A A A A A


Bincika

Luka 11:48
Wannan ya shaida cewa kun amince da abin da kakannin-kakanninku suka yi. Sun karkashe annabawa, ku kuma kun gina kaburburansu.


Luka 16:10
“Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba.


Luka 16:11
In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya?


Yohanna 2:24
Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane.


Yohanna 4:50
Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.” Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi.


Yohanna 6:27
Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yǎ zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.”


Yohanna 12:4
Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba, ya ce,


Ayyukan Manzanni 16:15
Da aka yi mata baftisma tare da iyalin gidanta, sai ta gayyace mu zuwa gidanta. Ta ce, “In kun amince ni mai bi ce cikin Ubangiji, sai ku zo ku sauka a gidana.” Sai ta kuwa rinjaye mu.


Ayyukan Manzanni 17:4
Waɗansu Yahudawa suka amince suka kuma bi Bulus da Sila, haka ma Helenawa da yawa masu tsoron Allah da kuma manyan mata ba kaɗan ba.


Ayyukan Manzanni 20:21
Na yi shela ga Yahudawa da Helenawa cewa dole juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.


Ayyukan Manzanni 23:21
Kada ka yarda da su, domin fiye da mutum arbaʼin daga cikinsu suna fakonsa. Sun yi rantsuwa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe shi. Suna nan a shirye yanzu, suna jira ka amince da roƙonsu.”


Ayyukan Manzanni 24:3
Koʼina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka.


Ayyukan Manzanni 24:14
Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa,


Romawa 2:18
in ka san nufinsa ka kuma amince da abin da yake mafifici domin an koyar da kai bisa ga doka;


1 Korintiyawa 11:19
Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku.


1 Korintiyawa 13:7
Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.


1 Korintiyawa 16:3
In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima.


2 Korintiyawa 1:15
Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.


2 Korintiyawa 2:3
Na rubuta yadda na yi ne saboda saʼad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka.


2 Korintiyawa 3:4
Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah.


2 Korintiyawa 7:4
Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.


2 Korintiyawa 7:16
Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske.


2 Korintiyawa 8:22
Ban da wannan kuma, mun aiko da ɗanʼuwanmu tare da su, wanda ya sha tabbatar mana da ƙwazonsa ta hanyoyi iri-iri, musamman yanzu, domin ya amince da ku da gaske.


2 Korintiyawa 9:4
Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba--kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku.


2 Korintiyawa 10:18
Ai, ba mai yabon kansa ake amincewa da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.


Galatiyawa 1:10
Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko na Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba.


1 Tessalonikawa 2:4
A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yǎ danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu.


1 Timoti 1:12
Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa.


2 Timoti 2:15
Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, maʼaikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.


Titus 2:10
kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali.


Ibraniyawa 11:11
Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce-Saratu kanta kuma bakararriya ce-ya iya zama mahaifi domin ya amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne.


Ibraniyawa 11:13
Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya saʼad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya.


Hausa Bible 2013
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc