A A A A A


Bincika

Mattiyu 2:2
suka tambaya, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”


Mattiyu 2:8
Sai ya aike su Betlehem, ya ce, “Ku je ku bincika a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.”


Mattiyu 2:11
Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Saʼan nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.


Mattiyu 4:9
Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in ka durƙusa ka yi mini sujada.”


Mattiyu 4:10
Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake: ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’ ”


Mattiyu 14:33
Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”


Mattiyu 15:9
A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”


Mattiyu 28:9
Kwaram, sai ga Yesu ya gamu da su, ya ce, “Gaisuwa.” Sai suka zo kusa da shi, suka rungumi ƙafafunsa, suka yi masa sujada.


Mattiyu 28:17
Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka.


Markus 7:7
A banza suke mini sujada, koyarwarsu dokokin mutane ne kawai.’


Luka 1:10
Da lokacin ƙone turare ya yi, duk taron masu sujada suna a waje suna adduʼa.


Luka 2:37
ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da adduʼa.


Luka 4:7
Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”


Luka 4:8
Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”


Luka 24:52
Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai.


Yohanna 4:20
Kakanninmu sun yi sujada a kan dutsen nan, amma ku Yahudawa ɗauka cewa inda ya kamata mu yi sujada shi ne Urushalima.”


Yohanna 4:21
Sai Yesu ya ce, “Ina tabbatar miki, mace, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a kan dutsen nan ko kuma a Urushalima ba.


Yohanna 4:22
Ku Samariyawa kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada; mu kuwa muna yi wa abin da muka sani ne sujada, gama ceto daga Yahudawa yake.


Yohanna 4:23
Duk da haka lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada cikin Ruhu da kuma gaskiya, domin irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.


Yohanna 4:24
Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada cikin ruhu da kuma cikin gaskiya.”


Yohanna 9:38
Sai mutumin ya ce, “Ubangiji, na gaskata,” ya kuma yi masa sujada.


Yohanna 12:20
To, akwai waɗansu Helenawa a cikin waɗanda suka haura don su yi sujada a Bikin.


Ayyukan Manzanni 7:7
Amma zan hore ƙasar da suka bauta wa.’ Allah ya ce, ‘kuma daga baya za su fita daga wannan ƙasa su kuma yi mini sujada a wannan wuri.’


Ayyukan Manzanni 7:43
Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek, da tauraron allahnku Refan, gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada. Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’ gaba da Babilon.


Ayyukan Manzanni 8:27
Saboda haka ya kama hanya, a kan hanyarsa kuwa sai ya sadu da wani mutumin Itiyofiya, wanda yake bābā, hafsa mai muhimmanci wanda yake lura da dukan maʼajin Kandas, sarauniyar mutanen Itiyofiya. Mutumin nan ya tafi Urushalima ne domin yin sujada,


Ayyukan Manzanni 13:2
Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawul domin aikin da na kira su.”


Ayyukan Manzanni 13:16
Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce: “Mutanen Israʼila da kuma ku Alʼummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni!


Ayyukan Manzanni 16:14
Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yardunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus.


Ayyukan Manzanni 17:23
Gama saʼad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu: ‘GA ALLAHN DA BA A SANI BA.’ To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku.


Ayyukan Manzanni 18:7
Sai Bulus ya bar majamiʼar ya kuma tafi ƙofar da take kusa da gidan Titiyus Yustus, mai yi wa Allah sujada.


Ayyukan Manzanni 18:13
Suka yi zarge cewa, “Wannan mutum yana rarrashin mutane su yi wa Allah sujada a hanyoyin da suka saɓa wa doka.”


Ayyukan Manzanni 24:11
Da sauƙi za ka iya tabbatar cewa, bai fi kwana goma sha biyu da suka wuce ne na tafi Urushalima, domin yin sujada ba.


Romawa 1:25
Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci-wanda ake yabo har abada. Amin.


Romawa 9:4
mutanen Israʼila. Su ne Allah ya mai da su ʼyaʼyansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawarai.


Romawa 11:4
Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Baʼal sujada ba.”


1 Korintiyawa 14:16
A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, saʼad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba?


1 Korintiyawa 14:25
asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yǎ yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!”


फिलिप्पी ३:३
Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,


2 Tessalonikawa 2:4
Zai yi gāba yǎ kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yǎ kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.


Ibraniyawa 1:6
Haka kuma, saʼad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya, ya ce, “Bari dukan malaʼikun Allah su yi masa sujada.”


Ibraniyawa 9:1
Alkawari na farko fa ya kunshi ƙaʼidodi domin sujada da kuma domin wuri mai tsarki a nan duniya.


Ibraniyawa 10:1
Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa-wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za ta taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara shekara ba.


Ibraniyawa 10:2
Da a ce za ta iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtace masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba.


Ibraniyawa 11:21
Ta wurin bangaskiya ne Yaƙub, saʼad da yake bakin mutuwa, ya albarkaci kowane ɗan Yusuf, ya kuma yi sujada yayinda yake jingine a kan sandansa.


Ibraniyawa 12:28
Saboda haka, da yake muna karɓar mulkin da ba ya jijjiguwa, sai mu yi godiya, ta haka kuwa mu yi wa Allah sujada yadda ya kamata, tare da bangirma da kuma tsoro,


Ruʼuya ta Yohanna 4:10
sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,


Ruʼuya ta Yohanna 5:14
Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.


Ruʼuya ta Yohanna 7:11
Dukan malaʼiku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada,


Ruʼuya ta Yohanna 11:1
Aka ba ni ƙara kamar sandan awo aka kuma ce mini, “Tafi ka auna haikalin Allah da bagaden, ka kuma ƙirga waɗanda suke sujada a can.


Ruʼuya ta Yohanna 11:16
Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada,


Ruʼuya ta Yohanna 13:4
Mutane suka yi wa macijin sujada domin ya ba wa dabbar ikonsa, suka yi wa dabbar sujada, suka kuma yi tambaya cewa, “Wane ne yake kama da dabban nan? Wa zai iya yaƙe ta?”


Ruʼuya ta Yohanna 13:8
Dukan mazaunan duniya za su yi wa dabbar sujada-dukan waɗanda ba a rubuta sunayensu a cikin littafin ran da yake na Ɗan Ragon da aka yanka tun kafin halittar duniya ba.


Ruʼuya ta Yohanna 13:12
Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta.


Ruʼuya ta Yohanna 13:15
Aka ba ta iko ta ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don ta yi magana ta kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada.


Ruʼuya ta Yohanna 14:7
Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin saʼar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”


Ruʼuya ta Yohanna 14:9
Malaʼika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu,


Ruʼuya ta Yohanna 14:11
Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.”


Ruʼuya ta Yohanna 15:4
Wane ne ba zai ji tsoronka, yǎ kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, Ya Ubangiji? Gama kai kaɗai ne mai tsarki. Dukan alʼummai za su zo su yi sujada a gabanka, gama an bayyana ayyukan adalcinka.”


Ruʼuya ta Yohanna 16:2
Malaʼika na fari ya je ya juye kwanonsa a bisan ƙasa, sai munanan gyambuna masu zafi suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar suka kuma yi wa siffarta sujada.


Ruʼuya ta Yohanna 19:4
Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka ta da murya suka ce: “Amin, Halleluya!”


Ruʼuya ta Yohanna 19:10
Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ʼyanʼuwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”


Ruʼuya ta Yohanna 20:4
Na ga kursiyai inda waɗanda aka ba su ikon shariʼa suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.


Ruʼuya ta Yohanna 22:8
Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma saʼad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban malaʼikan da yake nuna mini su, don in yi sujada.


Ruʼuya ta Yohanna 22:9
Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ʼyanʼuwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!”


Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc