A A A A A


Bincika

Mattiyu 6:30
In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, Ya ku masu ƙarancin bangaskiya?


Mattiyu 8:10
Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Israʼila da bangaskiya mai girma haka ba.


Mattiyu 8:13
Saʼan nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.


Mattiyu 8:26
Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Saʼan nan ya tashi ya tsauta wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.


Mattiyu 9:2
Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu ɗana, an gafarta maka zunubanka.”


Mattiyu 9:22
Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, “Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke,” Nan take macen ta warke.


Mattiyu 9:29
Saʼan nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”;


Mattiyu 13:58
Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.


Mattiyu 14:31
Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”


Mattiyu 15:28
Saʼan nan Yesu ya amsa, ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ʼYarta kuwa ta warke nan take.


Mattiyu 16:8
Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba?


Mattiyu 17:17
Yesu ya amsa, ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurin kai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”


Mattiyu 17:20
Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”


Mattiyu 21:21
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku’, sai yǎ faru.


Mattiyu 24:10
A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,


Markus 2:5
Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, an gafarta zunubanka.”


Markus 4:40
Sai ya ce wa almajiransa, “Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?”


Markus 5:34
Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki tafi cikin salama, kin kuma rabu da dukan wahalarki.”


Markus 6:6
Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu. Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.


Markus 9:19
Yesu ya ce, “Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.”


Markus 9:24
Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!”


Markus 10:52
Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.


Markus 16:14
Bayan haka, Yesu ya bayyana ga Sha Ɗayan, yayinda suke cin abinci. Ya tsauta musu a kan rashin bangaskiyarsu, da yadda suka ƙi gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi.


Luka 5:20
Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Aboki, an gafarta maka zunubanka.”


Lucas 7:9
Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake binsa, “Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Israʼila ba.”


Lucas 7:23
Mai albarka ne mutumin da bai yi shakkar bangaskiyar da yake da ita a kaina ba.”


Lucas 7:50
Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki tafi da salama.”


Lucas 8:25
Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?” A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?”


Lucas 8:48
Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki tafi cikin salama.”


Lucas 9:41
Yesu ya amsa, ya ce, “Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan.”


Lucas 12:28
In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, saʼan nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!


Lucas 12:46
Maigidan bawan nan zai dawo a ranar da wannan bawan bai yi tsammaninsa ba, kuma a saʼar da bai sani ba. Maigidan zai yayyanka shi, ya kuma ba shi rabonsa tare da marasa bangaskiya.


Lucas 17:5
Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!”


Lucas 17:6
Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.


Lucas 17:19
Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai. ”


Lucas 18:8
Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma saʼad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?”


Lucas 18:42
Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”


Lucas 22:32
Amma na yi maka adduʼa, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ʼyanʼuwanka.”


Ayyukan Manzanni 3:16
Ta wurin bangaskiya cikin sunan Yesu ne wannan mutum da kuke gani kuka kuma sani ya sami ƙarfi. Da sunan Yesu, da kuma bangaskiyar da take samuwa ta wurinsa ne ya ba shi cikakkiyar warkarwa, yadda dukanku kuke gani.


Ayyukan Manzanni 6:5
Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci.


Ayyukan Manzanni 6:7
Saboda haka maganar Allah ta yaɗu. Yawan almajirai a Urushalima kuwa ya yi saurin ƙaruwa, firistoci masu yawa kuma suka zama masu biyayya ga wannan bangaskiya.


Ayyukan Manzanni 11:24
Mutum ne nagari, cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, mutane masu yawan gaske kuwa suka juya ga Ubangiji.


Ayyukan Manzanni 13:8
Amma Elimas mai sihirin nan, (domin maʼanar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya.


Ayyukan Manzanni 14:9
Ya kasa kunne yayinda Bulus yake magana. Bulus kuma ya kafa masa ido, ya lura cewa yana da bangaskiyar da za ta warkar da shi


Ayyukan Manzanni 14:22
suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”


Ayyukan Manzanni 14:27
Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Alʼummai.


Ayyukan Manzanni 15:9
Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya.


Ayyukan Manzanni 16:5
Saboda haka ikkilisiyoyi suka ginu cikin bangaskiya suka kuma yi girma suka yi ta ƙaruwa kowace rana.


Ayyukan Manzanni 24:24
Bayan ʼyan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, Bayahudiya. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu.


Ayyukan Manzanni 26:18
ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’


Romawa 1:5
Ta wurinsa da kuma saboda sunansa, muka sami alheri muka kuma zama manzanni don mu kira mutane daga cikin dukan Alʼummai zuwa ga biyayyar da take zuwa daga bangaskiya.


Romawa 1:8
Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a koʼina a duniya.


Romawa 1:12
wato, don ni da ku mu ƙarfafa juna ta wurin bangaskiyarmu.


Romawa 1:17
Gama a cikin bishara an bayyana adalci daga Allah wanda yake ta wurin bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”


Romawa 1:31
su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi.


Romawa 3:3
Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah?


Romawa 3:22
Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci,


Romawa 3:25
Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yǎ nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba— 


Romawa 3:27
To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙaʼida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? Aʼa, sai dai ta wurin bangaskiya.


Romawa 3:28
Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba.


Romawa 3:30
da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin.


Romawa 3:31
To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi.


Romawa 4:5
Amma fa, game da mutumin da ba ya aiki sai dai dogara ga Allah wanda yake kuɓutar da masu mugunta, akan lissafta bangaskiyarsa a matsayin adalci ne.


Romawa 4:9
Shin, wannan albarkar a kan masu kaciya ne kawai, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Mun sha faɗi cewa an lissafta bangaskiyar Ibrahim adalci ne a gare shi.


Romawa 4:11
Ya kuma karɓi alamar kaciya, hatimin adalcin da yake da shi ta wurin bangaskiya tun yana marar kaciya. Saboda haka fa, ya zama mahaifin dukan waɗanda suka gaskata domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba.


Romawa 4:12
Ya kuma zama mahaifin masu kaciya waɗanda ba kaciya kaɗai suke da ita ba amma har ma suna bin gurbin bangaskiyar da mahaifinmu Ibrahim yake da ita kafin aka yi masa kaciya.


Romawa 4:13
Ba ta wurin doka ce Ibrahim da zuriyarsa suka sami alkawarin cewa zai zama magājin duniya ba, amma sai dai ta wurin adalcin da yake zuwa ta wurin bangaskiya.


Romawa 4:14
Gama da a ce masu kiyaye doka ne magāda, ai, da bangaskiya ba ta da amfani, alkawarin kuma ya zama banza,


Romawa 4:16
Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yǎ zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim-ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka.


Romawa 4:19
Ba tare da ya bar bangaskiyarsa ta yi rauni ba, ya fuskanci gaskiyan nan mai cewa jikinsa mai tsufa matacce ne-da yake yana da shekara wajen ɗari-mahaifar Saratu kuma matacciya ce.


Romawa 4:20
Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah,


Romawa 5:1
Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi,


Romawa 5:2
ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah.


Romawa 9:30
Me za mu ce ke nan? Ai, Alʼummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya;


Romawa 9:32
Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen bin ta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.”


Romawa 10:4
Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya.


Romawa 10:6
Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa: “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’ ” (wato, don yǎ sauko da Kiristi),


Romawa 10:8
Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela:


Romawa 10:17
Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.


Romawa 11:20
Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro.


Romawa 11:23
In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su.


Romawa 12:3
Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku: Kada yǎ ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yǎ auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.


Romawa 12:6
Muna da baye-baye dabam dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yǎ yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa.


Romawa 14:1
Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba ta yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba.


Romawa 14:2
Bangaskiyar mutum ta yarda masa yǎ ci kome, amma wanda bangaskiyarsa ba ta yi ƙarfi ba, yakan ci kayan lambu ne kawai.


Romawa 14:23
Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne.


1 Korintiyawa 2:5
domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.


1 Korintiyawa 12:9
Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda.


1 Korintiyawa 13:2
In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne.


1 Korintiyawa 13:13
Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata: bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.


1 Korintiyawa 15:14
In ba a tashe Kiristi ba kuwa, ai, waʼazinmu, da bangaskiyarku banza ne.


1 Korintiyawa 15:17
In kuwa ba a tashe Kiristi ba, bangaskiyarku a banza take, ya zama har yanzu kuna cikin zunubanku ke nan.


1 Korintiyawa 16:13
Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.


2 Korintiyawa 1:24
Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi.


2 Korintiyawa 4:13
A rubuce yake cewa: “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana.


2 Korintiyawa 5:7
Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba.


2 Korintiyawa 8:7
To, da yake kun fiffita a kowane abu-cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin dukan ƙwazo, da kuma cikin ƙaunarku dominmu-sai ku fiffita a wannan aikin alheri ma.


2 Korintiyawa 9:13
Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi naʼam da bisharar Kiristi, saboda kuma gudunmawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.


2 Korintiyawa 10:15
Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba ta kuma shafi aikin waɗansu ba. Sai dai muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku yǎ riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske.


2 Korintiyawa 13:5
Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin.


Galatiyawa 1:23
Sun dai sami labari ne kawai cewa: “Mutumin da dā yake tsananta mana yanzu yana waʼazin bangaskiyar da dā ya yi ƙoƙari yǎ hallaka.”


Galatiyawa 2:16
mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka.


Galatiyawa 2:20
An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne kuma nake raye ba, sai dai Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.


Galatiyawa 3:8
Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Alʼummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yǎ yi cewa, “Dukan alʼummai za su sami albarka ta wurinka.”


Galatiyawa 3:9
Saboda haka waɗanda suke da bangaskiya sun sami albarka tare da Ibrahim, mutumin bangaskiya.


Galatiyawa 3:11
A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”


Galatiyawa 3:12
Doka ba ta dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”


Galatiyawa 3:14
Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yǎ zo ga Alʼummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.


Galatiyawa 3:22
Amma Nassi ya furta cewa dukan duniya ɗan kurkukun zunubi ne, don abin da aka yi alkawari, da ake bayarwa ta wurin bangaskiya cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata.


Galatiyawa 3:23
Kafin bangaskiyan nan ta zo, muna a ɗaure kamar ʼyan kurkuku ta wurin Doka, a kulle sai a lokacin da bangaskiya ta bayyana.


Galatiyawa 3:24
Ta haka aka sa Dokar ta zama jagorarmu zuwa ga Kiristi don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya.


Galatiyawa 3:25
Yanzu da bangaskiya ta zo, ba mu ƙarƙashin Doka.


Galatiyawa 3:26
Dukanku ʼyaʼyan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu,


Galatiyawa 5:5
Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu.


Galatiyawa 5:6
Gama a cikin Kiristi Yesu kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.


Afisawa 1:13
Kiristi ya kawo muku gaskiya, wadda take labari mai daɗi game da yadda za ku sami ceto. Kun sa bangaskiyarku a cikin Kiristi aka kuwa yi muku alkawarin Ruhu Mai Tsarki don a nuna ku na Allah ne.


Afisawa 1:15
Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka,


Afisawa 3:12
A cikinsa da kuma ta wurin bangaskiya ne muke da ƙarfin halin zuwa kusa da Allah gabagaɗi.


Afisawa 3:17
Ina adduʼa domin Kiristi yǎ zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma adduʼa saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna,


Afisawa 4:5
Muna da Ubangiji ɗaya, bangaskiya ɗaya, baftisma kuma ɗaya.


Afisawa 4:13
Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Saʼan nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamarsa.


Afisawa 6:16
Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar Mugun nan da ita.


Afisawa 6:23
Salama zuwa ga ʼyanʼuwa, da kuma ƙauna tare da bangaskiya daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


Filibbiyawa 1:25
Na tabbata haka ne, na kuwa san zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku farin ciki,


Filibbiyawa 1:27
Komene ne ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara


Filibbiyawa 2:17
Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka.


Filibbiyawa 3:9
a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi-adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya.


Kolossiyawa 1:4
Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka.


Kolossiyawa 1:23
Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.


Kolossiyawa 2:5
Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi.


Kolossiyawa 2:7
ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.


Kolossiyawa 2:12
Da yake an binne ku tare da shi cikin baftisma haka kuma aka tashe ku tare da shi ta wurin bangaskiyarku a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.


1 Tessalonikawa 1:3
Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.


1 Tessalonikawa 1:8
Saƙon Ubangiji ya fito daga gare ku ne ba a Makidoniya da Akayya kaɗai ba— bangaskiyarku ga Allah ta zama sananne koʼina. Saboda haka ba ma bukata mu faɗa wani abu a kai,


1 Tessalonikawa 3:2
Muka aiki Timoti, wanda yake ɗanʼuwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yǎ gina ku yǎ kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku,


1 Tessalonikawa 3:5
Saboda wannan, saʼad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yǎ zama mai jaraban nan ya riga ya jarabce ku, ƙoƙarinmu kuma yǎ zama banza.


1 Tessalonikawa 3:6
Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku.


1 Tessalonikawa 3:7
Saboda haka ʼyanʼuwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku.


1 Tessalonikawa 3:10
Dare da rana muna adduʼa da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.


1 Tessalonikawa 4:5
ba cikin muguwar shaʼawa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;


1 Tessalonikawa 5:8
Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.


2 Tessalonikawa 1:3
Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ʼyanʼuwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa.


2 Tessalonikawa 1:4
Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da ɗaurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.


2 Tessalonikawa 1:11
Sane da wannan, kullum muna adduʼa saboda ku, don Allahnmu yǎ sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yǎ cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza.


2 Tessalonikawa 3:2
Ku kuma yi adduʼa yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya.


1 Timoti 1:2
zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya: Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu.


1 Timoti 1:4
ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah-wanda yake ta wurin bangaskiya.


1 Timoti 1:5
Makasuɗin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya.


1 Timoti 1:13
Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya.


1 Timoti 1:14
An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.


1 Timoti 1:19
kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu.


1 Timoti 2:7
Don haka ne aka sa ni mai waʼazi, da manzo kuma -gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba-na kuma zama malami mai koya wa alʼummai alʼamarin bangaskiya da kuma na gaskiya.


1 Timoti 2:15
Amma mata Za ta sami ceto za su sami ceto ta wurin haihuwa-in suka ci gaba cikin bangaskiya, ƙauna da kuma tsarki tare da halin sanin ya kamata.


1 Timoti 3:9
Dole su riƙe asirin bangaskiya su kuma kasance da lamiri mai tsabta.


1 Timoti 3:13
Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu.


1 Timoti 4:1
Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa.


1 Timoti 4:6
In ka nuna wa ʼyanʼuwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi.


1 Timoti 4:12
Kada ka bar wani yǎ rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki.


1 Timoti 5:8
In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.


1 Timoti 6:10
Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri iri.


1 Timoti 6:11
Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.


1 Timoti 6:12
Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, saʼad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa.


1 Timoti 6:21
wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya. Alheri yǎ kasance tare da ku.


2 Timoti 1:5
An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka.


2 Timoti 1:13
Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu.


2 Timoti 2:18
waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu.


2 Timoti 2:22
Ka yi nesa da mugayen shaʼawace-shaʼawace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta.


2 Timoti 3:8
Kamar dai yadda Yannes da Yamberes suka tayar wa Musa, haka waɗannan mutane ma suke tayar wa gaskiya-mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda, in ana zancen bangaskiya ne, to, fa ba sa ciki.


2 Timoti 3:10
Kai kam, ka san kome game da koyarwata, da halina, da niyyata, bangaskiya, haƙuri, ƙauna, jimiri,


2 Timoti 3:15
da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.


2 Timoti 4:7
Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.


Titus 1:1
Wasiƙa daga Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah— 


Titus 1:4
Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya: Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu.


Titus 1:13
Wannan shaida gaskiya ce. Saboda haka, sai ka tsauta musu sosai, don su zama sahihai a wajen bangaskiya,


Titus 2:2
Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.


Titus 3:15
Dukan waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gaggai mini da masoyanmu, masu bangaskiya. Alheri yǎ kasance tare da ku duka.


Filemon 1:5
domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka.


Filemon 1:6
Ina adduʼa ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi.


Ibraniyawa 3:12
Ku lura fa, ʼyanʼuwa, cewa kada waninku yǎ kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai.


Ibraniyawa 3:14
Mu masu tarayya ne da Kiristi idan mun riƙe bangaskiyarmu da ƙarfi daga farko har zuwa ƙarshe.


Ibraniyawa 3:19
Saboda haka mun ga cewa ba su iya shiga ba, saboda rashin bangaskiyarsu ne.


Ibraniyawa 4:2
Gama mu ma mun ji an yi mana waʼazin bishara, kamar yadda su ma suka ji; sai dai saƙon da suka ji ba ta amfane su ba, domin waɗanda suka ji ba su karɓe shi da bangaskiya ba.


Ibraniyawa 4:14
Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi.


Ibraniyawa 6:1
Dole mu yi ƙoƙarin zama balagaggu mu kuma fara tunani game da abubuwan da suka fi koyarwan nan mai sauƙi game da Kiristi. Bai kamata mu ci gaba da magana game da me ya sa dole mu juye daga ayyukan da suke kawo mutuwa da kuma me ya sa za mu kasance da bangaskiya a cikin Allah ba.


Ibraniyawa 6:12
Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari.


Ibraniyawa 10:22
bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa.


Ibraniyawa 10:38
Amma mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan ji daɗinsa ba.”


Ibraniyawa 11:1
Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba.


Ibraniyawa 11:3
Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani.


Ibraniyawa 11:4
Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadayar da ta fi wadda Kayinu ya miƙa. Ta wurin bangaskiya aka yabe shi cewa shi mai adalci ne, saʼad da Allah ya yi magana mai kyau game da bayarwarsa. Ta wurin bangaskiya kuma har yanzu yana magana, ko da yake ya riga ya mutu.


Ibraniyawa 11:5
Ta wurin bangaskiya ne aka ɗauki Enok daga wannan rayuwa, ta haka bai ɗanɗana mutuwa ba; ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi. Gama kafin a ɗauke shi, an yabe shi a kan ya gamshi Allah.


Ibraniyawa 11:6
In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yǎ gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.


Ibraniyawa 11:7
Ta wurin bangaskiya Nuhu, saʼad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya.


Ibraniyawa 11:8
Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim, saʼad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasar da zai karɓi gādo daga baya, ya kuwa yi biyayya ya tafi, ko da yake bai san inda za shi ba.


Ibraniyawa 11:9
Ta wurin bangaskiya ya yi zama a ƙasar da aka yi masa alkawari kamar baƙo a baƙuwar ƙasa; ya zauna a tentuna, haka ma Ishaku da Yaƙub, waɗanda su ma magādan alkawarin nan ne tare da shi.


Ibraniyawa 11:11
Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce-Saratu kanta kuma bakararriya ce-ya iya zama mahaifi domin ya amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne.


Ibraniyawa 11:13
Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya saʼad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya.


Ibraniyawa 11:17
Ta wurin bangaskiya Ibrahim, saʼad da Allah ya gwada shi, sai ya miƙa Ishaku hadaya. Shi da ya karɓi alkawaran ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa,


Ibraniyawa 11:20
Ta wurin bangaskiya ne Ishaku ya albarkaci Yaƙub da Isuwa game da nan gabansu.


Ibraniyawa 11:21
Ta wurin bangaskiya ne Yaƙub, saʼad da yake bakin mutuwa, ya albarkaci kowane ɗan Yusuf, ya kuma yi sujada yayinda yake jingine a kan sandansa.


Ibraniyawa 11:22
Ta wurin bangaskiya ne Yusuf, saʼad da kwanakinsa suka yi kusan ƙarewa, ya yi magana game da fitowar Israʼilawa daga Masar ya kuma ba da umarni game da ƙasusuwansa.


Ibraniyawa 11:23
Ta wurin bangaskiya ne iyayen Musa suka ɓoye shi har wata uku bayan haihuwarsa, domin sun ga cewa shi ba kamar sauran yara ba ne, ba su kuwa ji tsoron umarnin sarki ba.


Ibraniyawa 11:24
Ta wurin bangaskiya ne Musa, saʼad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Firʼauna.


Ibraniyawa 11:27
Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba; ya kuwa jure domin ya ga wannan wanda ba a iya gani.


Ibraniyawa 11:28
Ta wurin bangaskiya ya kiyaye Bikin Ƙetarewa ya kuma yayyafa jini, domin kada mai hallakar ʼyaʼyan fari yǎ taɓa ʼyaʼyan fari na Israʼila.


Ibraniyawa 11:29
Ta wurin bangaskiya ne mutane suka bi ta cikin Jan Teku, sai ka ce a kan busasshiyar ƙasa; amma da Masarawa suka yi ƙoƙari su yi haka, sai aka nutsar da su.


Ibraniyawa 11:30
Ta wurin bangaskiya ne katangar Yeriko ta rushe, bayan mutane suka yi ta kewaye ta har kwana bakwai.


Ibraniyawa 11:31
Ta wurin bangaskiya ne ba a kashe Rahab karuwan nan, ta tare da marasa biyayya ba don ta marabci ʼyan leƙan asiri.


Ibraniyawa 11:33
waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki,


Ibraniyawa 11:39
Waɗannan duka an yabe su saboda bangaskiyarsu, duk da haka babu waninsu da ya sami abin da aka yi alkawari.


Ibraniyawa 11:40
Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga makasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu.


Ibraniyawa 12:2
Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah.


Ibraniyawa 13:7
Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.


Yaƙub 1:3
domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi ɗaurewa.


Yaƙub 2:5
Ku saurara, ʼyanʼuwana ƙaunatattu: Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?


Yaƙub 2:14
Wanda amfani ne, ʼyanʼuwana, a ce wani yǎ ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za ta iya cetonsa kuwa?


Yaƙub 2:17
Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.


Yaƙub 2:18
Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.” Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi.


Yaƙub 2:20
Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce?


Yaƙub 2:22
Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi.


Yaƙub 2:24
Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba.


Yaƙub 2:26
Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce.


Yaƙub 5:15
Adduʼar da aka yi cikin bangaskiya, za ta warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa.


1 Bitrus 1:5
ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yǎ zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci.


1 Bitrus 1:7
Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne-wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta-domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi.


1 Bitrus 1:9
gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.


1 Bitrus 1:21
Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.


1 Bitrus 5:9
Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ʼyanʼuwanku koʼina a duniya suna shan irin wahalolin nan.


2 Bitrus 1:1
Wasiƙa daga Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kiristi. Zuwa ga waɗanda ta wurin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi sun sami bangaskiya mai daraja irin tamu:


2 Bitrus 1:5
Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani;


1 Yohanna 5:4
domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasarar a kan duniya.


Yahuda 1:3
Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa tsarkaka sau ɗaya tak.


Yahuda 1:20
Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi adduʼa cikin Ruhu Mai Tsarki.


Ruʼuya ta Yohanna 2:13
Na san inda kake da zama-inda Shaiɗan yana da gadon sarautarsa. Duk da haka ka riƙe sunana da gaske. Ba ka yi mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a kwanakin Antifas, amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a birninku-inda Shaiɗan yake zama.


Ruʼuya ta Yohanna 2:19
Na san ayyukanka, ƙaunarka da bangaskiyarka, hidimarka da ɗaurewarka, kuma cewa kana yin abubuwa a yanzu fiye da abin da ka yi da farko.


Ruʼuya ta Yohanna 21:8
Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata-wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutan da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”


Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc