”


Luka 6:11
Amma suka fusata, suka fara shawara da junansu a kan abin da za su yi da Yesu.


Luka 6:12
Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yǎ yi adduʼa, ya kuma kwana yana adduʼa ga Allah.


Luka 6:16
Yahuda ɗan Yaƙub, da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.


Luka 7:1
Bayan Yesu ya gama gaya wa mutanen dukan waɗannan abubuwa, sai ya shiga Kafarnahum.


Luka 7:3
Jarumin sojan ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu dattawan Yahudawa wajensa, yana roƙonsa yǎ zo yǎ warkar da bawansa.


Luka 7:4
Da suka isa wurin Yesu, sai suka roƙe shi sosai, suka ce, “Wannan mutum, ai, ya dace a yi masa haka,


Luka 7:6
Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa: “Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba.


Luka 7:9
Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake binsa, “Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Israʼila ba.”


Luka 7:11
Ba a daɗe ba, sai Yesu ya tafi wani garin da ake kira Nayin. Almajiransa da taro mai yawa suka tafi tare da shi.


Luka 7:14
Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, “Saurayi, na ce maka, tashi!”


Luka 7:15
Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa.


Luka 7:17
Wannan labarin game da Yesu, ya bazu koʼina a Yahudiya da kewayenta.


Luka 7:20
Da mutanen suka iso wurin Yesu, sai suka ce, “Yohanna Mai Baftisma ne ya aike mu wurinka, mu yi tambaya, ‘Ko kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?’ ”


Luka 7:21
A daidai lokacin nan, Yesu ya warkar da mutane da yawa masu ciwo, masu cututtuka, da kuma masu mugayen ruhohi. Ya kuma ba makafi da yawa ganin gari.


Luka 7:24
Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna, ya ce: “Me kuka je ƙallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne?


Luka 7:29
(Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma.


Luka 7:36
To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur.


Luka 7:37
Da wata mace wadda ta yi rayuwar zunubi a wannan gari ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo ɗan tandun turaren alabasta,


Luka 7:40
Sai Yesu ya ce masa, “Siman, ina da abin da zan faɗa maka.” Shi kuwa ya ce, “Malam sai ka faɗa.”


Luka 7:41
Yesu ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu da suke riƙe bashin mai ba da rance. Ana bin guda dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin.


Luka 7:43
Siman ya amsa, ya ce, “A ganina, wanda aka yafe wa mai yawa ne.” Sai Yesu ya ce, “Ka faɗi daidai.”


Luka 7:48
Sai Yesu ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”


Luka 7:50
Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki tafi da salama.”


Luka 8:1
Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana waʼazin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi,


Luka 8:4
Yayinda taron mai girma na taruwa, mutane kuma daga garuruwa dabam-dabam suna zuwa wurin Yesu, sai ya ba da wannan misali, ya ce,


Luka 8:19
Sai uwar Yesu da ʼyanʼuwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron.


Luka 8:22
Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya.


Luka 8:27
Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin: Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura.


Luka 8:28
Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!”


Luka 8:29
Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun yakan sha kamunsa. Ko da yake akan ɗaure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa.


Luka 8:30
Yesu ya tambaye shi, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa, “Legiyon,” wato, “Tuli,” gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa.


Luka 8:32
A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu.


Luka 8:35
Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.


Luka 8:37
Sai dukan mutanen yankin Gerasenawa suka roƙi Yesu ya bar su, don sun tsorata sosai. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa ya tafi.


Luka 8:38
Mutumin da aka fitar da aljanun daga cikinsa, ya roƙi Yesu don ya tafi tare da shi, amma Yesu ya sallame shi, ya ce,


Luka 8:39
“Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin.


Luka 8:40
Da Yesu ya koma, taron suka marabce shi, don dā ma duk suna jiransa.


Luka 8:41
Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majamiʼa, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa,


Luka 8:42
domin diyarsa ɗaya tak, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu yake kan hanyarsa, taron mutane masu yawa suka yi ta matsa shi a kowane gefe.


Luka 8:45
Yesu ya yi tambaya, “Wa ya taɓa ni?” Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, “Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe.”


Luka 8:46
Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.”


Luka 8:48
Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki tafi cikin salama.”


Luka 8:49
Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majamiʼar, ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.”


Luka 8:50
Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”


Luka 8:52
Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba ta mutu ba, tana barci ne.”


Luka 8:54
Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, ki tashi.”


Luka 8:55
Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu ta ci.


Luka 9:1
Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka.


Luka 9:9
Amma Hiridus, ya ce, “Yohanna dai na yanke kansa, amma wanne mutum ne nake jin labarin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ƙoƙari ya ga Yesu.


Luka 9:10
Da manzannin suka dawo, sai suka faɗa wa Yesu abin da suka yi. Sai ya ɗauke su, suka keɓe kansu su kaɗai, zuwa wani gari da ake kira Betsaida.


Luka 9:13
Yesu ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Sai suka ce masa, “Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron.”


Luka 9:16
Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen.


Luka 9:18
Wata rana saʼad da Yesu yana adduʼa a ɓoye, almajiransa kuma suna tare da shi, sai ya tambaye, su ya ce, “Wa, taron mutane ke ce da ni?”


Luka 9:21
Yesu ya gargaɗe su da ƙarfi, kada su gaya wa kowa wannan magana.


Luka 9:28
Bayan kamar kwana takwas da yin wannan magana, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yohanna, da kuma Yaƙub, suka hau kan dutse tare don yin adduʼa.


Luka 9:31
suka bayyana cikin kyakkyawar daraja, suna magana da Yesu. Suka yi zance a kan tashinsa, wanda shi ya kusan ya kawo ga cikarsa a Urushalima.


Luka 9:33
Da mutanen na barin Yesu, sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, wato, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Eliya.” (Bai ma san abin da yake faɗi ba.)


Luka 9:36
Da muryar ta gama magana, sai suka tarar Yesu shi kaɗai ne. Almajiran kuwa suka riƙe wannan alʼamari a zukatansu. A lokacin nan, ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.


Luka 9:37
Washegari, saʼad da Yesu tare da almajiran nan uku suka sauka daga kan dutsen, sai taro mai yawa ya haɗu da shi.


Luka 9:41
Yesu ya amsa, ya ce, “Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan.”


Luka 9:42
Yaron yana kan zuwa ke nan, sai aljanin ya buga shi ƙasa, cikin farfaɗiya. Amma Yesu ya kwaɓe mugun ruhun, ya warkar da yaron, sai ya miƙa shi ga mahaifinsa.


Luka 9:43
Duk suka yi mamakin girman Allah. Yayinda kowa yana cikin mamakin dukan abubuwan da Yesu ya yi, sai ya ce wa almajiransa,


Luka 9:47
Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi.


Luka 9:50
Yesu ya ce, “Kada ku hana shi, gama duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”


Luka 9:51
Da lokaci ya yi kusa da za a ɗauki Yesu zuwa sama, sai ya ɗaura niyyar tafiya Urushalima.


Luka 9:55
Amma Yesu ya juya, ya kwaɓe su.


Luka 9:58
Yesu ya amsa, ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama kuma suna da sheƙa, wato, wurin kwanansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa ba.”


Luka 9:60
Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”


Luka 9:62
Yesu ya amsa, ya ce, “Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, saʼan nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba.”


Luka 10:21
A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau.


Luka 10:25
Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don ya gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?”


Luka 10:26
Yesu ya amsa, ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?”


Luka 10:28
Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.”


Luka 10:29
Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu, ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?”


Luka 10:30
Yesu ya amsa, ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ʼyan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa duka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa.


Luka 10:37
Masanin dokoki ya amsa, ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.”


Luka 10:38
Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta.


Luka 10:40
Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ʼyarʼuwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”


Luka 11:1
Wata rana Yesu yana adduʼa a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin adduʼa, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.”


Luka 11:14
Saʼad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.


Luka 11:17
Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe.


Luka 11:27
Da Yesu yake cikin faɗin waɗannan abubuwa, sai wata mace daga cikin taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Mai albarka ce uwar da ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”


Luka 11:28
Yesu ya amsa, ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.”


Luka 11:29
Da taron mutane suka ƙaru, sai Yesu ya ce, “Wannan mugun zamani ne. Tana neman wata abin banmamaki, amma ba ko ɗaya da za a ba ta, sai dai ta Yunana.


Luka 11:37
Da Yesu ya gama magana, sai wani Bafarisiye ya gayyace shi cin abinci tare da shi. Sai kuwa ya shiga ya zauna a tebur.


Luka 11:38
Amma Bafarisiyen ya lura cewa, Yesu bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba, sai mamaki ya kama shi.


Luka 11:45
Sai ɗaya daga cikin masanan dokoki ya ce wa Yesu, “Malam, in ka faɗi waɗannan abubuwa haka, kai kuma ka zage mu ke nan.”


Luka 11:46
Yesu ya amsa, ya ce, “Ku masanan dokoki ma, kaitonku, domin kun ɗora wa mutane kaya masu nauyi waɗanda da ƙyar suke ɗaukawa, amma ku da kanku ba za ku sa ko yatsa ɗaya, don ku taimake su ba.


Luka 11:53
Da Yesu ya bar wurin, sai Farisiyawa da malaman dokoki suka fara gaba mai tsanani da shi, kuma suna tsokanansa da tambayoyi.


Luka 12:1
Ana nan saʼad da taron dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, Yesu fara yin magana, da farko da almajiransa, ya ce, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, munafunci.


Luka 12:14
Yesu ya amsa masa, ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?”


Luka 12:22
Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa.


Luka 13:1
A yanzun fa, akwai waɗansu da suka kasance a lokacin can, suka ba Yesu labarin Galiliyawa da Bilatus ya garwaya jininsu tare da jinin hadayunsu.


Luka 13:2
Yesu ya amsa, ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galiliyawan sun fi dukan sauran Galiliyawa zunubi ne, shi ya sa suka sha irin wannan wahala?


Luka 13:10
Wata ranar Asabbaci, Yesu yana koyarwa a wata majamiʼa,


Luka 13:12
Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, “Mace, an ʼyantar da ke daga rashin lafiyarki.”


Luka 13:14
Amma mai mulkin majamiʼar ya ji haushi da Yesu ya yi warkarwa a ranar Asabbaci. Sai ya ce wa mutanen, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Saboda haka, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba ranar Asabbaci ba.”


Luka 13:18
Sai Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi?


Luka 13:22
Saʼad da Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi ta cikin garuruwan da ƙauyukan, yana koyarwa.


Luka 13:31
A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.”


Luka 14:1
Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau.


Luka 14:3
Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa, ya ce, “Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?”


Luka 14:12
Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, “Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ʼyanʼuwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu.


Luka 14:15
Da jin haka, sai wani da yake tare da shi a tebur ɗin, ya ce wa Yesu, “Mai albarka ne wanda zai ci abinci a bikin nan a mulkin Allah.”


Luka 14:16
Yesu ya amsa, ya ce, “Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa.


Luka 14:25
Taron mutane mai yawa suna tafiya tare da Yesu, sai ya juya ya ce musu,


Luka 15:1
Yanzu fa, masu karɓar haraji da “masu zunubi” duka suna taruwa don jin koyarwar Yesu.


Luka 15:3
Sai Yesu ya faɗa musu wannan misali, ya ce,


Luka 15:11
Yesu ya ci gaba da cewa, “Akwai wani mutum wanda yake da ʼyaʼya biyu maza.


Luka 16:1
Yesu ya ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki wanda aka yi wa manajansa zargin yin banza da dukiyarsa.


Luka 16:14
Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki.


Luka 17:1
Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwa da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa.


Luka 17:11
Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili.


Luka 17:13
suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!”


Luka 17:16
Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.


Luka 17:17
Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtace ba? Ina sauran taran?


Luka 17:20
Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin ƙallon ku ba.


Luka 18:1
Yesu ya faɗa wa almajiransa wani misali, don ya koya musu yadda ya kamata su dinga yin adduʼa kullum, ban da fasawa.


Luka 18:9
Yesu ya kuma faɗi wannan misali ga waɗansu masu taƙama da adalcinsu, kuma suna rena sauran mutane, ya ce,


Luka 18:15
Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don ya taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su.


Luka 18:16
Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa, ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.


Luka 18:18
Wani mai mulki ya tambayi Yesu, ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”


Luka 18:19
Yesu ya amsa, ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, babu wani managarci, sai Allah kaɗai.


Luka 18:22
Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, saʼan nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”


Luka 18:24
Yesu ya kalle shi, ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah!


Luka 18:27
Yesu ya amsa, ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”


Luka 18:29
Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ʼyanʼuwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah,


Luka 18:35
Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara.


Luka 18:37
Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.”


Luka 18:38
Sai ya yi kira, ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”


Luka 18:40
Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi, ya ce,


Luka 18:42
Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”


Luka 18:43
Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.


Luka 19:1
Yesu ya shiga Yeriko, yana ratsa ta cikinta.


Luka 19:3
Ya so ya ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne.


Luka 19:4
Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don ya gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne.


Luka 19:5
Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.”


Luka 19:9
Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne.


Luka 19:28
Bayan Yesu ya yi wannan magana, sai ya yi gaba zuwa Urushalima.


Luka 19:35
Suka kawo shi wurin Yesu. Suka sa rigunarsu a kan ɗan jakin, saʼan nan suka sa Yesu a kai.


Luka 19:39
Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!”


Luka 20:1
Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu waʼazin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa.


Luka 20:8
Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”


Luka 20:17
Yesu ya zura musu ido, ya ce, “To, mene ne maʼanar abin da aka rubuta cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin  ’?


Luka 20:27
Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa,


Luka 20:34
Yesu ya amsa, ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure,


Luka 20:41
Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’


Luka 20:45
Yayinda dukan mutane suna cikin sauraronsa, sai Yesu ya ce wa almajiransa,


Luka 21:1
Da Yesu ya ɗaga ido, sai ya ga waɗansu masu arziki suna sa baikonsu a maʼajiyin haikalin.


Luka 21:5
Waɗansu daga cikin almajiransa, suka fara magana a kan yadda aka yi wa haikalin ado da duwatsu masu kyau, da kuma kyautai da aka keɓe wa Allah. Amma Yesu ya ce,


Luka 21:37
Kowace rana, Yesu yakan je haikalin ya yi koyarwa, da kowace yamma kuma, ya je ya kwana a kan tudun da ake kira Dutsen Zaitun.


Luka 22:2
manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane.


Luka 22:4
Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da maʼaikatan ʼyan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su.


Luka 22:6
Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, saʼad da taro ba sa nan tare da shi.


Luka 22:8
Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna, ya ce musu, “Ku je ku yi shirye-shiryen Bikin Ƙetarewa da za mu ci.”


Luka 22:13
Sai suka tafi, suka kuma iske kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.


Luka 22:14
Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa a tebur.


Luka 22:25
Yesu ya ce musu, “Sarakunan Alʼummai suna nuna iko a kan mutanensu, kuma waɗanda suke nuna iko a kansu, suna kiran kansu Masu Taimakon mutane.


Luka 22:34
Yesu ya ce, “Ina gaya maka Bitrus, kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.”


Luka 22:35
Sai Yesu ya tambaye, su ya ce, “Lokacin da na aike ku ba tare da jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma ba, kun rasa wani abu?” Suka amsa, “Babu.”


Luka 22:38
Almajiran suka ce, “Duba Ubangiji, ga takuba biyu.” Yesu ya ce, “Ya isa.”


Luka 22:39
Yesu ya fita zuwa Dutsen Zaitun kamar yadda ya saba, almajiransa kuma suka bi shi.


Luka 22:47
Yana cikin magana sai ga taro sun zo. Mutumin nan da ake kira Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun, shi ya bi da su. Sai ya matso kusa da Yesu don ya yi masa sumba.


Luka 22:48
Amma Yesu ya tambaye shi, ya ce, “Yahuda, ashe, da sumba za ka bashe Ɗan Mutum?”


Luka 22:49
Da masu bin Yesu suka ga abin da zai faru, sai suka ce, “Ubangiji, mu yi sara da takubanmu ne?”


Luka 22:51
Amma Yesu ya amsa, ya ce, “Kada a ƙara yin wannan haka!” Sai ya taɓa kunnen mutumin da aka sara, ya warkar da shi.


Luka 22:52
Sai Yesu ya ce wa manyan firistoci, da maʼaikatan ʼyan gadin haikali, da dattawa, waɗanda suka zo don su kama shi: “Ina jagoran wani tawaye ne, da za ku zo da takuba da sanduna?


Luka 22:63
Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa baʼa da duka.


Luka 22:66
Da gari ya waye, sai majalisar dattawa na mutane, da manyan firistoci, da malaman dokoki, suka taru wuri ɗaya. Sai aka kawo Yesu a gabansu.


Luka 22:67
Suka ce, “Ka faɗa mana, ko kai ne Kiristi?” Yesu ya amsa, ya ce, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ni ba,


Luka 23:3
Sai Bilatus ya tambayi Yesu, ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”


Luka 23:7
Da ya ji cewa, Yesu yana ƙarƙashin mulkin Hiridus, sai ya aika da shi zuwa wurin Hiridus, don a lokacin kuwa Hiridus yana Urushalima.


Luka 23:8
Da Hiridus ya ga Yesu, sai ya yi murna ƙwarai, don tun dā ma yana marmari ya gan shi. A kan abin da ya ji game da shi, ya yi fata ya ga Yesu, ya yi waɗansu ayyukan banmamaki.


Luka 23:9
Ya yi masa tambayoyi masu yawa, amma Yesu bai bashi ko amsa ba.


Luka 23:20
Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu.


Luka 23:25
Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda ta da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Saʼan nan ya ba da Yesu ga nufinsu.


Luka 23:26
Saʼad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya.


Luka 23:28
Yesu ya juya, ya ce musu, “ʼYan matan Urushalima, kada ku yi kuka saboda ni, amma ku yi kuka saboda kanku, da kuma saboda ʼyaʼyanku.


Luka 23:34
Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuriʼa.


Luka 23:42
Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni saʼad da ka shiga mulkinka.”


Luka 23:43
Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”


Luka 23:46
Yesu ya yi kira da babbar murya, ya ce, “Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.” Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.


Luka 23:49
Amma dukan mutanen da suka san Yesu, tare da mata da suka bi shi daga Galili, suka tsaya daga nesa suna ƙallon abubuwan nan.


Luka 23:52
Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu.


Luka 23:55
Matan da suka zo tare da Yesu, daga Galili suka bi Yusuf suka ga kabarin, da kuma yadda aka ajiye jikin.


Luka 24:3
Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba.


Luka 24:15
Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su.


Luka 24:19
Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?” Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane.


Luka 24:28
Da suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai Yesu ya yi kamar zai ci gaba.


Luka 24:35
Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin.


Luka 24:36
Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, “Salama a gare ku!”


Yohanna 1:17
Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi.


Yohanna 1:29
Washegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!


Yohanna 1:36
Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!”


Yohanna 1:37
Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.


Yohanna 1:38
Da juyewa, sai Yesu ya ga suna binsa, sai ya tambaye, su ya ce, “Me kuke nema?” Suka ce, “Rabbi,” (wato, Malam), “ina kake da zama?”


Yohanna 1:40
Andarawus ɗanʼuwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun da suka ji abin da Yohanna ya faɗa wanda kuma ya bi Yesu.


Yohanna 1:42
Ya kuma kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan  ).


Yohanna 1:43
Washegari Yesu ya yanke shawara yǎ tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, “Bi ni.”


Yohanna 1:45
Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa-Yesu Banazare, ɗan Yusuf.”


Yohanna 1:47
Da Yesu ya ga Natanayel yana zuwa, sai ya yi magana game da shi cewa, “Ga mutumin Israʼila na gaske wanda ba shi da haʼinci.”


Yohanna 1:48
Natanayel ya yi tambaya, ya ce, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa, ya ce, “Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yǎ kira ka.”


Yohanna 1:50
Yesu ya ce, “Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka.”


Yohanna 2:1
A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can,


Yohanna 2:2
aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren.


Yohanna 2:3
Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”


Yohanna 2:4
Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.”


Yohanna 2:7
Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika randunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal.


Yohanna 2:11
Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.


Yohanna 2:13
Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima.


Yohanna 2:19
Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke ta da shi cikin kwana uku.”


Yohanna 2:22
Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Saʼan nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi.


Yohanna 2:24
Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane.


Yohanna 3:2
Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”


Yohanna 3:3
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”


Yohanna 3:5
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.


Yohanna 3:10
Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Israʼila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba?


Yohanna 3:22
Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan Yahudiya, inda ya ɗan jima da su, ya kuma yi baftisma.


Yohanna 4:1
Sai Farisiyawa suka ji cewa Yesu yana samun yana kuma yi wa almajirai da yawa baftisma fiye da Yohanna,


Yohanna 4:2
ko da yake ba Yesu ne yake baftismar ba, sai almajiransa.


Yohanna 4:6
Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen saʼa ta shida ne.


Yohanna 4:7
Saʼad da wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Za ki ba ni ruwa in sha?”


Yohanna 4:10
Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, da shi kuwa ya ba ki ruwan rai.”


Yohanna 4:13
Yesu ya amsa, ya ce, “Kowa da ya sha wannan ruwa zai sāke jin ƙishirwa,


Yohanna 4:17
Ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Sai Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji.


Yohanna 4:21
Sai Yesu ya ce, “Ina tabbatar miki, mace, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a kan dutsen nan ko kuma a Urushalima ba.


Yohanna 4:26
Sai Yesu ya ce, “Ai, ni ɗin nan da yake magana da ke, Ni ne shi.”


Yohanna 4:34
Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.


Yohanna 4:44
(To, Yesu kansa ya taɓa faɗa cewa annabi ba shi da daraja a ƙasarsa).


Yohanna 4:47
Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yǎ zo yǎ warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.


Yohanna 4:48
Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”


Yohanna 4:50
Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.” Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi.


Yohanna 4:53
Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.


Yohanna 4:54
Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili.


Yohanna 5:1
Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa.


Yohanna 5:6
Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, “Kana so ka warke?”


Yohanna 5:8
Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.”


Yohanna 5:13
Mutumin da aka warkar kuwa bai ma san ko wane ne ba ne, gama Yesu ya ɓace cikin taron da yake can.


Yohanna 5:14
Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, “Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in da haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.”


Yohanna 5:15
Sai mutumin ya je ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkar da shi.


Yohanna 5:16
To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa.


Yohanna 5:17
Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yǎ zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.”


Yohanna 5:19
Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi.


Yohanna 6:1
Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya),


Yohanna 6:3
Saʼan nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa.


Yohanna 6:5
Saʼad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?”


Yohanna 6:10
Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.


Yohanna 6:11
Saʼan nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.


Yohanna 6:14
Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, “Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.”


Yohanna 6:15
Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.


Yohanna 6:17
inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna.


Yohanna 6:19
Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata.


Yohanna 6:22
Washegari taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka lura cewa jirgin ruwa ɗaya ne yake a can dā ma, kuma sun lura cewa Yesu bai shiga ciki tare da almajiransa ba, gama sun tashi su kaɗai.


Yohanna 6:24
Da taron suka lura cewa Yesu da almajiransa ba sa can, sai suka shiga jiragen ruwa suka tafi Kafarnahum neman Yesu.


Yohanna 6:26
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga abubuwan banmamaki ba, sai dai domin kun ci burodi kun ƙoshi.


Yohanna 6:29
Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne: a gaskata da wanda ya aiko.”


Yohanna 6:32
Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama.


Yohanna 6:35
Saʼan nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.


Yohanna 6:42
Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’ ”


Yohanna 6:43
Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku.


Yohanna 6:53
Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai dai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.


Yohanna 6:61
Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne?


Yohanna 6:64
Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi.


Yohanna 6:67
Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?”


Yohanna 6:70
Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ba ni na zaɓe ku Sha Biyu ba? Amma ɗayanku Iblis ne!”


Yohanna 7:1
Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yǎ je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi.


Yohanna 7:3
sai ʼyanʼuwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi.


Yohanna 7:6
Saboda haka Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna; amma a gare ku kowane lokaci daidai ne.


Yohanna 7:14
Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, saʼan nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa.


Yohanna 7:16
Yesu ya amsa, ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni.


Yohanna 7:21
Yesu ya ce musu, “Na yi abin banmamaki ɗaya, dukanku kuwa kuka yi mamaki.


Yohanna 7:28
Yesu yana cikin koyarwa a filin haikali ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “I, kun san ni, kun kuma san inda na fito. Ban zo don kaina ba, sai dai shi da ya aiko ni mai gaskiya ne. Ba ku san shi ba,


Yohanna 7:33
Sai Yesu ya ce, “Ina tare da ku na ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai, saʼan nan zan koma wurin wanda ya aiko ni.


Yohanna 7:37
A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yǎ zo wurina yǎ sha.


Yohanna 7:39
Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yǎ zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.


Yohanna 7:43
Sai mutanen suka rabu saboda Yesu.


Yohanna 7:50
Nikodimus, wanda ya je wurin Yesu dā, wanda kuma yake ɗayansu ya ce,


Yohanna 8:1
Amma Yesu ya tafi Dutsen Zaitun.


Yohanna 8:4
suka kuma ce wa Yesu, “Malam, an kama wannan mace tana zina.


Yohanna 8:6
Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi. Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa.


Yohanna 8:9
Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya. Manyan da farko, har sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin.


Yohanna 8:10
Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta, “Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”


Yohanna 8:11
Ta ce, “Ba kowa, ranka yǎ daɗe.” Sai Yesu ya ce, “Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi.”


Yohanna 8:12
Saʼad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yǎ sami hasken rayuwa.”


Yohanna 8:14
Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, gama na san inda na fito da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ko inda za ni ba.


Yohanna 8:19
Suka tambaye shi suka ce, “Ina Uban nan naka?” Sai Yesu ya ce, “Ba ku san ni ko Ubana ba. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma.”


Yohanna 8:21
Har wa yau Yesu ya sāke ce musu, “Zan tafi, za ku kuwa neme ni, za ku kuma mutu cikin zunubinku. Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba.”


Yohanna 8:25
Suka ce, “Wane ne kai?” Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ni ne wannan da na sha faɗi muku.


Yohanna 8:28
Saboda haka Yesu ya ce, “Saʼad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a saʼan nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini.


Yohanna 8:31
Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske.


Yohanna 8:34
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.


Yohanna 8:39
Suka ce, “To, ai, Ibrahim ne mahaifinmu.” Yesu ya ce, “Da ku ʼyaʼyan Ibrahim ne, da za ku aikata abubuwan da Ibrahim ya yi.


Yohanna 8:42
Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni.


Yohanna 8:49
Yesu ya ce, “Ni ba mai aljani ba ne, ni dai ina girmama Ubana, ku kuwa ba kwa girmama ni.


Yohanna 8:54
Yesu ya amsa, ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni.


Yohanna 8:58
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, Ni ne!”


Yohanna 8:59
Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali.


Yohanna 9:3
Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa.


Yohanna 9:11
Ya amsa ya ce, “Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari.”


Yohanna 9:14
To, a ranar da Yesu ya kwaɓa laka ya buɗe idanun mutumin ranar Asabbaci ce.


Yohanna 9:22
Iyayensa sun faɗa haka ne saboda suna tsoron Yahudawa, gama Yahudawa sun riga sun yanke shawara cewa duk wanda ya yarda cewa Yesu shi ne Kiristi, za a kore da shi daga majamiʼa.


Yohanna 9:35
Yesu ya ji labari cewa sun kore shi, da ya same shi kuwa, sai ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum?”


Yohanna 9:37
Yesu ya ce, “Yanzu ka gan shi; tabbatacce ma, shi ne yake magana da kai.”


Yohanna 9:39
Yesu ya ce, “Saboda shariʼa ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance.”


Yohanna 9:41
Yesu ya ce, “Ai, da ku makafi ne ma, da ba ku da zunubi, amma da yake kun ce, kuna gani, zunubanku suna nan daram.


Yohanna 10:6
Yesu ya yi wannan karin maganar, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.


Yohanna 10:7
Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.


Yohanna 10:23
Yesu kuwa yana a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon.


Yohanna 10:25
Yesu ya amsa, ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan banmamakin da nake yi cikin sunan Ubana suna shaida ni,


Yohanna 10:32
amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku manyan ayyukan banmamaki daga wurin Uba. A kan wanne a cikinsu kuke so ku jajjefe ni?”


Yohanna 10:34
Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?


Yohanna 10:40
Saʼan nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna


Yohanna 10:42
A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu.


Yohanna 11:3
Saboda haka ʼyanʼuwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, ga wanda kake ƙauna yana rashin lafiya.”


Yohanna 11:4
Saʼad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. Aʼa, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan.”


Yohanna 11:5
Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ʼyarʼuwarta da kuma Lazarus.


Yohanna 11:9
Yesu ya amsa, ya ce, “Ba saʼa goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba domin yana ganin hasken duniyan nan.


Yohanna 11:13
Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.


Yohanna 11:17
Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari.


Yohanna 11:20
Saʼad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida.


Yohanna 11:21
Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗanʼuwana bai mutu ba.


Yohanna 11:23
Yesu ya ce mata, “Ɗanʼuwanki zai sāke tashi.”


Yohanna 11:25
Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;


Yohanna 11:30
Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi.


Yohanna 11:32
Saʼad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗanʼuwana bai mutu ba.”


Yohanna 11:33
Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu.


Yohanna 11:35
Yesu ya yi kuka.


Yohanna 11:38
Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse.


Yohanna 11:39
Sai Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Marta, ʼyarʼuwan mamacin ta ce, “Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can.”


Yohanna 11:40
Sai Yesu ya ce, “Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?”


Yohanna 11:41
Saboda haka suka kawar da dutsen. Saʼan nan Yesu ya dubi sama ya ce, “Uba, na gode maka da ka saurare ni.


Yohanna 11:43
Saʼad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!”


Yohanna 11:44
Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a ɗaure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tube kayan bizo, ku bar shi yǎ tafi.”


Yohanna 11:45
Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi.


Yohanna 11:46
Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi.


Yohanna 11:51
Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa,


Yohanna 11:54
Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa.


Yohanna 11:56
Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?”


Yohanna 11:57
Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yǎ faɗa don su kama shi.


Yohanna 12:1
Kwana shida kafin Bikin Ƙetarewa, sai Yesu ya iso Betani, inda Lazarus yake, wanda Yesu ya ta da daga matattu.


Yohanna 12:2
A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi.


Yohanna 12:3
Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi tsantsa, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.


Yohanna 12:7
Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar janaʼizata.


Yohanna 12:9
Ana cikin haka sai babban taron Yahudawa suka sami labari Yesu yana can suka kuwa zo, ba kawai don shi ba amma don su kuma ga Lazarus, wanda ya ta da daga matattu.


Yohanna 12:11
gama dalilinsa Yahudawa da yawa suna komawa ga Yesu suna kuma ba da gaskiya gare shi.


Yohanna 12:12
Washegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima.


Yohanna 12:14
Yesu ya sami ɗan jaki, ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa,


Yohanna 12:16
Da fari almajiransa ba su gane dukan wannan ba. Sai bayan da aka ɗaukaka Yesu, saʼan nan suka gane cewa an rubuta waɗannan abubuwa game da shi ne, har ma suka yi masa waɗannan abubuwa.


Yohanna 12:21
Suka zo wurin Filibus, wanda yake daga Betsaida ta Galili, da roƙo. Suka ce, “Ranka yǎ daɗe, muna so mu ga Yesu.”


Yohanna 12:22
Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawus, Andarawus da kuma Filibus suka gaya wa Yesu.


Yohanna 12:23
Yesu ya amsa, ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum.


Yohanna 12:30
Yesu ya ce, “An yi wannan muryar saboda amfaninku ne, ba don nawa ba.


Yohanna 12:35
Sai Yesu ya faɗa musu, “Haske zai kasance da ku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya yayinda hasken yana nan tare da ku, kada duhu yǎ cim muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda za shi ba.


Yohanna 12:36
Ku dogara ga hasken yayinda kuke da shi, don ku zama ʼyaʼyan haske.” Da Yesu ya gama magana, sai ya tafi ya ɓuya daga gare su.


Yohanna 12:37
Ko bayan Yesu ya yi dukan waɗannan abubuwan banmamaki a gabansu, duk da haka ba su gaskata da shi ba.


Yohanna 12:41
Ishaya ya faɗi haka ne, saboda ya hangi ɗaukakar Yesu, ya kuwa yi magana a kansa.


Yohanna 12:44
Saʼan nan Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Duk wanda ya gaskata da ni, ba ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne.


Yohanna 13:1
Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yǎ koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa.


Yohanna 13:2
Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya iza Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yǎ bashe Yesu.


Yohanna 13:3
Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah;


Yohanna 13:7
Yesu ya amsa, ya ce, “Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane.”


Yohanna 13:8
Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.” Yesu ya amsa, ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.”


Yohanna 13:10
Yesu ya amsa, ya ce, “Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata yǎ wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba.”


Yohanna 13:21
Bayan ya faɗi haka, sai Yesu ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”


Yohanna 13:23
Sai ɗaya daga cikin almajiran, wanda Yesu yake ƙauna, yana zaune kusa da shi.


Yohanna 13:25
Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu ya ce, “Ubangiji, wane ne?”


Yohanna 13:26
Yesu ya amsa, ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan saʼad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman.


Yohanna 13:27
Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi. Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi maza ka yi shi,”


Yohanna 13:28
amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka.


Yohanna 13:29
Da yake Yahuda ne maʼaji, waɗansu sun ɗauka, Yesu yana ce masa yǎ sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yǎ ba wa matalauta wani abu.


Yohanna 13:31
Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa.


Yohanna 13:36
Siman Bitrus ya tambaye shi ya ce, “Ubangiji ina za ka?” Yesu ya amsa, ya ce, “Wurin da za ni, ba za ka iya zuwa yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.”


Yohanna 13:38
Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku!


Yohanna 14:6
Yesu ya amsa, ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.


Yohanna 14:9
Yesu ya amsa, ya ce: “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’?


Yohanna 14:23
Yesu ya amsa, ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi.


Yohanna 16:19
Yesu ya gane suna so su tambaye shi game da wannan, sai ya ce musu, “Kuna tambayar juna game da abin da nake nufi da na ce, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara gani na ba,’ da kuma, ‘Bayan an jima kaɗan, za ku gan ni’?


Yohanna 16:29
Sai almajiran Yesu suka ce, “Haba, yanzu ne fa kake magana a sarari ba tare da misalai ba.


Yohanna 16:31
Yesu ya amsa, ya ce, “A ƙarshe kun gaskata!


Yohanna 17:1
Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi adduʼa, ya ce: “Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yǎ ɗaukaka ka.


Yohanna 17:3
Rai madawwami kuwa shi ne: su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko.


Yohanna 18:1
Da ya gama adduʼa, sai Yesu ya fita tare da almajiransa suka haye Kwarin Kidron. A wancan ƙetaren kuwa akwai lambun zaitun, da shi da almajiransa suka shiga ciki.


Yohanna 18:2
To, Yahuda, wanda ya bashe shi, ya san wurin, domin Yesu ya sha zuwa wurin da almajiransa.


Yohanna 18:4
Yesu kuwa, sane da duk abin da zai same shi, ya fito ya tambaye, su ya ce, “Wa kuke nema?”


Yohanna 18:5
Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce, “Ni ne.” (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.)


Yohanna 18:6
Da Yesu ya ce, “Ni ne,” sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa.


Yohanna 18:7
Sai ya sāke tambayar su ya ce, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.”


Yohanna 18:8
Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, na gaya muku ni ne. In kuma ni ne kuke nema, sai ku bar waɗannan su tafi.”


Yohanna 18:11
Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?”


Yohanna 18:12
Sai ƙungiyar soja tare da shugaban sojanta da kuma maʼaikatan Yahudawa suka kama Yesu. Suka ɗaure shi


Yohanna 18:15
Siman Bitrus da kuma wani almajiri suna bin Yesu. Domin almajirin nan sananne ne ga babban firist, sai ya shiga tare da Yesu a filin gidan babban firist ɗin,


Yohanna 18:19
Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa.


Yohanna 18:20
Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majamiʼu ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba.


Yohanna 18:22
Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin maʼaikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”


Yohanna 18:23
Yesu ya amsa, ya ce, “In na faɗi abin da ba daidai ba, ka nuna abin da ba daidai ba. Amma in gaskiya na faɗa, don me ka mare ni?”


Yohanna 18:28
Saʼan nan Yahudawa suka fitar da Yesu daga wurin Kayifas zuwa fadar gwamnar Roma. A yanzu dai, safiya ta yi, don gudu kada su ƙazantar da kansu Yahudawa ba su shiga cikin fadar ba; sun so su iya ci Bikin Ƙetarewa.


Yohanna 18:32
Wannan kuwa ya faru ne don a cika kalmomin da Yesu ya yi da suka nuna irin mutuwar da zai yi.


Yohanna 18:33
Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?”


Yohanna 18:34
Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Wannan raʼayin kanka ne, ko waɗansu ne suka yi maka magana game da ni?”


Yohanna 18:36
Yesu ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.”


Yohanna 18:37
Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!” Yesu ya amsa, ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.”


Yohanna 19:1
Saʼan nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala.


Yohanna 19:5
Saʼad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai launin shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”


Yohanna 19:9
sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba.


Yohanna 19:11
Yesu ya amsa, ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”


Yohanna 19:12
Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yǎ saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”


Yohanna 19:13
Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shariʼar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Aramayik ana ce da shi Gabbata).


Yohanna 19:16
A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu.


Yohanna 19:18
Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu-ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.


Yohanna 19:19
Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne: “YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA.”


Yohanna 19:20
Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Aramayanci, Romanci da kuma Helenanci.


Yohanna 19:23
Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.


Yohanna 19:25
To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ʼyarʼuwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin.


Yohanna 19:26
Saʼad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Ya mace, ga ɗanki,”


Yohanna 19:28
Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”


Yohanna 19:29
Akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hissof, suka kai bakin Yesu.


Yohanna 19:30
Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.


Yohanna 19:32
Sai sojoji suka zo suka karya ƙafafun mutum na farko da aka gicciye tare da Yesu, da kuma na ɗayan.


Yohanna 19:33
Amma saʼad da suka zo kan Yesu suka tarar ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba.


Yohanna 19:34
A maimako, sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefe da māshi, nan take jini da ruwa suka fito.


Yohanna 19:38
Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin.


Yohanna 19:39
Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari.


Yohanna 19:40
Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga alʼadar Yahudawa ta janaʼiza.


Yohanna 19:41
A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba.


Yohanna 19:42
Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can.


Yohanna 20:2
Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!”


Yohanna 20:7
haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin.


Yohanna 20:9
(Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yǎ tashi daga matattu ba.)


Yohanna 20:12
sai ta ga waɗansu malaʼiku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu.


Yohanna 20:14
Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba ta gane cewa Yesu ne ba.


Yohanna 20:16
Yesu ya ce mata, “Maryamu.” Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Aramayanci, “Rabboni” (wanda yake nufin Malam).


Yohanna 20:17
Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ʼyanʼuwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ”


Yohanna 20:19
Da Yamman ranar farko ta mako, saʼad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama ta kasance tare da ku!”


Yohanna 20:21
Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama ta kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.”


Yohanna 20:24
Toma kuwa, (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran saʼad da Yesu ya zo.


Yohanna 20:26
Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama ta kasance tare da ku!”


Yohanna 20:29
Sai Yesu ya ce masa, “Wato, ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.”


Yohanna 20:30
Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba.


Yohanna 20:31
An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.


Yohanna 21:1
Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru:


Yohanna 21:4
Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.


Yohanna 21:7
Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa, (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan.


Yohanna 21:10
Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.”


Yohanna 21:12
Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne.


Yohanna 21:13
Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin.


Yohanna 21:14
Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.


Yohanna 21:15
Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?” Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Ciyar da ʼyaʼyan tumakina.”


Yohanna 21:16
Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”


Yohanna 21:17
Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.” Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina.


Yohanna 21:19
Yesu ya faɗi wannan ne, don yǎ nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yǎ ɗaukaka Allah. Saʼan nan ya ce masa, “Bi ni!”


Yohanna 21:20
Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu saʼad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”)


Yohanna 21:22
Yesu ya amsa, ya ce, “In na so yǎ kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.”


Yohanna 21:23
Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ʼyanʼuwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yǎ kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”


Yohanna 21:25
Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za ta sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.


Ayyukan Manzanni 1:1
A littafina na farko, Tiyofilus, na rubuta game da dukan abin da Yesu ya fara yi da abin da ya koyar


Ayyukan Manzanni 1:11
Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.”


Ayyukan Manzanni 1:14
Waɗannan duka suka duƙufa cikin adduʼa, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ʼyanʼuwansa.


Ayyukan Manzanni 1:16
ya ce, “ʼYanʼuwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu— 


Ayyukan Manzanni 1:21
Saboda haka dole a zaɓi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare da mu duk lokacin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a cikinmu,


Ayyukan Manzanni 1:22
farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa saʼad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.”


Ayyukan Manzanni 2:22
“Mutanen Israʼila, ku saurari wannan: Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin muʼujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.


Ayyukan Manzanni 2:32
Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan.


Ayyukan Manzanni 2:36
“Saboda haka bari dukan Israʼila su tabbatar da wannan: Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”


Ayyukan Manzanni 2:38
Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.


Ayyukan Manzanni 3:6
Sai Bitrus ya ce, “Azurfa ko zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. A cikin sunan Yesu Kiristi Banazare, ka yi tafiya.”


Ayyukan Manzanni 3:13
Allah na Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub, Allah na kakanninmu, ya ɗaukaka bawansa Yesu. Ku kuka ba da shi domin a kashe, kuka yi mūsun saninsa a gaban Bilatus, ko da yake ya yi niyya ya sake shi.


Ayyukan Manzanni 3:16
Ta wurin bangaskiya cikin sunan Yesu ne wannan mutum da kuke gani kuka kuma sani ya sami ƙarfi. Da sunan Yesu, da kuma bangaskiyar da take samuwa ta wurinsa ne ya ba shi cikakkiyar warkarwa, yadda dukanku kuke gani.


Ayyukan Manzanni 3:20
don kuma ya iya aika da Kiristi, wanda aka naɗa tun dā saboda ku-Yesu ke nan.


Ayyukan Manzanni 4:2
Sun damu ƙwarai da gaske domin manzannin suna koya wa mutane suna kuma shela a cikin Yesu cewa akwai tashin matattu.


Ayyukan Manzanni 4:10
to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Israʼila cewa: Da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye.


Ayyukan Manzanni 4:13
Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.


Ayyukan Manzanni 4:18
Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu.


Ayyukan Manzanni 4:27
Hakika Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Alʼummai da kuma mutanen Israʼila a wannan birni ne don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe.


Ayyukan Manzanni 4:30
Ka miƙa hannunka don ka warkar ka kuma yi ayyukan banmamaki da alamu masu banmamaki ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”


Ayyukan Manzanni 4:33
Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka.


Ayyukan Manzanni 5:30
Allahn kakanninmu ya ta da Yesu daga matattu-wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace.


Ayyukan Manzanni 5:40
Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kirawo manzannin suka sa aka yi musu bulala. Saʼan nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi.


Ayyukan Manzanni 5:42
Kowace rana, a filayen haikali da kuma gida gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.


Ayyukan Manzanni 6:14
Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja alʼadun da Musa ya ba mu.”


Ayyukan Manzanni 7:55
Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah.


Ayyukan Manzanni 7:59
Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi adduʼa ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”


Ayyukan Manzanni 8:12
Amma da suka gaskata da Filibus saʼad da yake waʼazin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata.


Ayyukan Manzanni 8:16
domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu.


Ayyukan Manzanni 8:35
Saʼan nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma fada masa labari mai daɗi game da Yesu.


Ayyukan Manzanni 9:5
Shawul ya yi tambaya, ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.”


Ayyukan Manzanni 9:17
Saʼan nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawul, sai ya ce, “Ɗanʼuwana Shawul, Ubangiji-Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan-ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”


Ayyukan Manzanni 9:20
Nan take ya fara waʼazi cikin majamiʼu cewa Yesu Ɗan Allah ne.


Ayyukan Manzanni 9:22
Duk da haka Shawul ya yi ta ƙara ƙarfi, ya kuma rikitar da Yahudawan da suke zaune a Damaskus, ta wurin tabbatar musu cewa, Yesu shi ne Kiristi.


Ayyukan Manzanni 9:27
Amma Barnabas ya ɗauke shi ya kawo shi wurin manzanni. Ya gaya musu yadda Shawul a kan hanyarsa ya ga Ubangiji kuma cewa Ubangiji ya yi magana da shi, da yadda a Damaskus ya yi waʼazi ba tsoro a cikin sunan Yesu.


Ayyukan Manzanni 9:34
Sai Bitrus ya ce masa, “Eniyas, Yesu Kiristi ya warkar da kai. Tashi ka naɗe tabarmarka.” Nan da nan Eniyas ya tashi.


Ayyukan Manzanni 10:36
Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Israʼila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa.


Ayyukan Manzanni 10:38
yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga koʼina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.


Ayyukan Manzanni 10:48
Saboda haka ya ba da umarni a yi musu baftisma cikin sunan Yesu Kiristi. Saʼan nan suka roƙi Bitrus yǎ zauna da su na ʼyan kwanaki.


Ayyukan Manzanni 11:17
To, in Allah ya ba su kyauta yadda ya ba mu, mu da muka gaskata da Ubangiji Yesu Kiristi, wane ni da zan yi hamayya da Allah?”


Ayyukan Manzanni 11:20
Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Helenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu.


Ayyukan Manzanni 13:6
Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani Bayahude mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu,


Ayyukan Manzanni 13:23
“Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Israʼila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari.


Ayyukan Manzanni 13:24
Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi waʼazin tuba da baftisma ga dukan mutanen Israʼila.


Ayyukan Manzanni 13:27
Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci.


Ayyukan Manzanni 13:33
ya cika mana, mu zuriyarsu, ta wurin ta da Yesu daga matattu. Kamar kuma yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa, “ ‘Kai Ɗana ne, yau na zama Uba a gare ka.’


Ayyukan Manzanni 13:38
“Saboda haka, ʼyanʼuwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi.


Ayyukan Manzanni 15:11
Aʼa! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”


Ayyukan Manzanni 15:26
mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi.


Ayyukan Manzanni 16:7
Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba.


Ayyukan Manzanni 16:18
Ta yi ta faɗin haka har kwanaki masu yawa. A ƙarshe Bulus ya damu ƙwarai sai ya juya ya ce wa aljanin, “A cikin sunan Yesu na umarce ka, ka rabu da ita!” Nan take aljanin ya rabu da ita.


Ayyukan Manzanni 16:31
Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto-kai da iyalinka.”


Ayyukan Manzanni 17:3
yana musu bayani da tabbatarwa cewa dole Kiristi ya sha wahala ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Wannan Yesun da nake sanar muku shi ne Kiristi.”


Ayyukan Manzanni 17:7
Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.”


Ayyukan Manzanni 17:18
Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana waʼazin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana waʼazin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu.


Ayyukan Manzanni 18:5
Saʼad da Sila da Timoti suka iso daga Makidoniya, sai Bulus ya ba da kansa ga yin waʼazi kaɗai, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Kiristi.


Ayyukan Manzanni 18:25
An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani.


Ayyukan Manzanni 18:28
Gama da ƙwazo ya ƙaryata Yahudawa a muhawwara a fili, yana tabbatar daga Nassosi cewa Yesu shi ne Kiristi.


Ayyukan Manzanni 19:4
Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya faɗa wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.”


Ayyukan Manzanni 19:5
Da ji wannan, sai aka yi musu baftisma a cikin sunan Ubangiji Yesu.


Ayyukan Manzanni 19:13
Waɗansu Yahudawa masu yawo gari gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake waʼazi, na umarce ku, ku fito.”


Ayyukan Manzanni 19:15
Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?”


Ayyukan Manzanni 19:17
Da Yahudawa da Helenawan da suke zama a Afisa suka ji wannan labari sai duk tsoro ya kama su, aka kuwa darjanta sunan Ubangiji Yesu ƙwarai.


Ayyukan Manzanni 20:21
Na yi shela ga Yahudawa da Helenawa cewa dole juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.


Ayyukan Manzanni 20:24
Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni-aikin shaida bisharar alherin Allah.


Ayyukan Manzanni 20:35
Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tukuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce: ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”


Ayyukan Manzanni 21:13
Sai Bulus ya amsa, ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a ɗaure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”


Ayyukan Manzanni 22:8
“Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ya amsa ya ce, ‘Ni ne Yesu Banazare, wanda kake tsanantawa.’


Ayyukan Manzanni 24:24
Bayan ʼyan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, Bayahudiya. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu.


Ayyukan Manzanni 25:19
A maimako haka, sai suka kawo waɗansu ʼyan maganganu game da addininsu da ba su yarda da shi ba da kuma game da wani Yesu da ya mutu wanda Bulus ya ce yana da rai.


Ayyukan Manzanni 26:9
“Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare.


Ayyukan Manzanni 26:15
“Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.’


Ayyukan Manzanni 28:23
Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yi musu bayyani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa.


Ayyukan Manzanni 28:31
Gabagaɗi ba tare da wani hani ba, ya yi waʼazin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi.


Romawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, bawan Kiristi Yesu, kirayaye yǎ zama manzo keɓaɓɓe kuma domin bisharar Allah— 


Romawa 1:4
wanda bisa ga Ruhun tsarki, aka shaida shi da iko cewa shi Ɗan Allah ta wurin tashinsa daga matattu. Wannan bishara kuwa game da Yesu Kiristi Ubangijinmu ne.


Romawa 1:6
Ku ma kuna cikin waɗanda aka kira ku zama na Yesu Kiristi.


Romawa 1:7
Wannan wasiƙa ce zuwa ga dukanku da kuke a Roma waɗanda Allah yake ƙauna, waɗanda kuma ya kira domin su zama tsarkaka: Alheri da salama gare ku daga Allah Ubanmu da kuma daga Ubangiji Yesu Kiristi.


Romawa 1:8
Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a koʼina a duniya.


Romawa 2:16
Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shariʼanta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.


Romawa 3:22
Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci,


Romawa 3:24
an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi.


Romawa 3:25
Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yǎ nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba— 


Romawa 3:26
ya yi haka domin yǎ nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yǎ zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.


Romawa 4:24
amma saboda mu ma, mu da Allah zai lissafta adalci-mu da muka ba da gaskiya gare shi da ya tashe Yesu Ubangijinmu daga matattu.


Romawa 5:1
Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi,


Romawa 5:11
Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu.


Romawa 5:15
Amma kyautan nan dabam take da laifin nan. Gama in mutane da yawa sun mutu saboda laifin mutum ɗayan nan, to, ai, alherin Allah da kuma kyautan nan mai zuwa ta wurin alherin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi, ya shafi mutane da yawa!


Romawa 5:17
Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi.


Romawa 5:21
domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yǎ yi mulki ta wurin adalci yǎ kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu.


Romawa 6:3
Ko ba ku sani ba cewa dukanmu da aka yi wa baftisma a cikin Kiristi Yesu an yi mana baftismar ne zuwa cikin mutuwarsa?


Romawa 6:11
Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu.


Romawa 6:23
Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.


Romawa 7:25
Godiya ga Allah-ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu! Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.


Romawa 8:1
Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu,


Romawa 8:2
gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ʼyantar da ni daga Dokar Musa.


Romawa 8:11
In kuwa Ruhu wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya ta da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.


Romawa 8:34
Wa zai yi hukunci? Yesu Kiristi ne, wanda ya mutu-fiye da haka ma, shi da aka ta da zuwa rai-yana zaune a hannun dama na Allah yana kuma yin roƙo a madadinmu.


Romawa 8:39
ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.


Romawa 10:9
Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya ta da shi daga matattu, za ka sami ceto.


Romawa 13:14
A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da shaʼawace-shaʼawacen mutuntaka.


Romawa 14:14
A matsayina na mai bin Ubangiji Yesu na tabbata ƙwarai cewa babu abincin da yake marar tsabta don kansa. Amma in wani ya ɗauka wani abu marar tsabta ne, to, a gare shi marar tsabta ne.


Romawa 15:5
Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yǎ ba ku ruhun haɗin kai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu,


Romawa 15:6
don da zuciya ɗaya da kuma baki ɗaya kuke ɗaukaka Allah da kuma Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi.


Romawa 15:16
in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Alʼummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Alʼummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


Romawa 15:17
Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah.


Romawa 15:30
Ina roƙonku ʼyanʼuwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin adduʼa ga Allah saboda ni.


Romawa 16:3
Ku gai da Firiskila da Akwila, abokan aikina cikin Kiristi Yesu.


Romawa 16:20
Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yǎ kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yǎ kasance tare da ku.


Romawa 16:25
Ɗaukaka ta tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga waʼazin Yesu Kiristi, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun filʼazal,


Romawa 16:27
ɗaukaka ta tabbata har abada ga Allah, wanda shi ne kaɗai mai hikima ta wurin Yesu Kiristi! Amin.


1 Korintiyawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, wanda aka kira domin yǎ zama manzon Kiristi Yesu, bisa ga nufin Allah, da kuma ɗanʼuwanmu Sostenes,


1 Korintiyawa 1:2
Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korinti, da waɗanda aka tsarkake cikin Kiristi Yesu, aka kuma kira domin su zama masu tsarki, tare da dukan waɗanda suke koʼina da suke kiran sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, Ubangijinsu da kuma namu:


1 Korintiyawa 1:3
Alheri da salama zuwa gare ku daga Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Kiristi.


1 Korintiyawa 1:4
Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu.


1 Korintiyawa 1:7
Saboda haka, ba ku rasa kowace baiwa ta ruhaniya ba, yayinda kuke jira da marmari, saboda bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi.


1 Korintiyawa 1:8
Zai ƙarfafa ku har zuwa ƙarshe, domin ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Kiristi.


1 Korintiyawa 1:9
Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.


1 Korintiyawa 1:10
Ina roƙonku ʼyanʼuwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku.


1 Korintiyawa 1:30
Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu.


1 Korintiyawa 2:2
Don na ƙudura a raina saʼad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye.


1 Korintiyawa 3:11
Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi.


1 Korintiyawa 4:15
Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara.


1 Korintiyawa 4:17
Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a koʼina, a kowace ikkilisiya.


1 Korintiyawa 5:4
Saboda haka saʼad da kun taru ikon Ubangijinmu Yesu kuma yana nan, ni ma ina tare da ku.


1 Korintiyawa 6:11
Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.


1 Korintiyawa 8:6
duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.


1 Korintiyawa 9:1
Ba ni da ʼyanci ne? Ni ba manzo ba ne? Ni ban gan Yesu Ubangijinmu ba ne? Ba ku ne sakamakon aikina cikin Ubangiji ba?


1 Korintiyawa 11:23
Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi,


1 Korintiyawa 12:3
Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu laʼananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi.


1 Korintiyawa 15:31
Gaskiya, ʼyanʼuwa, ina fuskantar mutuwa kowace rana. Taƙamar da nake da ita a kanku saboda Kiristi Yesu Ubangijinmu ne ya sa na faɗa haka.


1 Korintiyawa 15:57
Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.


1 Korintiyawa 16:23
Alherin Ubangiji Yesu yǎ kasance tare da ku.


1 Korintiyawa 16:24
Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin.


2 Korintiyawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti, ɗanʼuwanmu, Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korinti, tare da dukan tsarkaka a koʼina a Akayya:


2 Korintiyawa 1:2
Alheri da salama gare ku, daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


2 Korintiyawa 1:3
Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan taʼaziyya,


2 Korintiyawa 1:14
kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.


2 Korintiyawa 1:19
Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku waʼazinsa, ai, ba “I” da “Aʼa” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.


2 Korintiyawa 4:5
Gama ba waʼazin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.


2 Korintiyawa 4:10
Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yǎ bayyana a jikinmu.


2 Korintiyawa 4:11
Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.


2 Korintiyawa 4:14
Domin mun san cewa shi da ya ta da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yǎ kuma miƙa mu a gabansa tare da ku.


2 Korintiyawa 8:9
Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.


2 Korintiyawa 11:4
Gama in wani ya zo wurinku yana waʼazin wani Yesu dabam da wanda muka yi waʼazinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai.


2 Korintiyawa 11:31
Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba.


2 Korintiyawa 12:9
Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yǎ zauna tare da ni.


2 Korintiyawa 13:5
Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin.


2 Korintiyawa 13:14
Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.


Galatiyawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus manzo-aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da Allah Uba, wanda ya ta da shi daga matattu— 


Galatiyawa 1:3
Alheri da salama zuwa gare ku daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi,


Galatiyawa 1:12
Ban karɓe ta daga wurin wani mutum ba, ba a kuma koya mini ita ba ne, a maimako, na karɓe ta, ta wurin wahayi daga Yesu Kiristi ne.


Galatiyawa 2:4
Wannan zance ya taso domin waɗansu ʼyanʼuwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ʼyancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi.


Galatiyawa 2:16
mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka.


Galatiyawa 3:1
Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ruɗe ku? A idanunku aka bayyana Yesu Kiristi gicciyeyye a sarari.


Galatiyawa 3:14
Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yǎ zo ga Alʼummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.


Galatiyawa 3:22
Amma Nassi ya furta cewa dukan duniya ɗan kurkukun zunubi ne, don abin da aka yi alkawari, da ake bayarwa ta wurin bangaskiya cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata.


Galatiyawa 3:26
Dukanku ʼyaʼyan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu,


Galatiyawa 3:28
Babu bambanci tsakanin Bayahude da Bahelene, bawa da ʼyantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu.


Galatiyawa 4:14
Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce malaʼikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.


Galatiyawa 5:6
Gama a cikin Kiristi Yesu kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.


Galatiyawa 5:24
Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma shaʼawace-shaʼawacensa.


Galatiyawa 6:14
Kada in taɓa yin taƙama ga kome sai dai a cikin gicciyen Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa aka gicciye duniya a gare ni, aka kuma gicciye ni ga duniya.


Galatiyawa 6:17
A ƙarshe, kada kowa yǎ ƙara damuna, gama ina ɗauke tabbai masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu.


Galatiyawa 6:18
Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yǎ kasance tare da ruhunku, ʼyanʼuwa. Amin.


Afisawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yǎ zama manzon Kiristi Yesu. Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da suke amintattu cikin Kiristi Yesu:


Afisawa 1:2
Bari alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi su kasance tare da ku.


Afisawa 1:3
Yabo ya tabbata ga Allah da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama.


Afisawa 1:5
A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu mu zama ʼyaʼyansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu. Wannan kuwa ya sa ya ji daɗi.


Afisawa 1:15
Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka,


Afisawa 1:17
Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai ɗaukaka, yǎ ba ku Ruhunsa. Ruhun kuwa zai ba ku hikima yǎ kuma sa ku gane abin da ake nufi da sanin Allah.


Afisawa 2:7
Allah ya yi haka domin a zamanai masu zuwa yǎ yi amfani da mu a matsayin yalwar alherinsa da ya wuce misali, yadda yake a dukan abin da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu.


Afisawa 2:13
Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.


Afisawa 3:1
Ni Bulus, ɗan kurkuku na Kiristi Yesu saboda ku Alʼummai.


Afisawa 3:6
Asirin nan kuwa shi ne cewa ta wurin bishara, Alʼummai sun zama waɗanda za su yi gādo tare da Israʼila, gaɓoɓin jiki ɗaya, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Kiristi Yesu.


Afisawa 3:11
Wannan shi ne madawwamin shirinsa, kuma an aikata shi ta wurin Kiristi Yesu Ubangijinmu.


Afisawa 3:21
Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har yǎ zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin.


Afisawa 4:21
Da yake kun ji duka game da shi kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu,


Afisawa 5:20
Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi kuna gode wa Allah Uba a ko mene ne.


Afisawa 6:23
Salama zuwa ga ʼyanʼuwa, da kuma ƙauna tare da bangaskiya daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


Afisawa 6:24
Alheri yǎ tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangiji Yesu Kiristi da ƙauna marar ƙarewa.


Filibbiyawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus da Timoti, bayin Kiristi Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu a Filibbi, tare da masu kula da Ikkilisiya da kuma masu hidima:


Filibbiyawa 1:2
Alheri da salama gare ku daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


Filibbiyawa 1:6
da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yǎ zuwa ranar Kiristi Yesu.


Filibbiyawa 1:8
Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu.


Filibbiyawa 1:11
cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi-zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa.


Filibbiyawa 1:19
gama na san cewa ta wurin adduʼoʼinku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata.


Filibbiyawa 1:26
domin ta wurin kasancewata tare da ku, farin cikinku cikin Kiristi Yesu zai cika sosai ta dalilina.


Filibbiyawa 2:5
Ya kamata haleyanku su zama kamar na Kiristi Yesu:


Filibbiyawa 2:10
don a sunan Yesu kowace gwiwa za ta durƙusa, a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,


Filibbiyawa 2:11
kowane harshe kuma yǎ furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.


Filibbiyawa 2:19
Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi saʼad da na ji labarinku.


Filibbiyawa 2:21
Gama kowa yana lura da alʼamuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba.


Filibbiyawa 3:3
Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,


Filibbiyawa 3:8
Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi


Filibbiyawa 3:12
Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi.


Filibbiyawa 3:14
ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.


Filibbiyawa 3:20
Amma mu ʼyan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi,


Filibbiyawa 4:7
Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.


Filibbiyawa 4:19
Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.


Filibbiyawa 4:21
Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu. ʼYanʼuwan da suke tare da ni suna gaishe ku.


Filibbiyawa 4:23
Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yǎ kasance da ruhunku. Amin.


Kolossiyawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yǎ zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗanʼuwanmu.


Kolossiyawa 1:3
Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, saʼad da muke adduʼa dominku.


Kolossiyawa 1:4
Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka.


Kolossiyawa 2:6
To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa,


Kolossiyawa 3:17
Kuma komene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.


Kolossiyawa 4:11
Yesu (wannan da muke kira Yustus) shi ma yana gaisuwa. Waɗannan ne kaɗai Yahudawa masu bi a cikin abokan aikina saboda mulkin Allah. Sun kuma zama da taimako a gare ni.


Kolossiyawa 4:12
Efafaras naku, mai hidimar Kiristi Yesu, yana gaisuwa. Kullum yana adduʼa dominku sosai, don ku san cikakken abin da Allah yake so ku yi don kuma ku yi shi cikakke.


1 Tessalonikawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, Sila da Timoti, zuwa ga ikkilisiyar Tassalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi: Alheri da salama zuwa gare ku.


1 Tessalonikawa 1:3
Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.


1 Tessalonikawa 1:10
ku kuma jira dawowar Ɗansa daga sama, wanda ya tasa daga matattu-Yesu, wanda ya cece mu daga fushi mai zuwa.


1 Tessalonikawa 2:14
Gama ku, ʼyanʼuwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu: Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,


1 Tessalonikawa 2:15
waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane


1 Tessalonikawa 2:19
Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu saʼad da ya dawo? Ba ku ba ne?


1 Tessalonikawa 3:11
Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yǎ shirya mana hanya mu zo wurinku.


1 Tessalonikawa 3:13
Bari yǎ ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu saʼad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa.


1 Tessalonikawa 4:1
A ƙarshe, ʼyanʼuwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau.


1 Tessalonikawa 4:2
Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin ikon Ubangiji Yesu.


1 Tessalonikawa 4:14
Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu.


1 Tessalonikawa 5:9
Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.


1 Tessalonikawa 5:18
ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.


1 Tessalonikawa 5:23
Bari Allah da kansa, Allah na salama, yǎ tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.


1 Tessalonikawa 5:28
Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yǎ kasance tare da ku.


2 Tessalonikawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga ikkilisiya ta Tassalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi:


2 Tessalonikawa 1:2
Alheri da salama zuwa gare ku daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


2 Tessalonikawa 1:7
yǎ kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru saʼad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da malaʼikunsa masu iko.


2 Tessalonikawa 1:8
Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba.


2 Tessalonikawa 1:12
Muna wannan adduʼa don sunan Ubangijinmu Yesu yǎ sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi.


2 Tessalonikawa 2:1
Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku, ʼyanʼuwa,


2 Tessalonikawa 2:8
Saʼan nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yǎ kuma hallaka shi da darajar dawowarsa.


2 Tessalonikawa 2:14
Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi.


2 Tessalonikawa 2:16
Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yǎ ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege,


2 Tessalonikawa 3:6
A cikin sunan Ubangiji Yesu, muna muku umarni, ʼyanʼuwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗanʼuwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu.


2 Tessalonikawa 3:12
Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.


2 Tessalonikawa 3:18
Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yǎ kasance tare da ku duka.


1 Timoti 1:1
Wasiƙa daga Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu,


1 Timoti 1:2
zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya: Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu.


1 Timoti 1:12
Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa.


1 Timoti 1:14
An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.


1 Timoti 1:15
Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa: Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi-wanda nake mafi muni a cikinsu.


1 Timoti 1:16
Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yǎ iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami.


1 Timoti 2:5
Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu,


1 Timoti 3:13
Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu.


1 Timoti 4:6
In ka nuna wa ʼyanʼuwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi.


1 Timoti 5:21
Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun malaʼiku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci.


1 Timoti 6:3
In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba,


1 Timoti 6:13
Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida,


1 Timoti 6:14
ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yǎ bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi,


2 Timoti 1:1
Wasiƙa daga Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai wanda yake cikin Kiristi Yesu,


2 Timoti 1:2
zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana: Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu.


2 Timoti 1:9
wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki-ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun filʼazal,


2 Timoti 1:10
amma yanzu an bayyanata ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara.


2 Timoti 1:13
Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu.


2 Timoti 2:1
Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu.


2 Timoti 2:3
Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu.


2 Timoti 2:8
Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka ta da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata,


2 Timoti 2:10
Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.


2 Timoti 3:12
Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani.


2 Timoti 3:15
da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.


2 Timoti 4:1
A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shariʼa, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni:


Titus 1:1
Wasiƙa daga Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah— 


Titus 1:4
Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya: Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu.


Titus 2:13
yayinda muke sauraron begenmu mai albarka-bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi,


Titus 3:6
wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu,


Filemon 1:1
Wasiƙa daga Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗanʼuwanmu, zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,


Filemon 1:3
Alheri gare ku da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


Filemon 1:5
domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka.


Filemon 1:9
duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu.


Filemon 1:23
Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka.


Filemon 1:25
Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yǎ kasance da ruhunku.


Ibraniyawa 2:9
Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar malaʼiku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yǎ sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yǎ ɗanɗana mutuwa saboda kowa.


Ibraniyawa 2:11
Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ʼyan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ʼyanʼuwansa.


Ibraniyawa 3:1
Saboda haka, ʼyanʼuwa tsarkaka, waɗanda suke da rabo a kiran nan na sama, ku kafa tunaninku a kan Yesu, manzo da kuma babban firist wanda muke shaidawa.


Ibraniyawa 3:3
An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja.


Ibraniyawa 4:14
Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi.


Ibraniyawa 5:7
A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi adduʼoʼi da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi.


Ibraniyawa 6:20
inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.


Ibraniyawa 7:22
Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau.


Ibraniyawa 7:24
amma Yesu ba zai mutu ba, don haka zai zama firist har abada.


Ibraniyawa 8:6
Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakaici ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawarai mafi kyau.


Ibraniyawa 10:10
Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak.


Ibraniyawa 10:19
Saboda haka, ʼyanʼuwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu,


Ibraniyawa 12:2
Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah.


Ibraniyawa 12:24
Kun zo ga Yesu, mai yin sulhu na sabon alkawari, da kuma ga jinin da aka yayyafa wanda yake magana mafi kyau fiye da jinin Habila.


Ibraniyawa 13:8
Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada.


Ibraniyawa 13:12
Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yǎ tsarkake mutane ta wurin jininsa.


Ibraniyawa 13:15
Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah-yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.


Ibraniyawa 13:20
Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya ta da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma,


Ibraniyawa 13:21
yǎ kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yǎ aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin.


Yaƙub 1:1
Wasiƙa daga Yaƙub, bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Kiristi, Zuwa ga kabilan nan goma sha biyu, da suke warwartse a cikin alʼummai: Gaisuwa.


Yaƙub 2:1
ʼYanʼuwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci.