Instagram
English
A A A A A
Bincika
Mattiyu 1:18
Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance: An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf, amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


Mattiyu 3:4
Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fari ne da zumar jeji.


Mattiyu 7:16
Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?


Mattiyu 12:29
“Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yǎ ƙwace masa kaya ba tare da ya fara ɗaure mai ƙarfin nan tukuna ba? Saʼan nan zai iya washe gidansa.


Mattiyu 13:30
Ku ƙyale su su yi girma tare sai lokacin girbi. A lokacin zan gaya wa masu girbi: Da fari ku tara ciyayin ku kuma ɗaure su dami-dami don a ƙone; saʼan nan ku tara alkamar ku kuma kawo su cikin rumbuna.’ ”


Матфей 14:3
To, Hiridus ya kama Yohanna ya ɗaure, ya kuma sa shi cikin kurkuku saboda Hiridiyas, matar ɗanʼuwansa Filibus,


Матфей 14:4
gama Yohanna ya dinga ce masa, “Ba daidai ba ne ka aure ta.”


Матфей 16:19
Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka ɗaure a duniya zai zama a ɗaure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”


Матфей 18:18
“Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka ɗaure a duniya, za a ɗaure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.


Матфей 19:9
Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.”


Матфей 19:10
Almajiran suka ce masa, “In haka yake tsakanin miji da mata, ashe, ya ma fi kyau kada a yi aure.”


Матфей 19:12
Gama waɗansu bābānni ne domin haka aka haife su; waɗansu kuwa mutane ne suka mai da su haka; waɗansu kuma sun ƙi aure ne saboda mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar wannan yǎ ɗauka.”


Матфей 21:2
yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a ɗaure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini.


Матфей 21:19
Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ʼyaʼya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane.


Матфей 21:20
Saʼad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?”


Матфей 21:21
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku’, sai yǎ faru.


Матфей 22:2
“Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa.


Матфей 22:4
“Sai ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci: An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’


Матфей 22:8
“Saʼan nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba.’


Матфей 22:10
Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi.


Матфей 22:11
“Amma da sarkin ya shigo don yǎ ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren.


Матфей 22:12
Ya yi tambaya, ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.


Матфей 22:13
“Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku ɗaure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’


Матфей 22:25
A cikinmu an yi ʼyanʼuwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu, da yake bai sami ʼyaʼya ba, sai ya bar matarsa wa ɗanʼuwansa.


Матфей 22:28
To, a tashin matattu, matar wa a cikinsu bakwai ɗin nan za ta zama, da yake dukansu sun aure ta?”


Матфей 22:30
Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar malaʼiku a sama.


Матфей 24:32
“Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure: Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa.


Матфей 24:38
Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi;


Матфей 25:10
“Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.


Матфей 27:2
Suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus.


Luka 1:27
gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu.


Luka 2:36
Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure,


Luka 6:44
Kowane itace da irin ʼyaʼyansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ʼyaʼyan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ʼyaʼyan inabi daga sarƙaƙƙiya.


Luka 8:29
Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun yakan sha kamunsa. Ko da yake akan ɗaure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa.


Luka 10:34
Ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, saʼan nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa.


Luka 12:36
kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan.


Luka 13:6
Sai ya faɗa wannan misali, ya ce, “Wani mutum yana da itacen ɓaure, da aka shuka a gonar inabinsa. Da ya je cire ʼyaʼyan itacen, sai ya tarar ba ta yi ʼyaʼya ba.


Luka 13:7
Sai ya ce wa mai lura da gonar inabin, ‘Yau shekara uku ke nan ina zuwa neman ʼyaʼyan ɓaure daga itacen nan, amma ba na samun kome. Sare shi! Don me za a bar shi ya tare wuri.’


Luka 13:16
Ashe, ba ya kamata a ʼyantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya ɗaure ta ba?”


Luka 14:8
“In wani ya gayyace ka bikin aure, kada ka zaɓi wurin zama mai ban girma, don wataƙila akwai wani da ya fi ka girma, da aka gayyata.


Luka 14:20
Har yanzu wani ya ce, ‘Na yi aure yanzun nan, don haka ni ba zan iya zuwa ba.’


Luka 17:27
Mutane suna ci, suna sha, suna auraya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Saʼan nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka.


Luka 19:30
“Ku je ƙauyen da yake gaba da ku. Da kuna shiga, za ku tarar da wani ɗan jaki, wadda ba wanda ya taɓa hawa, a ɗaure a wurin. Ku kunce shi ku kawo nan.


Luka 20:28
“Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗanʼuwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ʼyaʼya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗanʼuwansa ʼyaʼya.’


Luka 20:31
da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ʼyaʼya.


Luka 20:33
Shin, a tashin matattu, matar wa za ta zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.”


Luka 20:34
Yesu ya amsa, ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure,


Luka 20:35
amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba.


Luka 21:29
Sai ya gaya musu wannan misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa.


Yohanna 1:48
Natanayel ya yi tambaya, ya ce, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa, ya ce, “Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yǎ kira ka.”


Yohanna 1:50
Yesu ya ce, “Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka.”


Yohanna 2:1
A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can,


Yohanna 2:2
aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren.


Yohanna 11:44
Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a ɗaure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tube kayan bizo, ku bar shi yǎ tafi.”


Yohanna 18:12
Sai ƙungiyar soja tare da shugaban sojanta da kuma maʼaikatan Yahudawa suka kama Yesu. Suka ɗaure shi


Yohanna 18:24
Sai Annas ya aika da shi, a ɗaure, wurin Kayifas babban firist.


Ayyukan Manzanni 8:23
Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma ɗaure cikin zunubi.”


Ayyukan Manzanni 12:6
A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shariʼa, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, ɗaure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa.


Ayyukan Manzanni 21:9
Yana kuwa da ʼyaʼya huɗu ʼyan mata waɗanda ba su yi aure ba, waɗanda suka yi annabci.


Ayyukan Manzanni 21:11
Da ya zo wurinmu, sai ya ɗauki ɗamarar Bulus, ya ɗaura hannuwansa da ƙafafunsa da ita saʼan nan ya ce, “Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara su kuma ba da shi ga Alʼummai.’ ”


Ayyukan Manzanni 21:13
Sai Bulus ya amsa, ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a ɗaure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”


Ayyukan Manzanni 21:33
Shugaban ƙungiyar sojan ya zo ya kama shi ya ba da umarni a ɗaure shi da sarƙoƙi biyu. Saʼan nan ya yi tambaya ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi.


Ayyukan Manzanni 22:5
kamar yadda babban firist da dukan Majalisa za su iya shaida. Na ma karɓi wasiƙu daga gare su zuwa ga ʼyanʼuwansu a Damaskus, na kuma tafi can don in kawo waɗannan mutane a ɗaure zuwa Urushalima don a hukunta su.


Ayyukan Manzanni 23:29
Na tarar cewa zargin da ake masa ya shafi waɗansu abubuwan da suka shafi dokarsu ne, amma ba wani zargi a kansa da ya isa kisa ko a ɗaure shi.


Ayyukan Manzanni 25:14
Da yake za su yi kwanaki da dama a can, sai Festus ya tattauna batun Bulus da sarki. Ya ce: “Akwai mutumin da Felis ya bari a ɗaure.


Ayyukan Manzanni 28:20
Saboda wannan ne na nemi in ganku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Israʼila ne, nake a ɗaure da wannan sarƙa.”


Romawa 7:2
Misali, bisa ga doka mace mai aure tana ɗaure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure.


Romawa 7:6
Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya ɗaure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙaʼida ba.


Romawa 11:17
In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan niʼimar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,


Romawa 11:19
To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.”


Romawa 11:23
In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su.


Romawa 11:24
Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?


Romawa 11:32
Gama Allah ya ɗaure dukan mutane ga rashin biyayya don yǎ nuna jinƙai ga kowa.


Romawa 16:7
Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka ɗaure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi.


1 Korintiyawa 7:1
To, game da zancen da kuka rubuta: Yana da kyau mutum yǎ zauna ba aure.


1 Korintiyawa 7:3
Ya kamata miji yǎ cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta.


1 Korintiyawa 7:8
To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa: Yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake.


1 Korintiyawa 7:9
Sai dai in ba za su iya kame kansu ba, to, su yi aure, don ya fi kyau a yi aure, da shaʼawa ta sha kan mutum.


1 Korintiyawa 7:10
Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa: Kada mace ta rabu da mijinta.


1 Korintiyawa 7:11
In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yǎ saki matarsa.


1 Korintiyawa 7:13
In kuma mace tana da miji wanda ba mai bi ba ne, kuma yana so yǎ zauna tare da ita, kada ta kashe auren.


1 Korintiyawa 7:15
Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne.


1 Korintiyawa 7:27
In kuna da aure, kada ku nemi kashe auren. In ba ku da aure, kada ku nemi yin aure.


1 Korintiyawa 7:28
Amma idan ka riga ka yi aure, to, ba laifi, ba zunubi ba ne, kuma idan yarinya ta yi aure, ba ta yi laifi ba. Sai dai waɗanda suka yi aure za su fuskanci damuwoyi masu yawa a cikin rayuwa, ni kuwa ina so in fisshe su daga wannan.


1 Korintiyawa 7:32
Zan so ku ʼyantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da alʼamuran Ubangiji-yadda zai gamshi Ubangiji.


1 Korintiyawa 7:33
Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da alʼamuran wannan duniya-yadda zai gamshi matarsa— 


1 Korintiyawa 7:34
hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da alʼamuran Ubangiji: Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da alʼamuran wannan duniya-yadda za ta gamshi mijinta.


1 Korintiyawa 7:36
In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yǎ yi aure, to, sai yǎ yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure.


1 Korintiyawa 7:38
Don haka, wanda ya auri budurwar ya yi daidai, amma wanda bai aure ta ba ya ma fi.


2 Korintiyawa 11:2
Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa tsantsa.


Galatiyawa 3:23
Kafin bangaskiyan nan ta zo, muna a ɗaure kamar ʼyan kurkuku ta wurin Doka, a kulle sai a lokacin da bangaskiya ta bayyana.


Afisawa 5:22
Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku kamar ga Ubangiji.


Filibbiyawa 1:7
Daidai ne in yi wannan tunani game da dukanku, da yake kuna a zuciyata; domin ko ina ɗaure cikin sarƙoƙi ko ina kāre bishara ina kuma tabbatar da ita, dukanku kuna tarayya cikin alherin Allah tare da ni.


Filibbiyawa 1:13
Ta haka, ya zama sananne ga dukan masu gadin fada da kuma ga kowa cewa an ɗaure ni da sarƙoƙi saboda Kiristi.


1 Tessalonikawa 3:1
Saboda haka da muka kāsa ɗaurewa, sai muka ga ya fi kyau a bar mu a Aten mu kaɗai.


2 Tessalonikawa 1:4
Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da ɗaurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.


1 Timoti 4:3
Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya.


1 Timoti 4:16
Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka ɗaure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka.


1 Timoti 5:11
Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama saʼad da shaʼawar jikinsu ta kāsa ɗaurewa game da waʼadin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure.


1 Timoti 5:14
Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ʼyaʼya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna.


2 Timoti 2:9
wadda nake shan wahala har ga ɗaurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a ɗaure take ba.


Евреям 12:1
Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin ɗaure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa.


Евреям 13:4
Aure yǎ zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.


1 Bitrus 3:1
Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba


1 Bitrus 3:7
Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yǎ hana adduʼoʼinku.


2 Bitrus 1:6
ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara masa ɗaurewa; ga ɗaurewa kuwa ku ƙara mata tsoron Allah;


Yahuda 1:6
Malaʼikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba amma suka bar gidansu kuwa-waɗannan ne fa ya tsare a duhu, ɗaure da dawwamammun sarƙoƙi saboda hukunci a babbar Ranan nan.


Ruʼuya ta Yohanna 1:13
A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,” saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya ɗaure a ƙirjinsa.


Ruʼuya ta Yohanna 2:2
Na san ayyukanka, faman aikinka da ɗaurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne.


Ruʼuya ta Yohanna 2:3
Kai kam ka ɗaure ka kuma jimre da wahala saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.


Ruʼuya ta Yohanna 2:19
Na san ayyukanka, ƙaunarka da bangaskiyarka, hidimarka da ɗaurewarka, kuma cewa kana yin abubuwa a yanzu fiye da abin da ka yi da farko.


Ruʼuya ta Yohanna 6:13
taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ʼyaʼyan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure saʼad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi.


Ruʼuya ta Yohanna 9:14
Ta ce wa malaʼika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki malaʼiku huɗun nan da suke a ɗaure a babban kogin Yuferites.”


Ruʼuya ta Yohanna 18:12
kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da luʼu-luʼai; lallausan lilin, tufa masu launin shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi;


Ruʼuya ta Yohanna 19:7
Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna mu kuma ɗaukaka shi! Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi, amaryarsa kuwa ta shirya kanta.


Ruʼuya ta Yohanna 19:9
Sai malaʼikan ya ce mini, “Rubuta: ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”


Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc