A A A A A


Bincika

Mattiyu 4:2
Bayan ya yi azumi yini arbaʼin da kuma dare arbaʼin, sai ya ji yunwa.


Mattiyu 6:16
“Saʼad da kuma kuna azumi, kada ku ɓata fuska, yadda munafukai suke yi. Sukan ɓata fuskokinsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke.


Mattiyu 6:17
Amma saʼad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka,


Mattiyu 6:18
domin kada mutane su ga alama cewa kana azumi, sai dai ga Ubanka kaɗai wanda ba a gani; Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.


Mattiyu 9:14
Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?”


Mattiyu 9:15
Yesu ya amsa, ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, saʼan nan za su yi azumi.


Markus 2:18
To, almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, sai waɗansu mutane suka zo suka tambayi Yesu, suka ce, “Yaya almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, amma almajiranka ba sa yi?”


Markus 2:19
Yesu ya amsa, ya ce, “Yaya abokan ango za su yi azumi, saʼad da yana tare da su? Ai, ba za su yi ba, muddin yana tare da su.


Markus 2:20
Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A saʼan nan ne fa za su yi azumi.


Luka 2:37
ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da adduʼa.


Luka 5:33
Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da adduʼa, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.”


Luka 5:34
Yesu ya amsa, ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su?


Luka 5:35
Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.”


Luka 18:12
Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’


Ayyukan Manzanni 13:2
Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawul domin aikin da na kira su.”


Ayyukan Manzanni 13:3
Saboda haka bayan suka yi azumi da adduʼa, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.


Ayyukan Manzanni 14:23
Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da adduʼa da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi.


Ayyukan Manzanni 27:9
An riga an ɓata lokaci da yawa, tafiya kuwa ta riga ta zama da hatsari domin a lokacin Azumi ya riga ta wuce. Saboda haka Bulus ya gargaɗe su,


Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc