A A A A A


Bincika

Mattiyu 1:23
“Ga shi budurwa za ta yi ciki, za ta haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel,”   — wanda yake nufin, “Allah tare da mu.”


Mattiyu 3:9
Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya ta da ʼyaʼya wa Ibrahim.


Mattiyu 3:16
Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa.


Mattiyu 4:3
Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.”


Mattiyu 4:4
Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ba da burodi kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’ ”


Mattiyu 4:6
Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, dira ƙasa. Gama a rubuce yake: “ ‘Zai umarci malaʼikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’ ”


Mattiyu 4:7
Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa: ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”


Mattiyu 4:10
Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake: ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’ ”


Mattiyu 5:8
Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.


Mattiyu 5:9
Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ʼyaʼyan Allah.


Mattiyu 5:34
Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam: ko da sama, domin kursiyin Allah ne;


Mattiyu 5:47
In kuwa kuna gai da ʼyanʼuwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba?


Mattiyu 6:7
Saʼad da kuma kuke adduʼa, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu.


Mattiyu 6:24
“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yǎ ƙi ɗaya, yǎ ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yǎ yi aminci ga ɗaya, saʼan nan yǎ rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah ku kuma bauta wa Kuɗi gaba ɗaya.”


Mattiyu 6:30
In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, Ya ku masu ƙarancin bangaskiya?


Mattiyu 6:32
Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu.


Mattiyu 6:33
Sai dai da farko, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.


Mattiyu 8:29
Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yǎ yi?


Mattiyu 9:8
Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan.


Mattiyu 12:4
Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin-wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai.


Mattiyu 12:28
Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.


Mattiyu 14:33
Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”


Mattiyu 15:3
Yesu ya amsa, ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda alʼadarku?


Mattiyu 15:4
Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’


Mattiyu 15:5
Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’


Mattiyu 15:6
ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda alʼadarku.


Mattiyu 15:31
Mutanen kuwa suka yi mamaki saʼad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Israʼila.


Mattiyu 16:16
Siman Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai.”


Mattiyu 16:23
Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin alʼamuran Allah, sai dai alʼamuran mutane.”


Mattiyu 18:17
In kuwa ya ƙi yǎ saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yǎ saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.


Mattiyu 19:6
Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yǎ raba.”


Mattiyu 19:24
Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yǎ shiga ta kafar allura, da mai arziki yǎ shiga mulkin Allah.”


Mattiyu 19:26
Yesu ya dube su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.”


Mattiyu 21:31
“Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.


Mattiyu 21:43
“Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani.


Mattiyu 22:16
Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hirudus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba.


Mattiyu 22:21
Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”


Mattiyu 22:29
Yesu ya amsa, ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba.


Mattiyu 22:31
Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu-ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne,


Mattiyu 22:32
‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, sai dai na masu rai.”


Mattiyu 22:37
Yesu ya amsa, ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’


Mattiyu 23:22
Duk kuma wanda ya rantse da sama, ya rantse ne da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune a kansa.


Mattiyu 26:61
suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”


Mattiyu 26:63
Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai: Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”


Mattiyu 27:40
suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”


Mattiyu 27:43
Ya dogara ga Allah. Bari Allah yǎ cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”


Mattiyu 27:46
Wajen saʼa ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani” — wanda yake nufi, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”


Mattiyu 27:54
Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizan ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”


Markus 1:1
Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah.


Markus 1:14
Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah.


Markus 1:15
Yana ce, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”


Markus 1:24
“Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai-Mai Tsarki nan na Allah!”


Markus 2:7
“Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”


Markus 2:12
Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!”


Markus 2:26
Ya shiga gidan Allah a zamanin Abiyatar babban firist, ya ci keɓaɓɓen burodin nan, ya kuma ba wa abokan tafiyarsa abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka?”


Markus 3:11
Duk saʼad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.”


Markus 3:35
Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗanʼuwana, da ʼyarʼuwata, da kuma mahaifiyata.”


Markus 4:11
Sai ya ce musu, “An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai.


Markus 4:14
Manomi yakan shuka maganar Allah.


Markus 4:15
Waɗansu mutane suna kama da irin da ya fāɗi a kan hanya, inda akan shuka maganar Allah. Da jin maganar, nan da nan sai Shaiɗan yǎ zo yǎ ɗauke maganar da aka shuka a zuciyarsu.


Markus 4:16
Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki.


Markus 4:18
Har yanzu, waɗansu mutane suna kama da irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar Allah,


Markus 4:20
Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, saʼan nan kuma su fid da amfani riɓi talatin talatin, ko sittin sittin, ko ɗari ɗari.”


Markus 4:26
Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona.


Markus 4:30
Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta mulkin Allah, ko kuwa da wane misali za mu bayyana shi?


Markus 5:7
Ya yi ihu da babbar murya, ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!”


Markus 7:8
Kun bar umarnan Allah, kuna bin alʼadun mutane.”


Markus 7:9
Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye alʼadunku!


Markus 7:11
Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah),


Markus 7:13
Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin alʼadun da kuke miƙa wa ʼyaʼyanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.”


Markus 8:33
Amma da Yesu ya juya ya dubi almajiransa, sai ya tsauta wa Bitrus, ya ce, “Tashi daga nan Shaiɗan! Ba ka da alʼamuran Allah a zuciyarka, sai na mutane.”


Markus 9:1
Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”


Markus 9:47
In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu,


Markus 10:6
Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’


Markus 10:9
Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yǎ raba.”


Markus 10:14
Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.


Markus 10:15
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”


Markus 10:18
Yesu ya amsa, ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari sai Allah kaɗai.


Markus 10:23
Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!”


Markus 10:24
Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “ʼYaʼyana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah!


Markus 10:25
Ya fi sauƙi raƙumi yǎ shiga ta kafar allura, da mai arziki yǎ shiga mulkin Allah.”


Markus 10:27
Yesu ya kalle su, ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.”


Markus 11:22
Yesu ya amsa, ya ce, “Ku gaskata da Allah.


Markus 12:14
Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin raʼayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu?


Markus 12:17
Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.” Suka yi mamakinsa ƙwarai.


Markus 12:24
Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah?


Markus 12:26
Game da tashin matattu kuwa-ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi, ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?


Markus 12:27
Shi ba Allah na matattu ba ne, sai dai na masu rai. Kun yi mummunan kuskure!”


Markus 12:29
Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan: ‘Ya ku Israʼila, ku saurara, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.


Markus 12:30
Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’


Markus 12:32
Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi.


Markus 12:33
Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.”


Markus 12:34
Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya.


Markus 14:25
Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ʼyaʼyan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”


Markus 15:34
A daidai saʼa ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” Wanda yake nufin, “Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?”


Markus 15:39
Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”


Markus 15:43
Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.


Markus 16:19
Bayan Ubangiji Yesu ya yi musu magana, sai aka ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zauna a hannun dama na Allah.


Luka 1:6
Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.


Luka 1:8
Wata rana da lokacin aikin firistoci na sashen Zakariya na yin hidima ya kewayo, yana kuma cikin hidimarsa ta firist a gaban Allah,


Luka 1:16
Shi ne zai juye mutanen Israʼila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu.


Luka 1:19
Malaʼikan ya ce, “Ni ne Jibraʼilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi.


Luka 1:26
A wata na shida, sai Allah ya aiki malaʼika Jibraʼilu zuwa Nazaret, wani gari a Galili,


Luka 1:30
Amma malaʼikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah.


Luka 1:32
Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar mahaifinsa Dawuda,


Luka 1:35
Malaʼikan ya amsa, ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.


Luka 1:37
Gama ba abin da zai gagari Allah.”


Luka 1:38
Maryamu ta amsa ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yǎ zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai malaʼikan ya tafi abinsa.


Luka 1:47
ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,


Luka 1:64
Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah.


Luka 1:68
“Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Israʼila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.


Luka 1:78
saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna, hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,


Luka 2:13
Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da malaʼikan, suna yabon Allah suna cewa,


Luka 2:14
“Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”


Luka 2:20
Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.


Luka 2:28
sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa:


Luka 2:38
Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.


Luka 2:40
Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa.


Luka 2:52
Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.


Luka 3:2
a lokacin da Annas da Kayifas suke manyan firistoci, sai maganar Allah ta zo wurin Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.


Luka 3:6
Dukan ʼyan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”


Luka 3:8
Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya ta da ʼyaʼya wa Ibrahim.


Luka 3:38
ɗan Enosh, ɗan Shitu, ɗan Adamu, ɗan Allah.


Luka 4:3
Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yǎ zama burodi.”


Luka 4:8
Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”


Luka 4:9
Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali, ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa.


Luka 4:12
Yesu ya amsa, ya ce, “An ce: ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”


Luka 4:34
“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai--Mai Tsarki na Allah!”


Luka 4:41
Bugu da ƙari, aljanu suka fiffita daga cikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya kwaɓe su, ya hana su magana, don sun san cewa shi ne Kiristi.


Luka 4:43
Amma ya ce, “Dole in yi waʼazin bisharar mulkin Allah ga sauran garuruwa, saboda wannan ne aka aiko ni.”


Luka 5:1
Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah,


Luka 5:21
Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”


Luka 5:25
Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.


Luka 5:26
Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.”


Luka 6:4
Ya shiga gidan Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodi, saʼan nan ya ci abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka. Ya kuma ba wa abokan tafiyarsa?”


Luka 6:12
Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yǎ yi adduʼa, ya kuma kwana yana adduʼa ga Allah.


Luka 6:20
Da ya dubi almajiransa, sai ya ce, “Masu albarka ne ku da kuke matalauta, gama mulkin Allah naku ne.


Luka 7:16
Sai tsoro ya kama su duka, suka yabi Allah, suna cewa, “Babban annabi ya bayyana a cikinmu. Allah ya zo domin yǎ taimaki mutanensa.”


Luka 7:28
Ina faɗa muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”


Luka 7:29
(Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma.


Luka 7:30
Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.)


Luka 8:1
Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana waʼazin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi,


Luka 8:10
Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda, “ ‘ko da yake suna ƙallo, ba za su gani ba, ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’ 


Luka 8:11
“Ga maʼanar misalin: irin, shi ne maganar Allah.


Luka 8:21
Ya amsa ya ce, “Uwana da ʼyanʼuwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.”


Luka 8:28
Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!”


Luka 8:39
“Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin.


Luka 9:2
Ya kuma aike su, su yi waʼazin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.


Luka 9:11
Amma taron mutane suka ji labari, sai suka bi shi. Ya marabce su, kuma ya yi musu magana a kan mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkarwa.


Luka 9:20
“Amma ku fa, wa, kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa, ya ce, “Kiristi na Allah.”


Luka 9:27
Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su ga mutuwa ba, sai sun ga mulkin Allah.”


Luka 9:43
Duk suka yi mamakin girman Allah. Yayinda kowa yana cikin mamakin dukan abubuwan da Yesu ya yi, sai ya ce wa almajiransa,


Luka 9:60
Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”


Luka 9:62
Yesu ya amsa, ya ce, “Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, saʼan nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba.”


Luka 10:9
Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’


Luka 10:11
‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.” ’


Luka 10:27
Sai ya amsa, ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’, kuma ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ”


Luka 11:20
Amma in da ikon Allah ne ni nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan.


Luka 11:28
Yesu ya amsa, ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.”


Luka 11:42
“Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na anananku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon.


Luka 11:49
Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa, ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’


Luka 12:6
Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba.


Luka 12:8
“Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban malaʼikun Allah.


Luka 12:9
Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban malaʼikun Allah.


Luka 12:20
“Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a bidi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’


Luka 12:21
“Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”


Luka 12:24
Ku dubi hankaki. Ba sukan yi shuki ko girbi ba, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa!


Luka 12:28
In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, saʼan nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!


Luka 12:30
Gama duniya ta masu bautar gumaka, da ba ta san Allah ba, tana faman neman dukan irin waɗannan abubuwa. Amma Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu.


Luka 13:13
Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.


Luka 13:18
Sai Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi?


Luka 13:20
Ya sāke tambaya, “Da me zan kwatanta mulkin Allah?


Luka 13:28
“ Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, saʼad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje.


Luka 13:29
Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah.


Luka 14:15
Da jin haka, sai wani da yake tare da shi a tebur ɗin, ya ce wa Yesu, “Mai albarka ne wanda zai ci abinci a bikin nan a mulkin Allah.”


Luka 15:10
Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban malaʼikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.”


Luka 16:13
“Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya ɗage ga yi wa ɗaya bauta, saʼan nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.”


Luka 16:15
Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah.


Luka 16:16
“An yi shelar Doka da Annabawa har zuwa lokacin Yohanna. Tun daga lokacin nan, bisharar mulkin Allah ne ake waʼazinta, kowa kuma yana ƙoƙarin kutsa kai ya shiga.


Luka 17:15
Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya.


Luka 17:18
Ba wanda ya dawo don ya yabi Allah, sai dai wannan baƙon?”


Luka 17:20
Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin ƙallon ku ba.


Luka 17:21
Mutane kuma ba za su ce, ‘Ga shi nan,’ ko kuma, ‘Ga shi can’ ba, domin mulkin Allah yana cikinku ne.”


Luka 18:2
Ya ce, “A wani gari, an yi wani alƙali wanda ba ya tsoron Allah, bai kuma kula da mutane ba.


Luka 18:4
“An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba,


Luka 18:7
Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne?


Luka 18:11
Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi adduʼa game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan.


Luka 18:13
“Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’


Luka 18:14
“Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”


Luka 18:16
Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa, ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.


Luka 18:17
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”


Luka 18:19
Yesu ya amsa, ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, babu wani managarci, sai Allah kaɗai.


Luka 18:24
Yesu ya kalle shi, ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah!


Luka 18:25
Hakika, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta ƙofar idon allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”


Luka 18:27
Yesu ya amsa, ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”


Luka 18:29
Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ʼyanʼuwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah,


Luka 18:43
Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.


Luka 19:11
Yayinda suna cikin sauraron wannan, sai ya ci gaba da gaya musu wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima, kuma mutanen suna tsammani mulkin Allah zai bayyana, nan da nan.


Luka 19:37
Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani.


Luka 19:44
Za su fyaɗa ke a ƙasa, ke da ʼyaʼyan da suke cikin katanganki. Ba za su bar wani dutse a kan wani ba, saboda ba ki gane da lokacin da Allah zai ziyarce ki ba.”


Luka 20:16
Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.” Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!”


Luka 20:21
Sai ʼyan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya.


Luka 20:25
Suka amsa, “Na Kaisar.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”


Luka 20:36
Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar malaʼiku ne. Su ʼyaʼyan Allah ne, tun da su ʼyaʼyan tashin matattu ne.


Luka 20:37
Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’


Luka 20:38
Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.”


Luka 21:5
Waɗansu daga cikin almajiransa, suka fara magana a kan yadda aka yi wa haikalin ado da duwatsu masu kyau, da kuma kyautai da aka keɓe wa Allah. Amma Yesu ya ce,


Luka 21:31
Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.


Luka 22:16
Ina dai gaya muku, ba zan ƙara cin sa ba, sai ya sami cika a mulkin Allah.”


Luka 22:18
Ina dai gaya muku, ba zan ƙara sha daga ʼyaʼyan inabi ba, sai mulkin Allah ya zo.”


Luka 22:69
Amma daga yanzu, Ɗan Mutum zai zauna a hannun dama na Allah Mai Iko.”


Luka 22:70
Sai dukansu suka tambaya, “Wato, kai Ɗan Allah ke nan?” Ya amma ya ce, “Kun faɗa daidai, ni ne.”


Luka 23:35
Mutanen suka tsaya suna ƙallo. Har masu mulki ma suka yi masa baʼa, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.”


Luka 23:40
Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi, ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi?


Luka 23:47
Da jarumin ya ga abin da ya faru, sai ya yabi Allah, ya ce, “Gaskiya, wannan mutum mai adalci ne.”


Luka 23:51
shi dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba. Shi daga Arimateya ne wani garin Yahudiya. Yana kuma jiran zuwa mulkin Allah.


Luka 24:19
Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?” Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane.


Luka 24:53
Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.


Yohanna 1:1
Tun fara farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.


Yohanna 1:2
Yana nan tare da Allah tun fara farawa.


Yohanna 1:6
Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna.


Yohanna 1:12
Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ʼyaʼyan Allah— 


Yohanna 1:13
ʼyaʼyan da aka haifa ba bisa hanyar ʼyan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.


Yohanna 1:18
Ba wanda ya taɓa ganin Allah, sai dai Allah da yake Ɗaya da kuma Makaɗaici wanda yake a gefen Uba, shi ne ya bayyana shi.


Yohanna 1:29
Washegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!


Yohanna 1:34
Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”


Yohanna 1:36
Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!”


Yohanna 1:49
Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Israʼila.”


Yohanna 1:51
Sai ya ƙara da cewa, “Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, malaʼikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum.”


Yohanna 3:2
Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”


Yohanna 3:3
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”


Yohanna 3:5
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.


Yohanna 3:16
“Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yǎ hallaka sai dai yǎ sami rai madawwami.


Yohanna 3:17
Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yǎ yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yǎ ceci duniya ta wurinsa.


Yohanna 3:18
Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.


Yohanna 3:21
Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.”


Yohanna 3:33
Mutumin da ya yarda da ita ya tabbatar da cewa Allah mai gaskiya ne.


Yohanna 3:34
Gama wannan da Allah ya aiko yakan faɗi kalmomin Allah ne, gama Allah yana ba da Ruhu babu iyaka.


Yohanna 3:36
Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”


Yohanna 4:10
Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, da shi kuwa ya ba ki ruwan rai.”


Yohanna 4:24
Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada cikin ruhu da kuma cikin gaskiya.”


Yohanna 5:18
Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don ya karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah.


Yohanna 5:25
Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo saʼad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.


Yohanna 5:42
na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku.


Yohanna 5:44
Ta yaya za ku gaskata in kuna nemi yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici ba?


Yohanna 6:27
Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yǎ zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.”


Yohanna 6:28
Sai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?”


Yohanna 6:29
Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne: a gaskata da wanda ya aiko.”


Yohanna 6:33
Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”


Yohanna 6:45
A rubuce yake a cikin Annabawa cewa: ‘Allah zai koyar da dukansu.’ Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina.


Yohanna 6:46
Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban.


Yohanna 6:69
Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”


Yohanna 7:17
Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana.


Yohanna 8:40
Ga shi kun ƙudura, sai kun kashe ni, ni mutumin da ya faɗa muku gaskiyar da na ji daga Allah. Ibrahim bai yi irin waɗannan abubuwa ba.


Yohanna 8:41
Kuna yin abubuwan da ubanku yake yi ne.” Suka ce, “Mu fa ba shegu ba ne. Uba guda kaɗai da muke da shi, shi ne Allah kansa.”


Yohanna 8:42
Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni.


Yohanna 8:47
Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jinsa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”


Yohanna 8:54
Yesu ya amsa, ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni.


Yohanna 9:3
Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa.


Yohanna 9:16
Sai waɗansu daga cikin Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye ranar Asabbaci.” Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai yi irin abubuwan banmamaki haka?” Sai raʼayinsu ya sha bamban.


Yohanna 9:24
Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka ɗaukaka Allah, mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”


Yohanna 9:29
Mun dai san cewa Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum ba mu san inda ya fito ba.”


Yohanna 9:31
Mun san cewa Allah ba ya sauraron masu zunubi. Yakan saurari mai tsoronsa mai aikata nufinsa.


Yohanna 9:33
Da mutumin nan ba daga Allah ba ne, da ba abin da zai iya yi.”


Yohanna 10:33
Sai Yahudawa suka ce, “Ba don wani daga cikin waɗannan muke so mu jajjefe ka ba, sai don saɓo, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.”


Yohanna 10:35
In har ya kira su ‘alloli’, waɗanda maganar Allah ta zo musu-Nassi ba zai karyuwa ba— 


Yohanna 10:36
me za ku ce game da wanda Allah ya keɓe wa kansa ya kuma aiko duniya? Don me kuke zargi na a kan saɓo, don na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’


Yohanna 11:4
Saʼad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. Aʼa, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan.”


Yohanna 11:22
Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.”


Yohanna 11:27
Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”


Yohanna 11:40
Sai Yesu ya ce, “Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?”


Yohanna 11:52
ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yǎ tattaro ʼyaʼyan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya.


Yohanna 12:43
gama sun fi son yabon mutane, fiye da yabon Allah.


Yohanna 13:3
Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah;


Yohanna 13:31
Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa.


Yohanna 13:32
In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikinsa, Allah zai ɗaukaka Ɗan a cikin kansa, zai kuma ɗaukaka shi nan take.


Yohanna 14:1
“Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.


Yohanna 16:2
Za su kore ku daga majamiʼa; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne.


Yohanna 16:27
Ai, shi Uban kansa yana ƙaunarku domin kun ƙaunace ni kun kuma gaskata cewa daga Allah na fito.


Yohanna 16:30
Yanzu mun gane cewa ka san kome ba sai wani ya tambaye ka ba. Wannan ya sa muka gaskata ka fito daga Allah.”


Yohanna 17:3
Rai madawwami kuwa shi ne: su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko.


Yohanna 19:7
Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yǎ mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”


Yohanna 20:17
Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ʼyanʼuwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ”


Yohanna 20:28
Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”


Yohanna 20:31
An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.


Yohanna 21:19
Yesu ya faɗi wannan ne, don yǎ nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yǎ ɗaukaka Allah. Saʼan nan ya ce masa, “Bi ni!”


Ayyukan Manzanni 1:3
Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arbaʼin ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah.


Ayyukan Manzanni 2:5
To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.


Ayyukan Manzanni 2:11
(Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa-mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”


Ayyukan Manzanni 2:17
“Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe, zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane. ʼYaʼyanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayoyi, dattawanku kuma za su yi mafarkai.


Ayyukan Manzanni 2:22
“Mutanen Israʼila, ku saurari wannan: Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin muʼujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.


Ayyukan Manzanni 2:23
An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye.


Ayyukan Manzanni 2:24
Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ʼyantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.


Ayyukan Manzanni 2:30
Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa.


Ayyukan Manzanni 2:32
Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan.


Ayyukan Manzanni 2:33
An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji.


Ayyukan Manzanni 2:36
“Saboda haka bari dukan Israʼila su tabbatar da wannan: Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”


Ayyukan Manzanni 2:39
Alkawarin dominku ne da ʼyaʼyanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa-domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”


Ayyukan Manzanni 2:47
suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.


Ayyukan Manzanni 3:8
Sai ya yi wuf da ƙafafunsa ya fara tafiya. Ya tafi tare da su ya shiga cikin filayen haikali yana tafiya yana tsalle, yana kuma yabon Allah.


Ayyukan Manzanni 3:9
Saʼad da dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana yabon Allah,


Ayyukan Manzanni 3:13
Allah na Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub, Allah na kakanninmu, ya ɗaukaka bawansa Yesu. Ku kuka ba da shi domin a kashe, kuka yi mūsun saninsa a gaban Bilatus, ko da yake ya yi niyya ya sake shi.


Ayyukan Manzanni 3:15
Kuka kashe tushen rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu. Mu shaidu ne ga wannan.


Ayyukan Manzanni 3:18
Amma ta haka ne Allah ya cika abin da ya rigyafaɗi ta bakin dukan annabawa, cewa, Kiristinsa zai sha wahala.


Ayyukan Manzanni 3:19
Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokatan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji,


Ayyukan Manzanni 3:21
Dole ya kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki.


Ayyukan Manzanni 3:22
Gama Musa ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai tasar muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku; dole ku saurari duk abin da ya faɗa muku.


Ayyukan Manzanni 3:25
Ku kuwa magādan annabawan ne da kuma na alkawarin da Allah ya yi da kakanninku. Ya ce wa Ibrahim, ‘Ta wurin zuriyarka, dukan kabilan duniya za su sami albarka.’


Ayyukan Manzanni 3:26
Da Allah ya tashe bawansa, ya aike shi da fari zuwa gare ku don ya albarkace ku ta wurin juye kowannenku daga mugayen hanyoyinku.”


Ayyukan Manzanni 4:10
to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Israʼila cewa: Da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye.


Ayyukan Manzanni 4:19
Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shariʼanta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah.


Ayyukan Manzanni 4:21
Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.


Ayyukan Manzanni 4:24
Saʼad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin adduʼa ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu.


Ayyukan Manzanni 4:31
Bayan suka yi adduʼa, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka ciku da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro.


Ayyukan Manzanni 5:4
Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”


Ayyukan Manzanni 5:29
Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce: “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!


Ayyukan Manzanni 5:30
Allahn kakanninmu ya ta da Yesu daga matattu-wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace.


Ayyukan Manzanni 5:31
Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don ya kawo tuba da gafarar zunubai ga Israʼila.


Ayyukan Manzanni 5:32
Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.”


Ayyukan Manzanni 5:39
Amma in daga Allah ne, ba za ku iya hana waɗannan mutane ba, za ku dai sami kanku kuna gāba da Allah ne.”


Ayyukan Manzanni 6:2
Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba.


Ayyukan Manzanni 6:4
mu kuwa mu mai da halinmu ga yin adduʼa da kuma hidimar maganar Allah.”


Ayyukan Manzanni 6:7
Saboda haka maganar Allah ta yaɗu. Yawan almajirai a Urushalima kuwa ya yi saurin ƙaruwa, firistoci masu yawa kuma suka zama masu biyayya ga wannan bangaskiya.


Ayyukan Manzanni 6:8
To, Istifanus, mutum cike da alheri da ikon Allah, ya aikata manyan ayyukan da alamu masu banmamaki a cikin mutane.


Ayyukan Manzanni 6:11
Saʼan nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”


Ayyukan Manzanni 7:2
Game da wannan ya amsa, ya ce: “ʼYanʼuwa da ubanni, ku saurare ni! Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim yayinda yake a ƙasar Mesofotamiya tukuna, kafin ya yi zama a Haran.


Ayyukan Manzanni 7:3
Allah ya ce, ‘Ka bar ƙasarka da kuma mutanenka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.’


Ayyukan Manzanni 7:4
“Saboda haka ya bar ƙasar Kaldiyawa ya kuma yi zama a Haran. Bayan mutuwar mahaifinsa, Allah ya aikar da shi wannan ƙasar da yanzu kuke zama.


Ayyukan Manzanni 7:5
Bai ba shi gādo a nan ba, ko taki ɗaya na ƙasa. Amma Allah ya yi masa alkawari cewa shi da zuriyarsa masu zuwa bayansa za su mallaki ƙasar, ko da yake a lokacin Ibrahim ba shi da yaro.


Ayyukan Manzanni 7:6
Allah ya yi magana da shi ta haka: ‘Zuriyarka za su yi baƙunci a wata ƙasar da ba tasu ba, za su yi bauta su kuma sha wulaƙanci har shekara ɗari huɗu.


Ayyukan Manzanni 7:7
Amma zan hore ƙasar da suka bauta wa.’ Allah ya ce, ‘kuma daga baya za su fita daga wannan ƙasa su kuma yi mini sujada a wannan wuri.’


Ayyukan Manzanni 7:9
“Domin kakanninmu sun ji kishin Yusuf, sai suka sayar da shi bawa zuwa Masar. Amma Allah ya kasance tare da shi


Ayyukan Manzanni 7:17
“Da lokaci ya yi kusa da Allah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim, sai yawan mutanenmu da suke a Masar ya ƙaru ƙwarai.


Ayyukan Manzanni 7:25
Musa ya yi tsammani mutanensa za su gane cewa, Allah yana amfani da shi don ya cece su, amma ba su gane ba.


Ayyukan Manzanni 7:32
‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.


Ayyukan Manzanni 7:35
“Wannan Musa ɗin da suka ƙi suna cewa, ‘Wa ya mai da kai mai mulki da kuma alƙali?’ Allah da kansa ya aike shi, ta wurin malaʼikan da ya bayyana a gare shi a ɗan itace, yǎ zama mai mulkinsu, da kuma mai cetonsu.


Ayyukan Manzanni 7:37
“Wannan Musa ne ya faɗa wa Israʼilawa cewa, ‘Allah zai aika muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku.’


Ayyukan Manzanni 7:42
Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa, cewa: “ ‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arbaʼin cikin, hamada, Ya gidan Israʼila?


Ayyukan Manzanni 7:43
Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek, da tauraron allahnku Refan, gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada. Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’ gaba da Babilon.


Ayyukan Manzanni 7:44
“Kakanni-kakanninmu suna da Wuri mai tsarki na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani.


Ayyukan Manzanni 7:45
Bayan sun gāji Wuri mai tsarkin nan, kakanninmu a ƙarƙashin jagorancin Yoshuwa suka kawo shi tare da su, lokacin da suka ƙwace ƙasar daga alʼumman da Allah ya kora a idanunsu. Wuri mai tsarki ɗin ya kasance a ƙasar har zamanin Dawuda,


Ayyukan Manzanni 7:46
wanda ya sami tagomashi daga Allah, ya kuma nemi yǎ yi wa Allah na Yaƙub wurin zama.


Ayyukan Manzanni 7:55
Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah.


Ayyukan Manzanni 7:56
Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”


Ayyukan Manzanni 8:2
Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa.


Ayyukan Manzanni 8:10
dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma”


Ayyukan Manzanni 8:12
Amma da suka gaskata da Filibus saʼad da yake waʼazin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata.


Ayyukan Manzanni 8:14
Saʼad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna.


Ayyukan Manzanni 8:20
Bitrus ya amsa, ya ce: “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi!


Ayyukan Manzanni 8:21
Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba.


Ayyukan Manzanni 9:20
Nan take ya fara waʼazi cikin majamiʼu cewa Yesu Ɗan Allah ne.


Ayyukan Manzanni 10:2
Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma adduʼa ga Allah ba fasawa.


Ayyukan Manzanni 10:3
Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani malaʼikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!”


Ayyukan Manzanni 10:4
Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?” Malaʼikan ya ce, “Adduʼoʼinka da kyautayinka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah.


Ayyukan Manzanni 10:15
Muryar ta yi magana da shi sau na biyu ta ce, “Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.”


Ayyukan Manzanni 10:22
Mutanen suka amsa, “Mun zo ne daga wurin Korneliyus wani jarumin. Shi mutum ne mai adalci mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa ke girmamawa. Wani malaʼika mai tsarki ya faɗa masa, yǎ sa ka zo gidansa don ya ji abin da za ka faɗa.”


Ayyukan Manzanni 10:28
Sai ya ce musu: “Ku da kanku kun san cewa dokarmu ta hana Bayahude yin cuɗanya, ko ya ziyarci Baʼalʼumme. Amma Allah ya nuna mini cewa kada in kira wani mutum marar tsarki ko marar tsabta.


Ayyukan Manzanni 10:31
ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji adduʼarka, ya kuma tuna da kyautayinka ga matalauta.


Ayyukan Manzanni 10:33
Saboda haka na aika a zo da kai nan da nan, ya kuma yi kyau da ka zo. To ga mu duka a nan a gaban Allah don mu saurari dukan abin da Ubangiji ya umarce ka ka faɗa mana.”


Ayyukan Manzanni 10:34
Saʼan nan Bitrus ya fara magana ya ce: “Yanzu na gane yadda gaskiya ne cewa Allah ba ya sonkai


Ayyukan Manzanni 10:36
Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Israʼila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa.


Ayyukan Manzanni 10:38
yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga koʼina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.


Ayyukan Manzanni 10:40
amma Allah ya tashe shi daga matattu a rana ta uku, ya sa kuma aka gan shi.


Ayyukan Manzanni 10:41
Ba dukan mutane ne suka gan shi ba, amma ta wurin shaidun da Allah ya riga ya zaɓa— ta wurin mu da muka ci muka kuma sha tare da shi bayan tashinsa daga matattu.


Ayyukan Manzanni 10:42
Ya umarce mu mu yi waʼazi ga mutane mu kuma shaida cewa shi ne wanda Allah ya naɗa yǎ zama mai shariʼa na masu rai da na matattu.


Ayyukan Manzanni 10:46
Gama sun ji su suna magana da waɗansu harsuna suna kuma yabon Allah. Sai Bitrus ya ce,


Ayyukan Manzanni 11:1
Manzanni da ʼyanʼuwa koʼina a Yahudiya suka ji cewa Alʼummai ma sun karɓi maganar Allah.


Ayyukan Manzanni 11:9
“Sai muryar daga sama ta yi magana sau na biyu, ta ce, ‘Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.’


Ayyukan Manzanni 11:17
To, in Allah ya ba su kyauta yadda ya ba mu, mu da muka gaskata da Ubangiji Yesu Kiristi, wane ni da zan yi hamayya da Allah?”


Ayyukan Manzanni 11:18
Saʼad da suka ji haka, ba su ƙara yin faɗa ba, suka kuma ɗaukaka Allah, suna cewa, “To fa, har Alʼummai ma Allah ya da tuba zuwa rai.”


Ayyukan Manzanni 11:23
Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu.


Ayyukan Manzanni 12:5
Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da adduʼa ga Allah dominsa.


Ayyukan Manzanni 12:22
Suka ta da murya suka ce, “Wannan muryar wani allah ne, ba ta mutum ba.”


Ayyukan Manzanni 12:23
Nan take, domin Hirudus bai yi wa Allah yabo ba, wani malaʼikan Ubangiji ya buge shi, tsutsotsi kuwa suka cinye shi ya kuma mutu.


Ayyukan Manzanni 12:24
Amma maganar Allah ta ci gaba da ƙaruwa ta kuma bazu.


Ayyukan Manzanni 13:5
Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majamiʼun Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu.


Ayyukan Manzanni 13:7
wanda yake maʼaikacin muƙaddas Sergiyus Faulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawul domin yana so ya ji maganar Allah.


Ayyukan Manzanni 13:16
Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce: “Mutanen Israʼila da kuma ku Alʼummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni!


Ayyukan Manzanni 13:17
Allahn mutanen Israʼila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar,


Ayyukan Manzanni 13:20
Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450. “Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Samaʼila.


Ayyukan Manzanni 13:21
Saʼan nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawul ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arbaʼin.


Ayyukan Manzanni 13:23
“Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Israʼila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari.


Ayyukan Manzanni 13:26
“Ya ku ʼyanʼuwa, ʼyaʼyan Ibrahim, da ku kuma Alʼummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto.


Ayyukan Manzanni 13:30
Amma Allah ya tashe shi daga matattu,


Ayyukan Manzanni 13:32
“Muna gaya muku labari mai daɗi cewa: Abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari,


Ayyukan Manzanni 13:34
Gaskiyar cewa Allah ya ta da shi daga matattu, a kan ba zai taɓa ruɓewa ba, an faɗe shi a cikin waɗannan kalmomi: “ ‘Zan ba ku tsarki da kuma tabbatattun albarkun da na yi wa Dawuda alkawari.’


Ayyukan Manzanni 13:36
“Gama saʼad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe.


Ayyukan Manzanni 13:37
Amma wanda Allah ya ta da daga matattu bai ruɓa ba.


Ayyukan Manzanni 13:43
Da aka sallami jamaʼa, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah.


Ayyukan Manzanni 13:46
Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagaɗi: suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Alʼummai.


Ayyukan Manzanni 13:47
Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa: “ ‘Na sa ka zama haske ga Alʼummai, domin ka kawo ceto har zuwa iyakar duniya.’ ”


Ayyukan Manzanni 13:50
Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka ta da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu.


Ayyukan Manzanni 14:15
“Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ʼyan adam ne kamarku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu.


Ayyukan Manzanni 14:22
suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”


Ayyukan Manzanni 14:26
Daga Attaliya kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antiyok, inda dā aka danƙa su ga alherin Allah saboda aikin da suka kammala yanzu.


Ayyukan Manzanni 14:27
Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Alʼummai.


Ayyukan Manzanni 15:4
Saʼad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu.


Ayyukan Manzanni 15:7
Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi, ya ce: “ʼYanʼuwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Alʼummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.


Ayyukan Manzanni 15:8
Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.


Ayyukan Manzanni 15:10
To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba?


Ayyukan Manzanni 15:12
Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Alʼummai ta wurinsu.


Ayyukan Manzanni 15:14
Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Alʼummai su zama nasa.


Ayyukan Manzanni 15:19
“Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Alʼummai waɗanda suke juyowa ga Allah.


Ayyukan Manzanni 16:10
Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu waʼazin bishara.


Ayyukan Manzanni 16:14
Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yardunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus.


Ayyukan Manzanni 16:17
Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.”


Ayyukan Manzanni 16:25
Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna adduʼa suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ʼyan kurkuku kuwa suna sauraronsu.


Ayyukan Manzanni 16:34
Sai mai gadin kurkukun ya kawo su cikin gidansa ya ba su abinci; ya kuwa cika da murna don ya gaskata da Allah-shi da dukan iyalinsa.


Ayyukan Manzanni 17:4
Waɗansu Yahudawa suka amince suka kuma bi Bulus da Sila, haka ma Helenawa da yawa masu tsoron Allah da kuma manyan mata ba kaɗan ba.


Ayyukan Manzanni 17:13
Da Yahudawan da suke a Tassalonika suka ji cewa Bulus yana waʼazin maganar Allah a Bereya, sai suka je can ma, suna zuga taro suna kuma ta da hankalinsu.


Ayyukan Manzanni 17:17
Saboda haka ya yi ta muhawwara a majamiʼa da Yahudawa da kuma Helenawa masu tsoron Allah, haka kuma da waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa.


Ayyukan Manzanni 17:23
Gama saʼad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu: ‘GA ALLAHN DA BA A SANI BA.’ To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku.


Ayyukan Manzanni 17:24
“Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa.


Ayyukan Manzanni 17:27
Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu.


Ayyukan Manzanni 17:29
“Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse-siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa.


Ayyukan Manzanni 17:30
A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a koʼina su tuba.


Ayyukan Manzanni 18:7
Sai Bulus ya bar majamiʼar ya kuma tafi ƙofar da take kusa da gidan Titiyus Yustus, mai yi wa Allah sujada.


Ayyukan Manzanni 18:11
Saboda haka Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da rabi, yana koya musu maganar Allah.


Ayyukan Manzanni 18:13
Suka yi zarge cewa, “Wannan mutum yana rarrashin mutane su yi wa Allah sujada a hanyoyin da suka saɓa wa doka.”


Ayyukan Manzanni 18:21
Amma da yake barin wurin, ya yi alkawari cewa, “Zan dawo in Allah ya yarda.” Saʼan nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.


Ayyukan Manzanni 18:26
Sai ya fara magana gabagaɗi a majamiʼa. Saʼad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.


Ayyukan Manzanni 19:8
Bulus ya shiga majamiʼa ya yi magana gabagaɗi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah.


Ayyukan Manzanni 19:11
Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus,


Ayyukan Manzanni 20:21
Na yi shela ga Yahudawa da Helenawa cewa dole juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.


Ayyukan Manzanni 20:24
Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni-aikin shaida bisharar alherin Allah.


Ayyukan Manzanni 20:25
“Yanzu na san cewa ba ko ɗaya daga cikinku wanda na zazzaga ina muku waʼazin mulkin Allah da zai sāke ganina.


Ayyukan Manzanni 20:27
Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba.


Ayyukan Manzanni 20:28
Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.


Ayyukan Manzanni 20:32
“To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za ta iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake.


Ayyukan Manzanni 21:19
Bulus ya gaishe su ya kuma ba su rahoto dalla-dalla a kan abin da Allah ya yi a cikin Alʼummai ta wurin aikinsa.


Ayyukan Manzanni 21:20
Da suka ji haka, sai suka yabi Allah. Saʼan nan suka ce wa Bulus: “Ka gani ɗanʼuwa, yawan dubban Yahudawan da suka gaskata, kuma dukansu masu himma ne a wajen bin doka.


Ayyukan Manzanni 22:3
“Ni Bayahude ne haifaffen Tarsus na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau.


Ayyukan Manzanni 22:14
“Saʼan nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa.


Ayyukan Manzanni 23:1
Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “ʼYanʼuwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yǎ zuwa yau.”


Ayyukan Manzanni 23:3
Sai Bulus ya ce masa, “Allah zai buge ka, kai farin bango! Ka zauna a can kana hukunta ni bisa ga doka, ga shi kai kanka kana ƙetare dokar ta wurin ba da umarni a buge ni!”


Ayyukan Manzanni 23:4
Waɗanda suke tsaye kusa da Bulus kuwa suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”


Ayyukan Manzanni 24:14
Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa,


Ayyukan Manzanni 24:15
ina kuma da irin bege ɗaya ga Allah yadda mutanen nan suke da shi, cewa akwai tashin matattu masu adalci da masu mugunta duka.


Ayyukan Manzanni 24:16
Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane.


Ayyukan Manzanni 26:6
Yanzu kuwa saboda begena cikin abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari ne, ake mini shariʼa yau.


Ayyukan Manzanni 26:7
Wannan shi ne alkawarin da kabilanmu goma sha biyu suke bege su ga cikawarsa, yayinda suke bauta wa Allah da himma dare da rana. Ya Sarki, saboda wannan bege ne fa Yahudawa suke zargena.


Ayyukan Manzanni 26:8
Don me wani a cikinku zai yi shakka cewa Allah yana ta da matattu?


Ayyukan Manzanni 26:18
ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’


Ayyukan Manzanni 26:20
Da farko ga waɗanda suke a Damaskus, saʼan nan ga waɗanda suke a Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya, da kuma ga Alʼummai su ma, na yi waʼazi don su tuba su juyo ga Allah su kuma tabbatar da tubansu ta wurin ayyukansu.


Ayyukan Manzanni 26:22
Amma na sami taimakon Allah har yǎ zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru— 


Ayyukan Manzanni 26:29
Bulus ya amsa, ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa-ina adduʼa ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.”


Ayyukan Manzanni 27:23
Jiya da dare wani malaʼikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni


Ayyukan Manzanni 27:24
ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lalle za ka tsaya a gaban Kaisar a yi maka shariʼa; Allah kuma cikin alherinsa ya ba ka dukan rayukan mutanen da suke tafiya tare da kai.’


Ayyukan Manzanni 27:25
Saboda haka ku yi ƙarfin hali, ku jamaʼa, gama gaskata Allah a kan cewa yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka zai faru.


Ayyukan Manzanni 27:35
Bayan da ya faɗi haka, sai ya ɗauki burodi ya yi godiya ga Allah a gabansu duka. Saʼan nan ya gutsuttsura ya fara ci.


Ayyukan Manzanni 28:6
Mutanen kuma suka yi zato zai kumbura ko kuma nan da nan zai fāɗi matacce, amma da aka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke raʼayi suka ce shi wani allah ne.


Ayyukan Manzanni 28:15
ʼYanʼuwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa.


Ayyukan Manzanni 28:23
Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yi musu bayyani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa.


Ayyukan Manzanni 28:28
“Saboda haka na so ku san cewa an aika da ceton Allah ga Alʼummai, za su kuwa saurara!”


Ayyukan Manzanni 28:31
Gabagaɗi ba tare da wani hani ba, ya yi waʼazin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi.


Romawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, bawan Kiristi Yesu, kirayaye yǎ zama manzo keɓaɓɓe kuma domin bisharar Allah— 


Romawa 1:2
bisharar da Allah ya yi alkawari tuntuni ta bakin annabawansa a cikin Nassosi Masu Tsarki


Romawa 1:4
wanda bisa ga Ruhun tsarki, aka shaida shi da iko cewa shi Ɗan Allah ta wurin tashinsa daga matattu. Wannan bishara kuwa game da Yesu Kiristi Ubangijinmu ne.


Romawa 1:7
Wannan wasiƙa ce zuwa ga dukanku da kuke a Roma waɗanda Allah yake ƙauna, waɗanda kuma ya kira domin su zama tsarkaka: Alheri da salama gare ku daga Allah Ubanmu da kuma daga Ubangiji Yesu Kiristi.


Romawa 1:8
Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a koʼina a duniya.


Romawa 1:9
Allah, wanda nake bauta wa da dukan zuciyata cikin waʼazin bisharar Ɗansa, shi ne shaidata a kan yadda kullum ina tunawa da ku


Romawa 1:10
cikin adduʼoʼina a kowane lokaci; ina kuma adduʼa cewa a ƙarshe in Allah ya yarda hanya za ta buɗe mini in zo wurinku.


Romawa 1:16
Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata: da farko ga Yahudawa, saʼan nan ga Alʼummai.


Romawa 1:17
Gama a cikin bishara an bayyana adalci daga Allah wanda yake ta wurin bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”


Romawa 1:18
Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu,


Romawa 1:19
gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi.


Romawa 1:20
Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa-madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa-ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.


Romawa 1:21
Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta.


Romawa 1:23
suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.


Romawa 1:24
Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen shaʼawace shaʼawacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya.


Romawa 1:25
Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci-wanda ake yabo har abada. Amin.


Romawa 1:26
Saboda wannan, Allah ya yashe su ga shaʼawace-shaʼawacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ʼyanʼuwansu mata wadda ba daidai ba.


Romawa 1:28
Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba.


Romawa 1:30
da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girmankai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu;


Romawa 1:32
Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.


Romawa 2:2
Yanzu mun san cewa hukuncin Allah a kan masu aikata waɗannan abubuwa daidai ne.


Romawa 2:3
Saboda haka saʼad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne?


Romawa 2:4
Ko kuma kana rena wadatar alherinsa, haƙurinsa, da kuma jimrewarsa ne ba tare da sanin cewa alherin Allah yana kai ka ga tuba ba ne?


Romawa 2:5
Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, saʼad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci.


Romawa 2:6
Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.”


Romawa 2:11
Gama Allah ba ya nuna bambanci.


Romawa 2:13
Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma waɗanda suke yin biyayya da dokar, su za a ce da su masu adalci.


Romawa 2:16
Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shariʼanta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.


Romawa 2:17
To, kai, da kake kiran kanka Bayahude; in kana dogara ga doka kana kuma taƙama da dangantakarka da Allah;


Romawa 2:23
Kai da kake taƙama da doka, kana nuna rashin bangirma ga Allah ta wurin karya dokar?


Romawa 2:24
Kamar yadda yake a rubuce: “Ana saɓon sunan Allah a cikin Alʼummai saboda ku.”


Romawa 2:29
Aʼa, mutum Bayahude ne in shi Bayahude ne a zuci; kuma kaciya ita ce kaciya ta zuci, ta wurin Ruhu, ba ta wurin rubutaccen doka ba. Irin wannan mutum yana samun yabo daga Allah ne, ba ɗan adam ba.


Romawa 3:2
Akwai riba ƙwarai ta kowace hanya! Da farko dai, su ne aka danƙa wa kalmomin nan na Allah.


Romawa 3:3
Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah?


Romawa 3:4
Ko kaɗan! Bari Allah yǎ zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yǎ zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Gama a tabbatar kana da gaskiya, saʼad da ka yi magana, ka kuma yi nasara saʼad da ka yi shariʼa.”


Romawa 3:5
Amma in rashin adalcinmu ya bayyana adalcin Allah a fili, me za mu ce ke nan? Za mu ce Allah ya yi rashin adalci ke nan da ya saukar da fushinsa a kanmu? (Ina magana kamar yadda mutum zai yi ne.)


Romawa 3:6
Sam, ko kusa! Da a ce haka ne, ta yaya Allah zai shariʼanta duniya?


Romawa 3:7
Wani zai iya ce, “In a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka ƙara ɗaukaka shi, to, don yaya zan zama mai zunubi, in ƙaryata tana kawo ɗaukaka ga Allah?”


Romawa 3:11
babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.


Romawa 3:18
“Ba sa tsoron Allah sam.”


Romawa 3:19
Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah.


Romawa 3:20
Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi.


Romawa 3:21
Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci.


Romawa 3:22
Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci,


Romawa 3:23
gama duka su yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah,


Romawa 3:25
Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yǎ nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba— 


Romawa 3:29
Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Alʼummai ba ne? I, shi Allahn Alʼummai ne ma,


Romawa 3:30
da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin.


Romawa 4:2
In fa da gaske ne Ibrahim ya sami kuɓuta ta wurin ayyuka, yana da abin da zai yin taƙama da shi ke nan-amma ba a gaban Allah ba.


Romawa 4:3
Me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne a gare shi.”


Romawa 4:5
Amma fa, game da mutumin da ba ya aiki sai dai dogara ga Allah wanda yake kuɓutar da masu mugunta, akan lissafta bangaskiyarsa a matsayin adalci ne.


Romawa 4:6
Dawuda ya faɗi haka saʼad da ya yi magana game da albarkar da aka yi wa mutumin da Allah ya lissafta adalci a gare shi, ba don ya yi ayyuka ba:


Romawa 4:17
Kamar yadda yake a rubuce cewa: “Na mai da kai uban alʼummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata-Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.


Romawa 4:20
Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah,


Romawa 4:21
yana kuma da cikakken tabbaci cewa Allah yana da iko yǎ cika abin da ya yi alkawari.


Romawa 4:24
amma saboda mu ma, mu da Allah zai lissafta adalci-mu da muka ba da gaskiya gare shi da ya tashe Yesu Ubangijinmu daga matattu.


Romawa 4:25
An miƙa shi ga mutuwa saboda zunubanmu, aka kuma tashe shi zuwa rai saboda Allah zai same mu marasa laifi.


Romawa 5:1
Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi,


Romawa 5:2
ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah.


Romawa 5:5
Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.


Romawa 5:6
Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba.


Romawa 5:8
Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan: Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.


Romawa 5:9
Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa!


Romawa 5:10
Gama in kuwa, saʼad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa!


Romawa 5:11
Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu.


Romawa 5:15
Amma kyautan nan dabam take da laifin nan. Gama in mutane da yawa sun mutu saboda laifin mutum ɗayan nan, to, ai, alherin Allah da kuma kyautan nan mai zuwa ta wurin alherin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi, ya shafi mutane da yawa!


Romawa 5:16
Kyautar Allah kuwa ba kamar sakamakon da ya bi zunubin mutum gudan nan ba ne: Hukuncin ya bi zunubin mutum gudan nan, ya kuma kawo hallaka, amma kyautar ta bi laifofin masu yawa ta kuma sa Allah ya gan mu a matsayin marasa laifi.


Romawa 5:17
Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi.


Romawa 5:18
Saboda haka, kamar yadda sakamakon laifin mutum guda ya jawo hallaka ga dukan mutane, haka ma sakamakon aikin adalci guda ya sa Allah ya same mu marasa laifi, wannan kuwa kawo rai ga dukan mutane.


Romawa 6:10
Mutuwar da ya yi, ya mutu ne sau ɗaya tak, saboda yǎ shafe zunubi, amma rayuwar da yake yi, yana yi ne cikin tarayya da Allah.


Romawa 6:11
Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu.


Romawa 6:13
Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci.


Romawa 6:17
Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku.


Romawa 6:22
Amma a yanzu da aka ʼyantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.


Romawa 6:23
Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.


Romawa 7:4
Saboda haka ʼyanʼuwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah.


Romawa 7:22
Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah;


Romawa 7:25
Godiya ga Allah-ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu! Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.


Romawa 8:3
Gama abin da dokar ba ta iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi saʼad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yǎ zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi.


Romawa 8:7
hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba.


Romawa 8:8
Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.


Romawa 8:9
Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.


Romawa 8:14
domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ʼyaʼyan Allah.


Romawa 8:16
Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ʼyaʼyan Allah ne.


Romawa 8:17
In kuwa mu ʼyaʼya ne, to, mu magāda ne-magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.


Romawa 8:19
Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ʼyaʼyan Allah.


Romawa 8:21
cewa za a ʼyantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ʼyancin ɗaukakar ʼyaʼyan Allah.


Romawa 8:23
Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ʼyaʼyan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.


Romawa 8:27
Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.


Romawa 8:28
Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.


Romawa 8:29
Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yǎ zama ɗan fari cikin ʼyanʼuwa masu yawa.


Romawa 8:31
Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?


Romawa 8:33
Wa zai kawo wani zargi a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Allah ne mai kuɓutarwa.


Romawa 8:34
Wa zai yi hukunci? Yesu Kiristi ne, wanda ya mutu-fiye da haka ma, shi da aka ta da zuwa rai-yana zaune a hannun dama na Allah yana kuma yin roƙo a madadinmu.


Romawa 8:39
ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.


Romawa 9:4
mutanen Israʼila. Su ne Allah ya mai da su ʼyaʼyansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawarai.


Romawa 9:5
Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin.


Romawa 9:6
Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Israʼila ne suke Israʼila na gaske ba.


Romawa 9:8
Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ʼyaʼyan Allah ba, aʼa, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.


Romawa 9:11
Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa:


Romawa 9:14
Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan!


Romawa 9:16
Saboda haka, bai danganta ga shaʼawar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah.


Romawa 9:18
Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.


Romawa 9:19
Waninku zai iya ce mini: “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?”


Romawa 9:20
Amma wane ne kai, Ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ”


Romawa 9:22
Haka ma aikin Allah yake. Ya so yǎ nuna fushinsa yǎ kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa-waɗanda aka shirya domin hallaka?


Romawa 9:26
kuma, “Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba,’ za a ce da su, ‘ʼyaʼyan Allah mai rai.’ ”


Romawa 10:1
ʼYanʼuwa, abin da zuciyata take so da kuma adduʼata ga Allah saboda Israʼilawa shi ne su sami ceto.


Romawa 10:2
Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba.


Romawa 10:3
Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah.


Romawa 10:9
Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya ta da shi daga matattu, za ka sami ceto.


Romawa 11:1
To, ina da tambaya: Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Israʼila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin.


Romawa 11:2
Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Eliya ba-yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Israʼila ya ce:


Romawa 11:4
Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Baʼal sujada ba.”


Romawa 11:8
kamar yadda yake a rubuce cewa: “Allah ya ba su ruhun ruɗewa, idanu don su kāsa gani, da kuma kunnuwa don su kāsa ji, har yǎ zuwa yau.”


Romawa 11:21
Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.


Romawa 11:22
Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah: tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka.


Romawa 11:23
In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su.


Romawa 11:26
Ta haka kuwa za a ceci dukan Israʼila, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Mai ceto zai zo daga Sihiyona; zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.


Romawa 11:29
gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa.


Romawa 11:30
Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu,


Romawa 11:31
haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku.


Romawa 11:32
Gama Allah ya ɗaure dukan mutane ga rashin biyayya don yǎ nuna jinƙai ga kowa.


Romawa 11:33
Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace! Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike, hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!


Romawa 11:35
“Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu, da Allah zai sāka masa?”


Romawa 12:1
Saboda haka, ina roƙonku, ʼyanʼuwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah-wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.


Romawa 12:2
Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake-abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.


Romawa 12:3
Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku: Kada yǎ ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yǎ auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.


Romawa 12:13
Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi.


Romawa 12:19
Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa: “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji.


Romawa 13:1
Dole kowa yǎ yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne.


Romawa 13:2
Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci.


Romawa 13:4
Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi.


Romawa 13:6
Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci.


Romawa 14:3
Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada yǎ rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada yǎ ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi.


Romawa 14:6
Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah.


Romawa 14:10
Kai kuwa, don me kake ganin laifin ɗanʼuwanka? Ko kuma don me kake rena ɗanʼuwanka? Gama duk za mu tsaya a gaban kujerar shariʼar Allah.


Romawa 14:11
A rubuce yake cewa: “ ‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji, ‘kowace gwiwa za ta durƙusa a gabana; kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ ”


Romawa 14:12
Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah.


Romawa 14:17
Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki,


Romawa 14:18
duk kuwa wanda yake bauta wa Kiristi a haka yana faranta wa Allah rai ne, yardajje kuma ga mutane.


Romawa 14:20
Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yǎ ci abin da zai sa wani yǎ yi tuntuɓe.


Romawa 14:22
Bari duk raʼayin da kake da shi game da wannan shaʼani yǎ kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba ta ba shi laifi game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa daidai ne ba.


Romawa 15:5
Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yǎ ba ku ruhun haɗin kai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu,


Romawa 15:6
don da zuciya ɗaya da kuma baki ɗaya kuke ɗaukaka Allah da kuma Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi.


Romawa 15:7
Ta haka sai ku karɓi juna kamar yadda Kiristi ya karɓe ku, don a yabi Allah.


Romawa 15:8
Ina dai gaya muku cewa Kiristi ya zama bawan Yahudawa a madadin gaskiyar Allah, don yǎ tabbatar da alkawaran da aka yi wa kakannin kakanninmu


Romawa 15:9
domin Alʼummai su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa, kamar yadda yake a rubuce: “Saboda haka zan yabe ka a cikin Alʼummai; zan rera waƙoƙi ga sunanka.”


Romawa 15:13
Bari Allah na bege yǎ cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.


Romawa 15:15
Na rubuta muku gabagaɗi a kan waɗansu batuttuwa, don in sāke tuna muku su, saboda alherin da Allah ya ba ni


Romawa 15:16
in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Alʼummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Alʼummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


Romawa 15:17
Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah.


Romawa 15:18
Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Alʼummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata


Romawa 15:30
Ina roƙonku ʼyanʼuwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin adduʼa ga Allah saboda ni.


Romawa 15:32
don da yardar Allah, in iso wurinku da farin ciki in kuma wartsake tare da ku.


Romawa 15:33
Allah na salama yǎ kasance tare da ku duka. Amin.


Romawa 16:20
Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yǎ kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yǎ kasance tare da ku.


Romawa 16:26
amma yanzu kuwa aka bayyana, aka kuma sanar ta wurin rubuce rubucen annabawa bisa ga umarnin Allah madawwami, domin dukan alʼummai su gaskata su kuma yi masa biyayya— 


Romawa 16:27
ɗaukaka ta tabbata har abada ga Allah, wanda shi ne kaɗai mai hikima ta wurin Yesu Kiristi! Amin.


1 Korintiyawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, wanda aka kira domin yǎ zama manzon Kiristi Yesu, bisa ga nufin Allah, da kuma ɗanʼuwanmu Sostenes,


1 Korintiyawa 1:2
Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korinti, da waɗanda aka tsarkake cikin Kiristi Yesu, aka kuma kira domin su zama masu tsarki, tare da dukan waɗanda suke koʼina da suke kiran sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, Ubangijinsu da kuma namu:


1 Korintiyawa 1:3
Alheri da salama zuwa gare ku daga Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Kiristi.


1 Korintiyawa 1:4
Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu.


1 Korintiyawa 1:9
Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.


1 Korintiyawa 1:18
Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne.


1 Korintiyawa 1:20
Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba?


1 Korintiyawa 1:21
Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba ta san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar waʼazin bishara.


1 Korintiyawa 1:24
amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Helenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah.


1 Korintiyawa 1:25
Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.


1 Korintiyawa 1:27
Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don ya kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya.


1 Korintiyawa 1:30
Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu.


1 Korintiyawa 2:1
Da na zo wurinku ʼyanʼuwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba.


1 Korintiyawa 2:5
domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.


1 Korintiyawa 2:7
Aʼa, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai.


1 Korintiyawa 2:9
Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”  —


1 Korintiyawa 2:10
Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa. Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah.


1 Korintiyawa 2:11
Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.


1 Korintiyawa 2:12
Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake.


1 Korintiyawa 2:14
Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.


1 Korintiyawa 3:6
Ni na shuka iri, Afollos kuma ya yi ban ruwa, amma Allah ne ya sa irin ya yi girma.


1 Korintiyawa 3:7
Don haka, da wanda ya yi shuki, da wanda ya yi ban ruwa, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, mai sa abubuwan su yi girma.


1 Korintiyawa 3:9
Gama mu abokan aiki ne na Allah; ku kuwa gonar ce ta Allah, ginin Allah kuma.


1 Korintiyawa 3:10
Ta wurin alherin da Allah ya ba ni, na kafa tushen gini kamar ƙwararren magini, wani kuma dabam yana gini a kai. Amma kowa yǎ lura da yadda yake gini.


1 Korintiyawa 3:16
Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku?


1 Korintiyawa 3:17
Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan.


1 Korintiyawa 3:19
Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”;


1 Korintiyawa 3:23
ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.


1 Korintiyawa 4:1
Saboda haka, ya kamata mutane su ɗauke mu a matsayin bayin Kiristi, da kuma a matsayin waɗanda aka ba su amanar asirin abubuwan Allah.


1 Korintiyawa 4:5
Saboda haka, kada ku shariʼanta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.


1 Korintiyawa 4:9
Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin ƙallo ga dukan duniya, ga malaʼiku da kuma mutane.


1 Korintiyawa 4:20
Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko.


1 Korintiyawa 5:13
Allah zai yi wa waɗanda suke ba ʼyan ikkilisiya ba hukunci. “Ku yi waje da irin mugun mutumin nan daga cikinku.”


1 Korintiyawa 6:9
Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku: Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ʼyan daudu,


1 Korintiyawa 6:10
ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.


1 Korintiyawa 6:11
Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.


1 Korintiyawa 6:13
“An yi abinci domin ciki ne, cikin kuma domin abinci.” Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.


1 Korintiyawa 6:14
Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma.


1 Korintiyawa 6:19
Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne;


1 Korintiyawa 6:20
saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.


1 Korintiyawa 7:7
Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.


1 Korintiyawa 7:15
Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne.


1 Korintiyawa 7:17
Duk da haka, sai kowa yǎ kasance a rayuwar da Ubangiji ya sa shi da kuma wanda Allah ya kira shi. Umarnin da na kafa a dukan ikkilisiyoyi ke nan.


1 Korintiyawa 7:19
Kaciya ba wani abu ba ne, rashin kaciya kuma ba wani abu ba ne. Kiyaye umarnin Allah shi ne muhimmin abu.


1 Korintiyawa 7:20
Ya kamata kowa yǎ kasance a matsayin da yake ciki saʼad da Allah ya kira shi.


1 Korintiyawa 7:24
ʼYanʼuwa, a duk matsayin da mutum yake saʼad da aka kira shi, sai yǎ kasance haka a sabuwar dangantakarsa da Allah.


1 Korintiyawa 7:40
A nawa raʼayi, za ta fi jin daɗi in ta zauna haka-a ganina kuwa ina ba ku shawara ce daga Ruhun Allah da na ce haka.


1 Korintiyawa 8:3
Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi.


1 Korintiyawa 8:4
To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa: Mun san cewa gunki ba kome ba ne a duniya, kuma babu wani Allah sai dai ɗaya.


1 Korintiyawa 8:6
duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.


1 Korintiyawa 8:8
Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.


1 Korintiyawa 9:9
Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi saʼad da yake sussukar hatsi.” Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu saʼad da ya ce haka?


1 Korintiyawa 9:21
Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar, (ko da yake ba ni da ʼyanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar.


1 Korintiyawa 10:5
Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu koʼina a cikin hamada.


1 Korintiyawa 10:13
Ba jarabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.


1 Korintiyawa 10:20
Aʼa, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu.


1 Korintiyawa 10:30
In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?


1 Korintiyawa 10:31
Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.


1 Korintiyawa 10:32
Kada ku sa wani yǎ yi tuntuɓe, ko Bayahude ne, ko Bahelene ko kuma ikkilisiyar Allah— 


1 Korintiyawa 11:3
To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne.


1 Korintiyawa 11:7
Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.


1 Korintiyawa 11:12
Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake.


1 Korintiyawa 11:13
Ku kanku duba mana: Ya yi kyau mace ta yi adduʼa ga Allah da kanta a buɗe?


1 Korintiyawa 11:16
In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata alʼada-haka ma ikkilisiyoyin Allah.


1 Korintiyawa 11:19
Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku.


1 Korintiyawa 11:22
Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? Aʼa, ko kaɗan!


1 Korintiyawa 12:3
Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu laʼananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi.


1 Korintiyawa 12:6
Akwai aiki iri iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.


1 Korintiyawa 12:18
Hakika, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowannensu, kamar yadda yake so su zama.


1 Korintiyawa 12:24
gaɓoɓi masu kyan gani kuwa, ba su bukatar yawan girmamawa. Allah ya harhaɗa jikunanmu yadda gaɓoɓin da ake gani kamar ba su da muhimmanci suna da amfani,


1 Korintiyawa 12:28
A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, saʼan nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, saʼan nan kuma masu magana da harsuna iri iri.


1 Korintiyawa 13:12
Yanzu kam muna ganin abubuwa kamar a madubi sai dai ba sosai ba, amma a ranan nan za mu gani fuska da fuska. Yanzu kam sanina ba cikakke ba ne, amma a ranan nan zan kasance da cikakken sani, kamar dai yadda Allah ya san ni a yanzu.


1 Korintiyawa 14:2
Gama duk wanda yake magana da wani harshe ba da mutane yake magana ba, sai dai da Allah. Hakika, ba wanda yake fahimtarsa; yana faɗin asirai ta wurin ruhu ne.


1 Korintiyawa 14:16
A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, saʼad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba?


1 Korintiyawa 14:18
Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka.


1 Korintiyawa 14:25
asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yǎ yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!”


1 Korintiyawa 14:28
In babu mai fassara, sai mai magana yǎ yi shiru a cikin ikkilisiya, yǎ yi wa kansa magana da kuma Allah.


1 Korintiyawa 14:33
Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka,


1 Korintiyawa 14:36
Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso?


1 Korintiyawa 15:9
Gama ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban kuma isa a kira ni manzo ba, domin na tsananta wa ikkilisiyar Allah.


1 Korintiyawa 15:10
Amma bisa ga alherin Allah, na zama abin da nake, alherinsa zuwa gare ni kuwa bai zama a banza ba. Aʼa, na yi aiki fiye da dukansu, duk da haka, ba ni ba ne, sai dai alherin Allah da yake tare da ni ne.


1 Korintiyawa 15:15
Sai ma ya zama mun zama masu ba da shaidar ƙarya game da Allah ke nan, domin mun shaida game da Allah cewa ya tashe Kiristi daga matattu. Bai tashe Kiristi ba ke nan, in lalle ba a ta da matattu.


1 Korintiyawa 15:24
Saʼan nan sai ƙarshen ta zo, saʼad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko.


1 Korintiyawa 15:27
Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi.


1 Korintiyawa 15:28
Saʼad da ya yi haka, saʼan nan Ɗan kansa yǎ koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yǎ zama kome da kome.


1 Korintiyawa 15:34
Ku koma cikin hankalinku yadda ya kamata, ku kuma daina yin zunubi, gama akwai waɗansu da ba su san Allah ba--na faɗi wannan ne don ku kunyata.


1 Korintiyawa 15:38
Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta.


1 Korintiyawa 15:50
Ina sanar da ku, ʼyanʼuwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba.


1 Korintiyawa 15:57
Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.


1 Korintiyawa 16:1
To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa.


2 Korintiyawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti, ɗanʼuwanmu, Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korinti, tare da dukan tsarkaka a koʼina a Akayya:


2 Korintiyawa 1:2
Alheri da salama gare ku, daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


2 Korintiyawa 1:3
Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan taʼaziyya,


2 Korintiyawa 1:4
wanda yakan yi mana taʼaziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya taʼazantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da taʼaziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.


2 Korintiyawa 1:9
Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake ta da matattu.


2 Korintiyawa 1:12
Wannan shi ne taƙamarmu: Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba.


2 Korintiyawa 1:18
Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “Aʼa” ba ce.


2 Korintiyawa 1:19
Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku waʼazinsa, ai, ba “I” da “Aʼa” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.


2 Korintiyawa 1:20
Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.


2 Korintiyawa 1:21
Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu,


2 Korintiyawa 1:23
Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korinti ba.


2 Korintiyawa 2:14
Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a koʼina.


2 Korintiyawa 2:15
Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka.


2 Korintiyawa 2:17
Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.


2 Korintiyawa 3:3
Kun nuna cewa ku wasiƙa ce daga Kiristi, sakamakon hidimarmu, ba wadda aka rubuta da inki ba, sai dai da Ruhun Allah mai rai. Ba kuma a kan allunan dutse ba, sai dai a kan allunan zukatan mutane.


2 Korintiyawa 3:4
Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah.


2 Korintiyawa 3:5
Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne.


2 Korintiyawa 4:1
Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba.


2 Korintiyawa 4:2
Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.


2 Korintiyawa 4:4
Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah.


2 Korintiyawa 4:6
Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yǎ haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yǎ ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.


2 Korintiyawa 4:7
Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba.


2 Korintiyawa 4:15
Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yǎ zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.


2 Korintiyawa 5:1
Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba.


2 Korintiyawa 5:5
Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.


2 Korintiyawa 5:11
To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku.


2 Korintiyawa 5:13
In hankalinmu a taɓe yake, ai, saboda Allah ne, in kuwa cikin hankalinmu muke, ai, saboda ku ne.


2 Korintiyawa 5:18
Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu:


2 Korintiyawa 5:19
wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu.


2 Korintiyawa 5:20
Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi: Ku sulhuntu da Allah.


2 Korintiyawa 5:21
Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


2 Korintiyawa 6:1
A matsayinmu na abokan aikin Allah muna roƙonku kada ku karɓi alherin Allah a banza.


2 Korintiyawa 6:2
Gama ya ce, “A lokacin samun alherina, na ji ka, a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.” Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto.


2 Korintiyawa 6:4
A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da masifu,


2 Korintiyawa 6:7
da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah, muna riƙe da makaman adalci dama da hagu,


2 Korintiyawa 6:16
Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce: “Zan zauna tare da su, in yi tafiya a cikinsu, zan zama Allahnsu, su kuma su zama mutanena.”


2 Korintiyawa 7:1
Da yake muna da waɗannan alkawarai, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.


2 Korintiyawa 7:6
Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai taʼaziyya ya yi mana taʼaziyya da zuwan Titus,


2 Korintiyawa 7:9
Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba.


2 Korintiyawa 7:10
Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa.


2 Korintiyawa 7:11
Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana: ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan shaʼani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.


2 Korintiyawa 7:12
To, ko da yake na rubuto muku, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana.


2 Korintiyawa 8:1
To, ʼyanʼuwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya.


2 Korintiyawa 8:5
Ba su yi yadda muka zata ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, saʼan nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah.


2 Korintiyawa 8:16
Ina gode wa Allah, wanda ya sa a zuciyar Titus, irin kula da nake da shi dominku.


2 Korintiyawa 9:7
Ya kamata kowa yǎ bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba: gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.


2 Korintiyawa 9:8
Allah kuwa yana da iko yǎ ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.


2 Korintiyawa 9:11
Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za ta zama sanadin godiya ga Allah.


2 Korintiyawa 9:12
Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah.


2 Korintiyawa 9:13
Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi naʼam da bisharar Kiristi, saboda kuma gudunmawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.


2 Korintiyawa 9:14
A cikin adduʼarsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku.


2 Korintiyawa 9:15
Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!


2 Korintiyawa 10:4
Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi.


2 Korintiyawa 10:5
Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi.


2 Korintiyawa 10:13
Amma mu kam, ba za mu yi taƙama mu zarce iyakarmu ba, sai dai za mu yi taƙama cikin filin da Allah ya ƙayyade mana, filin kuwa ya kai har zuwa wurinku.


2 Korintiyawa 11:2
Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa tsantsa.


2 Korintiyawa 11:7
Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku waʼazin bisharar Allah kyauta?


2 Korintiyawa 11:11
Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku!


2 Korintiyawa 11:31
Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba.


2 Korintiyawa 12:2
Na san wani a cikin Kiristi wanda shekaru goma sha huɗu da suka wuce an ɗauke zuwa sama ta uku. Ko a cikin jiki ne, ko kuwa ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, Allah ne ya sani.


2 Korintiyawa 12:3
Na kuma san cewa wannan mutum, ko a cikin jiki ne, ko kuma ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, amma Allah ne ya sani,


2 Korintiyawa 12:19
Ko tun dā can, kuna tsammani muna kāre kanmu a gare ku ne? A gaban Allah muke magana, kamar waɗanda suke cikin Kiristi. Ƙaunatattuna, kome da muke yi, muna yi ne don inganta ku ne.


2 Korintiyawa 12:21
Ina tsoro kada saʼad da na sāke zuwa, Allahna zai ƙasƙantar da ni a gabanku, kuma in yi baƙin ciki saboda waɗanda suka yi zunubi a dā, ba su kuma tuba daga aikin ƙazanta, da na fasikanci, da kuma lalata da suka sa kansu a ciki ba.


2 Korintiyawa 13:4
Ko da yake tabbatacce an gicciye shi cikin rashin ƙarfi, duk da haka, yana rayuwa bisa ga ikon Allah. Haka mu ma marasa ƙarfi ne a cikinsa, amma ta wurin ikon Allah za mu rayu tare da shi don mu yi muku hidima.


2 Korintiyawa 13:7
Muna adduʼa ga Allah kada ku aikata wani laifi: Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, aʼa, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne.


2 Korintiyawa 13:11
A ƙarshe ʼyanʼuwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.


2 Korintiyawa 13:14
Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.


Galatiyawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus manzo-aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da Allah Uba, wanda ya ta da shi daga matattu— 


Galatiyawa 1:3
Alheri da salama zuwa gare ku daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi,


Galatiyawa 1:4
wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yǎ cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah da kuma Ubanmu,


Galatiyawa 1:10
Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko na Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba.


Galatiyawa 1:13
Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta.


Galatiyawa 1:15
Amma saʼad da Allah, wanda ya keɓe ni daga haihuwa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi


Galatiyawa 1:20
Ina tabbatar muku a gaban Allah cewa abin da nake rubuta muku ba ƙarya ba ne.


Galatiyawa 1:24
Sai suka yabi Allah saboda ni.


Galatiyawa 2:6
Game da waɗanda kuma aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne-ko su wane ne, ai, duk ɗaya ne a wurina; domin Allah ba ya tāra-ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙare ni da kome ba.


Galatiyawa 2:8
Gama Allah wanda ya yi aiki cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Alʼummai.


Galatiyawa 2:17
“In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Almasihu, saʼan nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Almasihu yana ƙarfafa zunubi ke nan? Aʼa, ko kusa!


Galatiyawa 2:19
Gama ta wurin Doka na mutu ga Doka saboda in rayu ga Allah.


Galatiyawa 2:20
An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne kuma nake raye ba, sai dai Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.


Galatiyawa 2:21
Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!”


Galatiyawa 3:5
Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne?


Galatiyawa 3:6
Ku dubi Ibrahim mana: “Ya gaskata Allah, aka kuwa lissafta wannan adalci ne a gare shi.”


Galatiyawa 3:8
Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Alʼummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yǎ yi cewa, “Dukan alʼummai za su sami albarka ta wurinka.”


Galatiyawa 3:11
A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”


Galatiyawa 3:17
Abin da nake nufi shi ne: Dokar da aka shigar bayan shekaru 430, ba ta kawar da alkawarin da Allah ya riga ya kafa ba, har da zai kawar da alkawarin.


Galatiyawa 3:18
Gama da a ce gādon ya dangana a kan doka ne, to, da ba zai dangana a kan alkawari ba; amma Allah cikin alherinsa ya ba wa Ibrahim gādon ta wurin alkawari.


Galatiyawa 3:20
Matsakanci fa ba domin ɗaya ba ne. Amma Allah ɗaya yake.


Galatiyawa 3:21
To, Dokar ce tana gāba da alkawaran Allah ke nan? Sam, ko kaɗan! Gama da a ce an ba da Dokar da tana iya ba da rai, hakika, da sai a sami adalci ta wurin Doka.


Galatiyawa 3:26
Dukanku ʼyaʼyan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu,


Galatiyawa 4:4
Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,


Galatiyawa 4:6
Domin ku ʼyaʼya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake yin kira, “Abba, Uba.”


Galatiyawa 4:7
Saboda haka kai ba bawa ba ne, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.


Galatiyawa 4:8
Dā saʼad da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda bisa ga ainihi ba alloli ba ne.


Galatiyawa 4:9
Amma yanzu da kuka san Allah-ko kuma a ce Allah ya san ku-ta yaya kuke sāke komawa ga ƙaʼidodi marasa ƙarfi abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu?


Galatiyawa 4:14
Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce malaʼikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.


Galatiyawa 5:21
da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.


Galatiyawa 6:7
Kada a ruɗe ku: Ba a yi wa Allah baʼa. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne.


Galatiyawa 6:16
Salama da jinƙai su tabbata ga dukan waɗanda suke bin wannan ƙaʼida, har ma ga Israʼila na Allah.


Afisawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yǎ zama manzon Kiristi Yesu. Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da suke amintattu cikin Kiristi Yesu:


Afisawa 1:2
Bari alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi su kasance tare da ku.


Afisawa 1:3
Yabo ya tabbata ga Allah da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama.


Afisawa 1:4
Tun dā can, kafin ma a halicci duniya Allah ya zaɓe mu a cikin Kiristi don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa.


Afisawa 1:6
Don haka muna yabon Allah saboda alherin da ya yi mana domin mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.


Afisawa 1:7
Ta wurin mutuwar Kiristi ne muka sami ʼyanci, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah


Afisawa 1:9
Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yǎ cika ta wurin Kiristi.


Afisawa 1:10
Saʼan nan da lokaci ya yi, Allah zai yi duk abin da ya shirya, kuma Kiristi zai kawo kome da yake a sama da ƙasa a ƙarƙashin ikonsa.


Afisawa 1:11
Saboda Kiristi ne muka sami gādo daga Allah, gama ya zaɓe mu daga farko, kome kuma ya faru yadda ya shirya tuntuni.


Afisawa 1:12
Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi ne, za mu yabi ɗaukakar Allah.


Afisawa 1:13
Kiristi ya kawo muku gaskiya, wadda take labari mai daɗi game da yadda za ku sami ceto. Kun sa bangaskiyarku a cikin Kiristi aka kuwa yi muku alkawarin Ruhu Mai Tsarki don a nuna ku na Allah ne.


Afisawa 1:14
Ruhu Mai Tsarki shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari kuma cewa mu mallakarsa ce. Wannan shi ne wani dalilin da za mu yabi Allahnmu mai ɗaukaka.


Afisawa 1:17
Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai ɗaukaka, yǎ ba ku Ruhunsa. Ruhun kuwa zai ba ku hikima yǎ kuma sa ku gane abin da ake nufi da sanin Allah.


Afisawa 1:18
Ina kuma adduʼa cewa zuciyarku ta waye don ku gane begen da aka ba ku saʼad da Allah ya zaɓe ku. Saʼan nan ne za ku gane albarku masu ɗaukakan da za su zama naku tare da dukan tsarkaka.


Afisawa 1:19
Ina so ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali wanda yake namu. Da wannan ikon nan mai girma ne


Afisawa 1:22
Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi wannan iko a kan kome don amfanin ikkilisiya.


Afisawa 2:2
Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya da Shaiɗan, wannan mai mulkin sararin sama. Shi ne ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙi biyayya ga Allah.


Afisawa 2:3
Dukanmu mun yi irin rayuwan nan a dā, muna bin kwaɗayi da shaʼawace shaʼawacen jikunanmu da tunaninmu. Mun ba wa Allah haushi, kuma dā za a hukunta mu kamar sauran mutane.


Afisawa 2:4
Amma saboda yawan ƙaunar da yake yi mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai,


Afisawa 2:5
ya ba mu rai saʼad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.


Afisawa 2:6
Allah ya tashe mu tare da Kiristi ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya.


Afisawa 2:7
Allah ya yi haka domin a zamanai masu zuwa yǎ yi amfani da mu a matsayin yalwar alherinsa da ya wuce misali, yadda yake a dukan abin da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu.


Afisawa 2:8
Allah ya cece ku ta wurin alheri saʼad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yin ku ba ne, kyauta ce daga Allah.


Afisawa 2:10
Allah ya shirya mana mu yi abubuwa masu kyau mu kuma yi rayuwa kamar yadda kullum yake so mu yi. Shi ya sa ya aiko da Kiristi yǎ sa mu zama abin da muke.


Afisawa 2:12
A lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Israʼila, kuma ba ku da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah.


Afisawa 2:16
A kan gicciye Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo salama tsakaninmu da Allah.


Afisawa 2:19
Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ʼyan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma.


Afisawa 2:22
Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.


Afisawa 3:2
Na tabbata kun ji labarin hidimar alheri na musamman da Allah ya ba ni dominku.


Afisawa 3:3
Wannan wasiƙa za ta faɗa muku kaɗan game da yadda Allah ya nuna mini shirinsa na asiri.


Afisawa 3:7
Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina.


Afisawa 3:8
Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Allah, ni aka ba wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Alʼummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali.


Afisawa 3:9
An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru.


Afisawa 3:10
Nufinsa shi ne, yanzu, ta wurin ikkilisiya, a sanar wa masu mulki da masu iko a samaniya cewa Allah yana da hikima iri dabam dabam.


Afisawa 3:12
A cikinsa da kuma ta wurin bangaskiya ne muke da ƙarfin halin zuwa kusa da Allah gabagaɗi.


Afisawa 3:19
Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani-domin a cika ku da dukan cikar Allah.


Afisawa 4:1
A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da mutanen da Allah ya zaɓa su zama nasa.


Afisawa 4:6
Allah ɗaya ne wanda yake Uban dukan kome, wanda yake a bisanmu duka, yana aiki ta wurinmu duka, yana kuma a cikinmu duka.


Afisawa 4:12
Ya yi haka don yǎ shirya mutanen Allah saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi.


Afisawa 4:13
Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Saʼan nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamarsa.


Afisawa 4:18
Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu.


Afisawa 4:24
Dole kuma ku sanya sabon hali domin ku sabon mutum ne, wanda aka halitta cikin kamannin Allah, yǎ zama mai adalci, mai tsarki da kuma mai gaskiya.


Afisawa 4:30
Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa.


Afisawa 4:32
Ku yi alheri ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.


Afisawa 5:1
Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ʼyaʼya


Afisawa 5:2
ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu ya kuma ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.


Afisawa 5:5
Ku dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah.


Afisawa 5:6
Kada wani yǎ ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.


Afisawa 5:20
Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi kuna gode wa Allah Uba a ko mene ne.


Afisawa 6:6
Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su saʼad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku.


Afisawa 6:11
Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan.


Afisawa 6:13
Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin saʼad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku ɗage.


Afisawa 6:17
Ku kuma ɗauki ƙwalƙwalin ceto, da takobin Ruhu, wato Maganar Allah,


Afisawa 6:23
Salama zuwa ga ʼyanʼuwa, da kuma ƙauna tare da bangaskiya daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


Filibbiyawa 1:2
Alheri da salama gare ku daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


Filibbiyawa 1:3
Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku.


Filibbiyawa 1:7
Daidai ne in yi wannan tunani game da dukanku, da yake kuna a zuciyata; domin ko ina ɗaure cikin sarƙoƙi ko ina kāre bishara ina kuma tabbatar da ita, dukanku kuna tarayya cikin alherin Allah tare da ni.


Filibbiyawa 1:8
Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu.


Filibbiyawa 1:11
cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi-zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa.


Filibbiyawa 1:14
Saboda sarƙoƙina, yawancin ʼyanʼuwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagaɗi da kuma babu tsoro.


Filibbiyawa 1:28
ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku-wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne.


Filibbiyawa 2:6
Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,


Filibbiyawa 2:9
Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,


Filibbiyawa 2:11
kowane harshe kuma yǎ furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.


Filibbiyawa 2:13
gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.


Filibbiyawa 2:15
don ku zama marasa abin zargi, sahihai ʼyaʼyan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya


Filibbiyawa 2:27
Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yǎ rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki.


Filibbiyawa 3:3
Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,


Filibbiyawa 3:9
a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi-adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya.


Filibbiyawa 3:14
ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.


Filibbiyawa 3:15
Dukanmu da muka balaga ya kamata mu yi wannan irin ganin abubuwa. In kuwa saboda wani dalili tunaninku ya yi dabam, Allah zai bayyana muku wannan ma.


Filibbiyawa 3:19
Ƙaddararsu hallaka ce, allahnsu cikinsu ne, rashin kunyarsu shi ne abin fahariyarsu. Hankalinsu yana kan kayan duniya.


Filibbiyawa 4:6
Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe roƙenku ga Allah ta wurin adduʼa da roƙo, tare da godiya.


Filibbiyawa 4:7
Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.


Filibbiyawa 4:9
Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina-ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.


Filibbiyawa 4:18
An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.


Filibbiyawa 4:19
Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.


Filibbiyawa 4:20
Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin.


Kolossiyawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yǎ zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗanʼuwanmu.


Kolossiyawa 1:2
Zuwa ga tsarkaka da kuma amintattun ʼyanʼuwa cikin Kiristi da suke a Kolossi: Bari alheri da salama daga Allah Ubanmu su kasance tare da ku.


Kolossiyawa 1:3
Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, saʼad da muke adduʼa dominku.


Kolossiyawa 1:6
da ta zo muku. Koʼina a duniya wannan bishara tana hayayyafa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta.


Kolossiyawa 1:9
Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin adduʼa dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yǎ sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka.


Kolossiyawa 1:10
Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya: kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah.


Kolossiyawa 1:11
Allah yǎ ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki


Kolossiyawa 1:15
Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta.


Kolossiyawa 1:19
Gama Allah ya ji daɗi yǎ sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi,


Kolossiyawa 1:21
A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku.


Kolossiyawa 1:22
Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi.


Kolossiyawa 1:25
Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai.


Kolossiyawa 1:27
Allah ya yi haka domin ya so ku Alʼummai ku gane abubuwan ban mamakinsa da kuma asirinsa mai ɗaukaka. Wannan asirin kuwa shi ne: Kiristi yana zama a cikinku, shi ne kuma begenku na samun rabo a cikin ɗaukakarsa.


Kolossiyawa 2:2
Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa.


Kolossiyawa 2:3
Kiristi ne ya sa a san asirin Allah.


Kolossiyawa 2:9
Kiristi yana da halin Allah,


Kolossiyawa 2:12
Da yake an binne ku tare da shi cikin baftisma haka kuma aka tashe ku tare da shi ta wurin bangaskiyarku a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.


Kolossiyawa 2:13
Kun zama matattu saboda ku masu zunubi ne kuma saboda halin zunubanku aka ware. Saʼan nan Allah ya sa kuka rayu tare da Kiristi. Ya gafarta mana dukan zunubanmu.


Kolossiyawa 2:19
Ya yanke dangantaka da Kiristi wanda yake kai, wanda ta gare shi ne dukkan jiki yake a haɗe, yake tsaye ta wurin taimakon gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma girma kamar yadda Allah yake sa yǎ yi girma.


Kolossiyawa 2:23
Yin biyayya da irin waɗannan ƙaʼidodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan shaʼawace shaʼawacenmu.


Kolossiyawa 3:1
Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah.


Kolossiyawa 3:3
Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah.


Kolossiyawa 3:6
Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan.


Kolossiyawa 3:12
Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawaliʼu da sauƙinkai da jimrewa.


Kolossiyawa 3:16
Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.


Kolossiyawa 3:17
Kuma komene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.


Kolossiyawa 3:22
Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji.


Kolossiyawa 4:3
Ku kuma yi mana adduʼa, mu ma, don Allah yǎ buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi.


Kolossiyawa 4:11
Yesu (wannan da muke kira Yustus) shi ma yana gaisuwa. Waɗannan ne kaɗai Yahudawa masu bi a cikin abokan aikina saboda mulkin Allah. Sun kuma zama da taimako a gare ni.


Kolossiyawa 4:12
Efafaras naku, mai hidimar Kiristi Yesu, yana gaisuwa. Kullum yana adduʼa dominku sosai, don ku san cikakken abin da Allah yake so ku yi don kuma ku yi shi cikakke.


Kolossiyawa 4:18
Ni Bulus ne nake rubuta muku wannan gaisuwa da hannuna. Ku tuna da sarƙoƙina. Alherin Allah yǎ kasance tare da ku.


1 Tessalonikawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, Sila da Timoti, zuwa ga ikkilisiyar Tassalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi: Alheri da salama zuwa gare ku.


1 Tessalonikawa 1:2
Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin adduʼoʼinmu.


1 Tessalonikawa 1:3
Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.


1 Tessalonikawa 1:4
Gama mun sani, ʼyanʼuwa, ƙaunatattu na Allah, cewa ya zaɓe ku,


1 Tessalonikawa 1:8
Saƙon Ubangiji ya fito daga gare ku ne ba a Makidoniya da Akayya kaɗai ba— bangaskiyarku ga Allah ta zama sananne koʼina. Saboda haka ba ma bukata mu faɗa wani abu a kai,


1 Tessalonikawa 1:9
gama su kansu su suke ba da labari irin karɓar da kuka yi mana. Suna faɗin yadda kuka juyo ga Allah daga gumaka don ku bauta wa Allah rayayye da kuma na gaskiya,


1 Tessalonikawa 2:2
Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba.


1 Tessalonikawa 2:4
A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yǎ danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu.


1 Tessalonikawa 2:5
Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu.


1 Tessalonikawa 2:8
Muka ƙaunace ku ƙwarai har muka ji daɗin bayyana muku, ba bisharar Allah kaɗai ba amma har rayukanmu ma, domin kun zama ƙaunatattu a gare mu.


1 Tessalonikawa 2:9
Ba shakka kuna iya tunawa, ʼyanʼuwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku waʼazin bisharar Allah.


1 Tessalonikawa 2:10
Ku shaidu ne, haka ma Allah, na yadda muka yi zaman tsarki, adalci da kuma marar aibi a cikinku, ku da kuka ba da gaskiya.


1 Tessalonikawa 2:12
muna ƙarfafa ku, muna taʼazantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za ta cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.


1 Tessalonikawa 2:13
Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, saʼad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.


1 Tessalonikawa 2:14
Gama ku, ʼyanʼuwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu: Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,


1 Tessalonikawa 2:15
waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane


1 Tessalonikawa 2:16
suna ƙoƙarin hana mu yin magana ga Alʼummai don kada su sami ceto. Ta haka kullum suke ƙara tara tsibin zunubansu. Fushin Allah ya aukar musu a ƙarshe.


1 Tessalonikawa 3:2
Muka aiki Timoti, wanda yake ɗanʼuwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yǎ gina ku yǎ kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku,


1 Tessalonikawa 3:9
Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku?


1 Tessalonikawa 3:11
Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yǎ shirya mana hanya mu zo wurinku.


1 Tessalonikawa 3:13
Bari yǎ ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu saʼad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa.


1 Tessalonikawa 4:1
A ƙarshe, ʼyanʼuwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau.


1 Tessalonikawa 4:3
Nufin Allah ne a tsarkake ku: cewa ku guje wa fasikanci;


1 Tessalonikawa 4:5
ba cikin muguwar shaʼawa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;


1 Tessalonikawa 4:7
Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki.


1 Tessalonikawa 4:8
Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.


1 Tessalonikawa 4:9
Yanzu kuwa game da ƙaunar ʼyanʼuwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna.


1 Tessalonikawa 4:14
Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu.


1 Tessalonikawa 4:16
Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban malaʼika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko.


1 Tessalonikawa 5:9
Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.


1 Tessalonikawa 5:18
ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.


1 Tessalonikawa 5:23
Bari Allah da kansa, Allah na salama, yǎ tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.


2 Tessalonikawa 1:1
Wasiƙa daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga ikkilisiya ta Tassalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi:


2 Tessalonikawa 1:2
Alheri da salama zuwa gare ku daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


2 Tessalonikawa 1:3
Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ʼyanʼuwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa.


2 Tessalonikawa 1:4
Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da ɗaurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.


2 Tessalonikawa 1:5
Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala.


2 Tessalonikawa 1:6
Allah mai adalci ne: Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala


2 Tessalonikawa 1:8
Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba.


2 Tessalonikawa 1:11
Sane da wannan, kullum muna adduʼa saboda ku, don Allahnmu yǎ sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yǎ cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza.


2 Tessalonikawa 1:12
Muna wannan adduʼa don sunan Ubangijinmu Yesu yǎ sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi.


2 Tessalonikawa 2:4
Zai yi gāba yǎ kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yǎ kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.


2 Tessalonikawa 2:11
Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya


2 Tessalonikawa 2:13
Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku, ʼyanʼuwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya.


2 Tessalonikawa 2:16
Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yǎ ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege,


2 Tessalonikawa 3:5
Bari Ubangiji yǎ bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.


1 Timoti 1:1
Wasiƙa daga Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu,


1 Timoti 1:2
zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya: Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu.


1 Timoti 1:4
ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah-wanda yake ta wurin bangaskiya.


1 Timoti 1:9
Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,


1 Timoti 1:11
da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini.


1 Timoti 1:17
Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.


1 Timoti 2:2
da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.


1 Timoti 2:3
Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu,


1 Timoti 2:5
Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu,


1 Timoti 2:10
sai dai su yi ayyuka masu kyan da suka dace da matan da suke masu bauta wa Allah.


1 Timoti 3:5
(In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?)


1 Timoti 3:15
in na yi jinkiri, za ka san yadda ya kamata mutane su tafiyar da halayensu a cikin jamaʼar Allah, wadda take ikkilisiyar Allah rayayye, ginshiƙi da kuma tushen gaskiya.


1 Timoti 4:3
Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya.


1 Timoti 4:4
Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya,


1 Timoti 4:5
domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma adduʼa.


1 Timoti 4:7
Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labarai banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah.


1 Timoti 4:8
Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa.


1 Timoti 4:10
(saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama), domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.


1 Timoti 5:4
Amma in gwauruwa tana da ʼyaʼya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.


1 Timoti 5:5
Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za ta sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da adduʼoʼi dare da rana gare shi don taimako.


1 Timoti 5:21
Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun malaʼiku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci.


1 Timoti 6:1
Duk waɗanda suke ƙarƙashin bauta, ya kamata su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci girmamawa matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwarmu.


1 Timoti 6:3
In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba,


1 Timoti 6:5
da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi.


1 Timoti 6:6
Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa.


1 Timoti 6:11
Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.


1 Timoti 6:13
Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida,


1 Timoti 6:15
wanda Allah zai kawo a daidai lokaci-Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji,


1 Timoti 6:17
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu.


1 Timoti 6:20
Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi,


2 Timoti 1:1
Wasiƙa daga Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai wanda yake cikin Kiristi Yesu,


2 Timoti 1:2
zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana: Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu.


2 Timoti 1:3
Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin adduʼoʼina.


2 Timoti 1:6
Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana.


2 Timoti 1:7
Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.


2 Timoti 1:8
Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah,


2 Timoti 2:9
wadda nake shan wahala har ga ɗaurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a ɗaure take ba.


2 Timoti 2:14
Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.


2 Timoti 2:15
Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, maʼaikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.


2 Timoti 2:16
Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah.


2 Timoti 2:19
Duk da haka, ƙaƙƙarfan tushen nan na Allah yana nan daram, an hatimce shi da wannan rubutu: “Ubangiji ya san waɗanda suke nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, dole yǎ yi nesa da aikata mugunta.”


2 Timoti 2:25
Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yǎ yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya,


2 Timoti 3:4
masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗin a maimakon ƙaunar Allah— 


2 Timoti 3:16
Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsautarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci,


2 Timoti 3:17
domin mutumin Allah yǎ zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.


2 Timoti 4:1
A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shariʼa, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni:


2 Timoti 4:2
Ka yi waʼazin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa-da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa.


Titus 1:1
Wasiƙa daga Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah— 


Titus 1:2
duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun filʼazal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,


Titus 1:3
da lokacin da Allah ya zaɓa ya cika sai ya bayyana maganarsa a sarari ta wurin waʼazin da aka danƙa mini amana ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu.


Titus 1:4
Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya: Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu.


Titus 1:7
Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yǎ zama marar aibi-ba mai girmankai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba.


Titus 1:16
Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba.


Titus 2:5
su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yǎ rena maganar Allah.


Titus 2:10
kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali.


Titus 2:11
Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane.


Titus 2:12
Yana koya mana mu ce, “Aʼa” ga rashin tsoron Allah da kuma shaʼawace-shaʼawacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani,


Titus 2:13
yayinda muke sauraron begenmu mai albarka-bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi,


Titus 3:4
Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana,


Titus 3:8
Wannan magana tabbatacciya ce, ina kuma ina so ka nanata waɗannan abubuwa ƙwarai, domin waɗanda suka dogara ga Allah su himmantu ga aiki mai kyau. Waɗannan abubuwa suna da kyau sosai suna kuma da amfani ga kowane mutum.


Filemon 1:3
Alheri gare ku da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.


Filemon 1:4
Kullum nakan gode wa Allahna saʼad da nake tuna da kai cikin adduʼoʼina,


Ibraniyawa 1:1
A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokatai dabam dabam da kuma a hanyoyi iri iri,


Ibraniyawa 1:3
Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama.


Ibraniyawa 1:5
Gama ga wane daga cikin malaʼikun Allah ya taɓa cewa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka”? Ko kuwa, “Zan zama Ubansa, shi kuma zai zama Ɗana”?


Ibraniyawa 1:6
Haka kuma, saʼad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya, ya ce, “Bari dukan malaʼikun Allah su yi masa sujada.”


Ibraniyawa 1:8
Amma game da Ɗan, ya ce, “Kursiyinka, Ya Allah, zai kasance har abada abadin, adalci kuma zai zama sandan mulkinka.


Ibraniyawa 1:9
Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka, ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.”


Ibraniyawa 1:13
Ga wane daga cikin malaʼiku Allah ya taɓa cewa, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka”?


Ibraniyawa 2:4
Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da muʼujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa.


Ibraniyawa 2:8
ka kuma sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” Ta sa kome a ƙarƙashinsa, Allah bai bar wani abu da bai sa a ƙarƙashinsa ba. Duk da haka a yanzu ba mu ga kowane abu a ƙarƙashinsa ba.


Ibraniyawa 2:9
Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar malaʼiku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yǎ sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yǎ ɗanɗana mutuwa saboda kowa.


Ibraniyawa 2:10
Ta wurin kawo ʼyaʼya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yǎ zama cikakke ta wurin shan wahala.


Ibraniyawa 2:13
Har wa yau ya ce, “Zan dogara gare shi.” Ya kuma ce, “Ga ni, da ʼyaʼyan da Allah ya ba ni.”


Ibraniyawa 2:17
Saboda wannan dole a mai da shi kamar ʼyanʼuwansa ta kowace hanya, domin yǎ zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yǎ kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane.


Ibraniyawa 3:2
Ya yi aminci ga wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ya yi aminci ga dukan gidan Allah.


Ibraniyawa 3:4
Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne.


Ibraniyawa 3:5
Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba.


Ibraniyawa 3:6
Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gaɗi da kuma begen da muke taƙama a kai.


Ibraniyawa 3:12
Ku lura fa, ʼyanʼuwa, cewa kada waninku yǎ kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai.


Ibraniyawa 3:18
Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba?


Ibraniyawa 4:3
Mu kam da muka gaskata mu ne muka shiga wannan hutu, kamar yadda Allah ya ce, “Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya kammala aikinsa tun halittar duniya.


Ibraniyawa 4:4
Gama a wani wuri ya yi magana a kan rana ta bakwai cikin waɗannan kalmomi, “A rana ta bakwai kuwa Allah ya huta daga dukan aikinsa.”


Ibraniyawa 4:7
Saboda haka Allah ya sāke sa wata rana, yana kiranta Yau, bayan wani dogon lokaci Allah ya yi magana ta bakin Dawuda, yadda aka riga aka faɗa: “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”


Ibraniyawa 4:8
Gama da a ce Yoshuwa ya ba su hutu, da Allah bai yi magana daga baya a kan wata rana dabam ba.


Ibraniyawa 4:9
Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah;


Ibraniyawa 4:10
gama duk wanda ya shiga hutun Allah, shi ma yakan huta daga nasa aiki, kamar yadda Allah ya huta daga nasa.


Ibraniyawa 4:12
Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke.


Ibraniyawa 4:13
Babu wani abu cikin dukan halittar da yake ɓoye daga fuskar Allah. Kowane abu a buɗe yake yana kuma a shimfiɗe a idanun wanda dole mu ba da lissafi a gare shi.


Ibraniyawa 4:14
Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi.


Ibraniyawa 5:1
Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yǎ wakilce su a kan alʼamuran Allah, domin yǎ miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai.


Ibraniyawa 5:4
Ba wanda yakan kai kansa a wannan matsayi mai girma; sai ko Allah ya kira shi, kamar yadda aka yi wa Haruna.


Ibraniyawa 5:5
Haka ma Kiristi bai kai kansa neman ɗaukaka na zama babban firist ba. Allah ne dai ya ce masa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka.”


Ibraniyawa 5:10
Allah kuwa ya naɗa shi yǎ zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek.


Ibraniyawa 5:12
Gaskiya, a yanzu ya kamata a ce kun zama malamai, sai ga shi kuna bukatar wani yǎ sāke koya muku abubuwa masu sauƙi game da abin da Allah ya faɗa. Kuna bukatar madara, ba abinci mai ƙauri ba!


Ibraniyawa 6:1
Dole mu yi ƙoƙarin zama balagaggu mu kuma fara tunani game da abubuwan da suka fi koyarwan nan mai sauƙi game da Kiristi. Bai kamata mu ci gaba da magana game da me ya sa dole mu juye daga ayyukan da suke kawo mutuwa da kuma me ya sa za mu kasance da bangaskiya a cikin Allah ba.


Ibraniyawa 6:3
Da yardar Allah, za mu ci gaba ga ƙarin ganewa.


Ibraniyawa 6:5
waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa,


Ibraniyawa 6:6
ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jamaʼa.


Ibraniyawa 6:7
Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah.


Ibraniyawa 6:10
Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba.


Ibraniyawa 6:13
Babu wanda ya fi Allah, saboda haka saʼad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa,


Ibraniyawa 6:17
Saboda haka da Allah ya so yǎ bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa.


Ibraniyawa 6:18
Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu.


Ibraniyawa 7:1
Wannan Melkizedek sarkin Salem ne da kuma firist na Allah Mafi Ɗaukaka. Shi ne ya sadu da Ibrahim ya albarkace shi saʼad da Ibrahim ya dawowa daga cin nasara a bisa sarakuna,


Ibraniyawa 7:3
Ba shi da mahaifi ko mahaifiya, ba shi da asali, ba shi da farko ko ƙarshe, shi dai kamar Ɗan Allah ne kuma firist ne har abada.


Ibraniyawa 7:15
Canjin nan a Dokar Allah ya ƙara fitowa fili da wani firist dabam wanda yake kamar Melkizedek ya bayyana.


Ibraniyawa 7:19
(gama doka ba ta mai da wani abu cikakke ba), yanzu kuwa bege mafi kyau ya ɗauki matsayinta. Ta haka kuma muka matso kusa da Allah.


Ibraniyawa 7:20
Allah kansa ya yi rantsuwa saʼad da aka naɗa wannan firist. Amma bai yi wani alkawari kamar wannan ba saʼad da aka naɗa sauran firistoci,


Ibraniyawa 7:21
shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa: “Ubangiji ya rantse, ba kuwa zai canja zuciyarsa ba: ‘Kai firist ne na har abada.’ ”


Ibraniyawa 7:25
Saboda haka ya iya ba da ceto gaba ɗaya ga masu zuwa wurin Allah ta wurinsa, gama kullum a raye yake saboda yǎ yi roƙo dominsu.


Ibraniyawa 8:8
Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce: “Ina gaya muku lokaci yana zuwa, saʼad da zan yi sabon alkawari da gidan Israʼila da kuma gidan Yahuda.


Ibraniyawa 8:10
Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Israʼila, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu. Zan zama Allahnsu, su kuwa za su zama mutanena.


Ibraniyawa 9:14
balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtace lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!


Ibraniyawa 9:20
Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”


Ibraniyawa 9:24
Wannan ne ya sa Kiristi bai shiga wuri mai tsarkin da mutum ne ya yi wanda yake hoto ne kawai na ainihin ba. A maimakon haka, ya tafi cikin sama, yana kuma a can tare da Allah don yǎ taimake mu.


Ibraniyawa 10:7
Sai na ce, ‘Ga ni nan-a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi na zo in aikata nufinka, Ya Allah.’ ”


Ibraniyawa 10:12
Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah.


Ibraniyawa 10:21
da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah,


Ibraniyawa 10:22
bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa.


Ibraniyawa 10:27
A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za ta cinye abokan gāban Allah.


Ibraniyawa 10:29
Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri?


Ibraniyawa 10:31
Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.


Ibraniyawa 10:36
Kuna bukata ku jimre don saʼad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari.


Ibraniyawa 11:3
Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani.


Ibraniyawa 11:4
Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadayar da ta fi wadda Kayinu ya miƙa. Ta wurin bangaskiya aka yabe shi cewa shi mai adalci ne, saʼad da Allah ya yi magana mai kyau game da bayarwarsa. Ta wurin bangaskiya kuma har yanzu yana magana, ko da yake ya riga ya mutu.


Ibraniyawa 11:5
Ta wurin bangaskiya ne aka ɗauki Enok daga wannan rayuwa, ta haka bai ɗanɗana mutuwa ba; ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi. Gama kafin a ɗauke shi, an yabe shi a kan ya gamshi Allah.


Ibraniyawa 11:6
In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yǎ gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.


Ibraniyawa 11:10
Gama yana zuba ido ga birnin nan mai tushe, wanda mai zānen gininsa da kuma mai gininsa Allah ne.


Ibraniyawa 11:16
A maimako, suna marmarin wata ƙasa mafi kyau-ta sama. Saboda haka Allah ba ya kunya a kira shi Allahnsu, domin ya riga ya shirya musu birni.


Ibraniyawa 11:17
Ta wurin bangaskiya Ibrahim, saʼad da Allah ya gwada shi, sai ya miƙa Ishaku hadaya. Shi da ya karɓi alkawaran ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa,


Ibraniyawa 11:18
ko da yake Allah ya ce masa, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”


Ibraniyawa 11:19
Ibrahim ya yi tunani cewa Allah yana iya ta da matattu, a misalce kuwa, ya sāke karɓan Ishaku daga matattu.


Ibraniyawa 11:25
Ya zaɓa yǎ sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yǎ ji daɗin shaʼawace-shaʼawacen zunubi na ɗan lokaci.


Ibraniyawa 11:40
Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga makasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu.


Ibraniyawa 12:2
Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah.


Ibraniyawa 12:7
Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ʼyaʼya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa?


Ibraniyawa 12:10
Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa.


Ibraniyawa 12:15
Ku lura fa kada wani yǎ kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai yǎ tsira har yǎ kawo rikici, yǎ kuma ƙazantar da mutane da yawa.


Ibraniyawa 12:16
Ku lura kada wani yǎ zama mai fasikanci, ko marar tsoron Allah kamar Isuwa, wanda saboda ƙwaryar abinci ɗaya tak ya sayar da gādonsa na ɗan fari.


Ibraniyawa 12:22
Sai dai kun zo ne ga Dutsen Sihiyona, ga Urushalima ta sama, birnin Allah mai rai. Kun zo ga dubu dubban malaʼikun da suke cikin taron farin ciki,


Ibraniyawa 12:23
kun zo ga ikkilisiyar ɗan fari, waɗanda sunayensu suna a rubuce a sama. Kun zo ga Allah, alƙalin dukan mutane, kun kuma zo ga ruhohin mutane masu adalci da aka mai da su cikakku.


Ibraniyawa 12:28
Saboda haka, da yake muna karɓar mulkin da ba ya jijjiguwa, sai mu yi godiya, ta haka kuwa mu yi wa Allah sujada yadda ya kamata, tare da bangirma da kuma tsoro,


Ibraniyawa 12:29
gama “Allahnmu wuta ne mai cinyewa.”


Ibraniyawa 13:4
Aure yǎ zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.


Ibraniyawa 13:5
Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”


Ibraniyawa 13:7
Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.


Ibraniyawa 13:15
Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah-yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.


Ibraniyawa 13:16
Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.


Ibraniyawa 13:17
Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.


Ibraniyawa 13:20
Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya ta da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma,


Ibraniyawa 13:24
Ku gai da dukan shugabanninku da kuma dukan mutanen Allah. Waɗanda suke Italiya suna gaishe ku.


Ibraniyawa 13:25
Alherin Allah yǎ kasance da ku duka.


Yaƙub 1:1
Wasiƙa daga Yaƙub, bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Kiristi, Zuwa ga kabilan nan goma sha biyu, da suke warwartse a cikin alʼummai: Gaisuwa.


Yaƙub 1:5
In waninku ya rasa hikima, ya kamata ya roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.


Yaƙub 1:12
Mai albarka ne mutumin da yake ɗaurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.


Yaƙub 1:13
Saʼad da aka jarrabci mutum, kada yǎ ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa;


Yaƙub 1:20
gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so.


Yaƙub 1:27
Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne: a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.


Yaƙub 2:5
Ku saurara, ʼyanʼuwana ƙaunatattu: Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?


Yaƙub 2:16
sai waninku yǎ ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani?


Yaƙub 2:19
Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan-har da rawan jiki.


Yaƙub 2:23
Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah.


Yaƙub 3:9
Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke laʼantar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah.


Yaƙub 4:2
Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba.


Yaƙub 4:4
Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yǎ zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.


Yaƙub 4:6
Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai amma yakan ba da alheri ga masu tawaliʼu.”


Yaƙub 4:7
Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.


Yaƙub 4:8
Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.


1 Bitrus 1:1
Wasiƙa daga Bitrus, manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a cikin duniya, da suke warwatse koʼina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya,


1 Bitrus 1:2
waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa: Alheri da salama su zama naku a yalwace.


1 Bitrus 1:3
Yabo ya tabbata ga Allah da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,


1 Bitrus 1:5
ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yǎ zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci.


1 Bitrus 1:21
Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.


1 Bitrus 1:23
Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah.


1 Bitrus 2:4
Da kuka zo gare shi, rayayyen Dutse-da mutane suka ƙi amma Allah ya zaɓa, kuma mai daraja a gare shi— 


1 Bitrus 2:5
ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi.


1 Bitrus 2:9
Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, alʼumma mai tsarki, jamaʼa mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.


1 Bitrus 2:10
Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai.


1 Bitrus 2:12
Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.


1 Bitrus 2:15
Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci.


1 Bitrus 2:16
Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ʼyantar, sai dai kada ku yi amfani da ʼyancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah.


1 Bitrus 2:17
Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa: Ku ƙaunaci ʼyanʼuwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.


1 Bitrus 2:19
Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah.


1 Bitrus 2:20
Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah.


1 Bitrus 3:4
Maimakon haka, kyanku ya kamata yǎ zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawaliʼu da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.


1 Bitrus 3:5
Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya,


1 Bitrus 3:17
Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.


1 Bitrus 3:18
Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yǎ kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,


1 Bitrus 3:20
waɗanda dā ba su yi biyayya ba saʼad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa,


1 Bitrus 3:21
ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma-ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,


1 Bitrus 3:22
wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah-malaʼiku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.


1 Bitrus 4:2
Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen shaʼawace-shaʼawacen jiki, sai dai nufin Allah.


1 Bitrus 4:6
Dalilin ke nan da ya sa aka yi waʼazin bishara har ga waɗanda yanzu suke mutattu, don ko da yake an hukunta su a matsayin mutane a batun jiki, amma su rayu ga Allah a batun ruhu.


1 Bitrus 4:10
Kowa yǎ yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam.


1 Bitrus 4:11
In wani ya yi magana, ya kamata yǎ yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yǎ yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin.


1 Bitrus 4:14
In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.


1 Bitrus 4:16
Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna.


1 Bitrus 4:17
Gama lokaci ya yi da za a fara yi wa iyalin Allah shariʼa; in kuwa ya fara da mu, to, me zai faru da waɗanda ba sa biyayya da bisharar Allah?


1 Bitrus 4:18
Kuma, “In da ƙyar masu adalci su kuɓuta, me zai faru da marasa tsoron Allah da kuma masu zunubi?”


1 Bitrus 4:19
Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.


1 Bitrus 5:2
Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula-ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima;


1 Bitrus 5:5
Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin, “Allah yana gāba da mai girmankai, amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”


1 Bitrus 5:6
Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yǎ ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama.