A A A A A


Bincika

Mattiyu 5:8
“Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah.


Mattiyu 6:21
Domin kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”


Mattiyu 9:4
Yesu kuwa, da yake ya san tunaninsu, ya ce, “Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?


Mattiyu 12:21
Al'ummai kuma za su sa zuciya ga sunansa.”


Mattiyu 12:35
Mutumin kirki kam, ta kyakkyawar taskar zuciya tasa yakan yi abin kirki, mugu kuwa, ta mummunar taskar zuciya tasa yakan yi mugun abu.


Mattiyu 13:15
Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta, Sun toshe kunnuwansu, Sun kuma runtse idanunsu, Don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu, Su kuma fahimta a zuciyarsu, Har su juyo gare ni in warkar da su.’


Mattiyu 13:19
Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.


Mattiyu 18:35
Haka kuma Ubana da yake Sama zai yi da ko wannenku, in ba ku yafe wa 'yan'uwanku da zuciya ɗaya ba.”


Mattiyu 22:37
Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.


Markus 2:6
To, waɗansu malaman Attaura na nan zaune, suna ta wuswasi a zuciya tasu,


Markus 2:8
Nan da nan, da Yesu ya gane a ransa suna ta wuswasi haka a zuci, sai ya ce musu, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?


Markus 3:5
Da ya duddube su da fushi, yana baƙin ciki da taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.


Markus 4:15
Waɗanda suka fāda a hanya kuwa, su ne kwatancin waɗanda aka shuka Maganar a zuciya tasu. Da zarar sun ji, nan da nan sai Shaiɗan ya zo ya ɗauke Maganar da aka shuka a zuciya tasu.


Markus 6:19
Hirudiya kuwa na riƙe da Yahaya cikin zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami hanya ba,


Markus 6:52
don ba su fahimci al'amarin gurasan nan ba, saboda zuciyarsu ta taurare.


Markus 7:19
tun da yake ba zuciya tasa ya shiga ba, cikinsa ne, ta haka kuma zai fita?” Ta haka Yesu ya halatta kowane irin abinci.


Markus 7:21
Don daga ciki ne, wato daga zuciyar mutum, mugayen tunani yake fitowa, kamar su fasikanci, da sata, da kisankai, da zina,


Markus 7:34
Ya ɗaga kai sama ya yi ajiyar zuciya, sai ya ce masa, “Iffata!” wato “Buɗu!”


Markus 8:12
Sai ya yi wata doguwar ajiyar zuciya, ya ce, “Don me mutanen zamanin nan suke neman ganin alama? Hakika, ina gaya muku, ba wata alamar da za a nuna wa mutanen wannan zamani.”


Markus 8:17
Da yake Yesu ya gane haka, sai ya ce musu, “Don me kuke zancen ba ku da gurasa? Ashe, har yanzu ba ku gane ba, ba ku kuma fahimta ba? Zuciyarku a taurare take?


Markus 9:50
Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sane, dame za a daɗaɗa shi? Sai ku kasance da gishiri a zuciyarku, ku yi zaman lafiya da juna.”


Markus 11:23
Hakika, ina gaya muku, kowa ya ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku’, bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata abin da ya faɗa zai auku, sai a yi masa shi.


Markus 12:30
Sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka, da kuma dukkan ƙarfinka.’


Markus 12:33
A ƙaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukan hankali, da dukkan ƙarfi, a kuma ƙaunaci ɗan'uwa kamar kai, ai, ya fi dukkan hadayar ƙone-ƙone da yanke-yanke nesa.”


Luka 1:46
Sai Maryamu ta ce, “Zuciyata na ɗaukaka shi, Ubangiji,


Luka 1:66
Duk waɗanda suka ji kuwa suka riƙe a zuciyarsu, suna cewa, “Me ke nan ɗan yaron nan zai zama?” Gama ikon Ubangiji yana tare da shi.


Luka 2:35
Domin tunanin zukata da yawa su bayyana. I, ke ma, takobi zai tsaga zuciyarki.”


Luka 5:22
Da Yesu ya gane wuswasinsu, ya amsa musu ya ce, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?


Luka 6:45
Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”


Luka 8:12
Waɗanda suka fāɗi a hanya su ne kwatancin waɗanda suka ji Maganar Allah, sa'an nan Iblis ya zo ya ɗauke Maganar daga zuciyarsu, don kada su ba da gaskiya su sami ceto.


Luka 8:15
Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kamkam da zuciya ɗaya kyakkyawa, suka jure har suka yi amfani.


Luka 9:47
Amma da Yesu ya gane tunanin zuciyarsu, ya kama hannun wani ƙaramin yaro ya ajiye shi kusa da shi.


Luka 10:27
Sai ya amsa ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.”


Luka 12:34
don kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”


Luka 21:34
“Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko.


Luka 24:32
Suka ce wa juna, “Ashe, zuciyarmu ba ta yi annuri ba, sa'ad da yake a hanya, yana bayyana mana Littattafai?”


Luka 24:38
Sai ya ce musu, “Don me kuka firgita, kuke kuma tantama a zuciyarku?


Yohanna 2:25
domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da yake zuciyar ɗan adam.


Yohanna 5:38
Maganarsa kuwa ba ta zauna a zuciyarku ba, domin ba ku gaskata wanda ya aiko ni ba.


Yohanna 7:38
Duk mai gaskatawa da ni, kamar yadda Nassi ya ce, ‘Daga zuciyarsa ne kogunan ruwan rai za su gudana.’ ”


Yohanna 12:40
“Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu, Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci, Har su juyo gare ni in warkar da su.”


Yohanna 13:2
Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi.


Yohanna 14:17
Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam, kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.


Yohanna 16:6
Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku.


Yohanna 16:22
Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa'an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku.


Ayyukan Manzanni 1:24
Sai suka yi addu'a, suka ce, “Ya Ubangiji, masanin zuciyar kowa, a cikin waɗannan mutum biyu ka nuna wanda ka zaɓa,


Ayyukan Manzanni 2:26
Saboda haka, zuciyata ta yi fari, ina farin ciki matuƙa. Ko da yake kuma ni jiki ne, zan zauna ina sa zuciya,


Ayyukan Manzanni 4:36
Ana cikin haka sai Yusufu, wani Balawiye, asalinsa mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannin suke kira Barnaba, (wato ɗan ƙarfafa zuciya),


Ayyukan Manzanni 5:3
Sai Bitrus ya ce, “Kai, Hananiya, ta ƙaƙa Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga kuɗin gonar?


Ayyukan Manzanni 5:4
Kafin ka sayar, ba taka ba ce? Bayan ka sayar kuma, kuɗin ba halalinka ba ne? Ta ƙaƙa ka riya wannan aiki a zuciyarka? Ai, ba mutum ka yi wa ƙarya ba, Allah ka yi wa.”


Ayyukan Manzanni 7:39
Amma kakanninmu suka ƙi yi masa biyayya, suka ture shi, zuciya tasu ta koma ƙasar Masar.


Ayyukan Manzanni 8:21
Ba ruwanka da wannan al'amari sam, don zuciyarka ba ɗaya take ba a gaban Allah.


Ayyukan Manzanni 8:22
Saboda haka sai ka tuba da wannan mugun aiki naka, ka roƙi Ubangiji ko a gafarta maka abin da ka riya a zuciyarka.


Ayyukan Manzanni 8:37
Filibus ya ce, “In dai ka ba da gaskiya da zuciya ɗaya, ai, sai a yi maka.” Bābān ya amsa ya ce, “Na gaskata Yesu Almasihu ɗan Allah ne.”


Ayyukan Manzanni 11:23
Da ya iso ya kuma ga alherin da Allah ya yi musu, ya yi farin ciki, ya gargaɗe su duka su tsaya ga Ubangiji da dukan zuciyarsu,


Ayyukan Manzanni 15:8
Allah kuwa, masanin zuciyar kowa, ya yi musu shaida da ya ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.


Ayyukan Manzanni 16:14
Ɗaya daga cikin masu sauraronmu wata mace ce, mai suna Lidiya, mai sayar da jar hajja, mutuniyar Tayatira, mai ibada ce kuma. Ubangiji ya buɗe zuciyarta, har ta mai da hankali ga abin da Bulus ya faɗa.


Ayyukan Manzanni 16:40
To, da suka fita daga kurkukun, suka tafi wurin Lidiya. Bayan sun ga 'yan'uwa, suka kuma ƙarfafa musu zuciya, suka tashi.


Ayyukan Manzanni 20:1
Bayan hargowar nan ta kwanta, Bulus ya kira masu bi, bayan ya ƙarfafa musu zuciya, ya yi bankwana da su, ya tafi ƙasar Makidoniya.


Ayyukan Manzanni 20:2
Da ya zazzaga lardin nan, ya kuma ƙarfafa masu zuciya ƙwarai, ya zo ƙasar Hellas,


Ayyukan Manzanni 23:6
Amma da Bulus ya ga sashe ɗaya Sadukiyawa ne, ɗayan kuma Farisiyawa, ya ɗaga murya a majalisar ya ce, “Ya 'yan'uwa, ni ma Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ga shi kuwa, saboda na sa zuciya ga tashin matattu ne ake yi mini shari'a.”


Ayyukan Manzanni 24:15
Ina sa zuciya ga Allah, yadda su waɗannan ma suke sawa, wato za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.


Ayyukan Manzanni 26:6
Ai, saboda na sa zuciya ga cikar alkawarin nan ne da Allah ya yi wa kakanninmu nake nan a tsaye a yi mini shari'a.


Ayyukan Manzanni 26:7
Alkwarin nan kuwa, shi ne wanda kabilanmu goma sha biyu suke himmantuwa ga bauta wa Allah dare da rana, suna sa zuciya su ga cikarsa. Saboda sa zuciyar nan kuma fa Yahudawa suke ƙarata, ya sarki!


Ayyukan Manzanni 27:20
Da dai muka yi kwana da kwanaki ba mu ga rana ko taurari ba, gawurtacciyar iskar hadiri kuma ta yi ta bugunmu, sai muka fid da zuciya da tsira.


Ayyukan Manzanni 28:20
Shi ya sa na nema in gana da ku, tun da yake dai saboda sa zuciyar nan da Isra'ila take yi ne nake ɗaure da sarƙan nan.”


Ayyukan Manzanni 28:27
Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta, Sun toshe kunnuwansu, Sun kuma runtse idanunsu, Wai don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu, Su kuma fahimta a zuciyarsu, Har su juyo gare ni in warkar da su.’


Romawa 1:21
Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta.


Romawa 2:5
Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.


Romawa 4:18
Ibrahim kuwa ko da yake ba halin sa zuciya a gare shi, sai ya yi ta sawa, ya gaskata zai zama uban al'ummai da yawa, kamar yadda aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za ta yawaita.”


Romawa 5:2
Ta wurinsa kuma muka sami shiga alherin nan da muke a ciki, saboda bangaskiyarmu, muna kuma taƙama da sa zuciyarmu ga samun ɗaukakar nan ta Allah.


Romawa 5:4
jimiri kuma yake sa ingataccen hali, ingataccen hali kuma yake sa sa zuciya,


Romawa 5:5
ita sa zuciyar nan kuwa ba ta sāce iska faufau, domin Allah ya kwarara ƙaunarsa a zukatanmu, ta wurin Ruhu Mai Tsarki da aka ba mu.


Romawa 6:17
Amma godiya tā tabbata ga Allah, ko da yake dā can ku bayin zunubi ne, a yanzu kam kuna biyayya da zuciya ɗaya ga irin koyarwar nan da aka yi muku.


Romawa 7:8
Amma zunubi, da ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya haddasa ƙyashi iri iri a zuciyata. Gama da ba domin shari'a ba, da zunubi ba shi da wani tasiri.


Romawa 7:22
Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da shari'ar Allah.


Romawa 8:9
Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.


Romawa 8:10
In kuwa Almasihu yana a zuciyarku, ba ruwan jikinku da zunubi ke nan, Ruhu kuwa rai ne a gare ku saboda kun sami adalcin Allah.


Romawa 8:11
In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.


Romawa 8:20
An sarayar da halitta ta zama banza, ba da nufinta ba, amma da nufin wanda ya sarayar da ita. Duk da haka, akwai sa zuciya,


Romawa 8:24
Sa'ad da aka cece mu ne muka yi wannan sa zuciya. Amma kuwa, ai, sa zuciya ga abin da aka samu, ba sa zuciya ba ce. Wa yake sa zuciya ga abin da ya samu?


Romawa 8:25
In kuwa muna sa zuciya ga abin da ba mu samu ba, da jimiri mukan yi sauraronsa.


Romawa 9:2
cewa ina da matuƙar baƙin ciki da kuma takaici marar yankewa a zuciyata.


Romawa 9:18
Wato, yana nuna jinƙai ga wanda ya so, yana kuma taurara zuciyar wanda ya so.


Romawa 10:1
Ya 'yan'uwa, muradin zuciyata da kuma roƙona ga Allah saboda su, shi ne su sami ceto.


Romawa 10:8
Amma me Nassi ya ce? “Maganar, ai, tana kusa da kai, tana ma a bakinka, da kuma a cikin zuciyarka.” Ita ce maganar bangaskiya da muke wa'azi.


Romawa 10:9
Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto.


Romawa 11:34
“Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa wa ya taɓa ba shi wata shawara?”


Romawa 12:8
mai ƙarfafa zuciya kuwa, wajen ƙarfafawarsa, mai yin gudunmawa kuwa, yă bayar hannu sake, shugaba yă yi shugabancinsa da himma, mai yin aikin tausayi, yă yi shi da fara'a.


Romawa 12:12
Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu'a.


Romawa 14:22
Kana da bangaskiya? To, ka riƙe ta tsakaninka da Allah. Albarka tā tabbata ga wanda zuciyarsa ba ta ba shi laifi ba, a game da abin da hankalinsa ya ga daidai ne.


Romawa 15:4
Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta shi ne domin a koya mana, domin mu ɗore a cikin sa zuciyar nan tamu ta wurin haƙuri da ta'aziyyar da Littattafai suke yi mana.


Romawa 15:12
Ishaya kuma ya ce, “Tsatson Yesse zai bayyana, Wanda zai tashi yă mallaki al'ummai, A gare shi ne al'ummai za su sa zuciya.”


Romawa 15:13
Allah mai kawo sa zuciya, yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama saboda bangaskiyarku, domin ku yi matuƙar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.


Romawa 15:24
ina sa zuciya in gan ku, in zan wuce zuwa ƙasar Asbaniya, har ma ku raka ni zuwa can, bayan da na ɗan ɗebe kewa da ganinku.


1 Korintiyawa 2:9
Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa, “Abubuwan da ido bai taɓa gani ba, Kunne bai taɓa ji ba, Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba, Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”


1 Korintiyawa 3:16
Ashe, ba ku sani ku Haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a zuciyarku?


1 Korintiyawa 6:19
Ashe, ba ku sani ba, jikinku Haikali ne na Ruhu Mai Tsarki wanda yake a zuciyarku, wanda kuka kuma samu a gun Allah? Ai, ku ba mallakar kanku ba ne.


1 Korintiyawa 8:9
Sai dai ku lura, kada 'yancin nan naku ya zama abin sa tuntuɓe ga waɗanda ba su tsai da zuciyarsu ba.


1 Korintiyawa 9:10
Ba saboda mu musamman yake magana ba? Hakika saboda mu ne aka rubuta. Ai, ya kamata mai noma yă yi noma da sa zuciya, mai sussuka kuma yă yi sussuka da sa zuciya ga samun rabo daga amfanin gonar.


1 Korintiyawa 9:11
Da yake mun shuka iri na ruhu a zuciyarku, to, wani ƙasaitaccen abu ne, in mun mori amfaninku irin na duniya?


1 Korintiyawa 13:7
Ƙauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da bangaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali, da jimiri a cikin kowane hali.


1 Korintiyawa 14:25
asiran zuciyarsa kuma su tonu. Ta haka sai ya fāɗi ya yi wa Allah sujada, yana cewa lalle Allah na cikinku.


1 Korintiyawa 15:10
Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake, alherin da ya yi mini kuwa ba a banza yake ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, alherin Allah ne da yake zuciyata.


1 Korintiyawa 16:7
Ba sona ne in gan ku a yanzu in wuce kawai ba, a'a, ina sa zuciya ma in yi kwanaki a wurinku, in Ubangiji ya yarda.


2 Korintiyawa 1:7
Sa zuciyarmu a kanku ƙaƙƙarfa ce, domin mun sani, kamar yadda kuka yi tarayya da mu a cikin shan wuya, haka kuma, za ku yi tarayya a cikin ta'aziyyar.


2 Korintiyawa 1:12
Fariyarmu ke nan, lamirinmu yana ba da shaida, cewa mun yi zaman tsarki a duniya da zuciya ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa ga wayo irin na ɗan adam ba, sai dai bisa ga alherin Allah.


2 Korintiyawa 1:17
Ashe, a lokacin da na yi niyyar yin haka, wato na nuna rashin tsai da zuciya ke nan? Ko kuwa shiririta nake yi kawai irin ta halin mutuntaka, in ce, “I” in koma in ce, “A'a”?


2 Korintiyawa 2:7
Gara dai ku yafe masa, ku kuma ƙarfafa masa zuciya, don kada gāyar baƙin ciki ya sha kansa.


2 Korintiyawa 3:12
Tun da yake muna da sa zuciya irin wannan, to, muna magana ne gabanmu gaɗi ƙwarai.


2 Korintiyawa 5:2
A jikin nan muna ajiyar zuciya, mun ƙosa mu samu a suturta mu da jiki namu na Sama,


2 Korintiyawa 5:6
Saboda haka, kullum muke da ƙarfin zuciya, mun kuma sani, muddin muna tare da wannan jiki, a rabe muke da Ubangiji,


2 Korintiyawa 5:8
Hakika muna da ƙarfin zuciya, mun kuma gwammace mu rabu da jikin nan, mu zauna a gun Ubangiji.


2 Korintiyawa 5:9
Saboda haka, ko muna gunsa, ko muna a rabe da shi, burinmu shi ne mu faranta masa zuciya.


2 Korintiyawa 6:11
Ya ku Korantiyawa, ba mu ɓoye muku kome ba, mun saki zuciya da ku ƙwarai.


2 Korintiyawa 6:12
Ai, ba wata rashin yarda a zuciyarmu, sai dai a taku.


2 Korintiyawa 6:13
Ina roƙonku kamar 'ya'yana, ku ma ku saki zuciya da mu.


2 Korintiyawa 7:2
Ku saki zuciya da mu, ai, ba mu cuci kowa ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu zambaci kowa ba.


2 Korintiyawa 7:4
Na amince da ku ƙwarai, ina kuma taƙama da ku gaya. Zuciyata ta ƙarfafa ƙwarai. Duk da wahalce-wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.


2 Korintiyawa 7:6
Amma Allah, shi da yake ƙarfafa wa ƙasƙantattu zuciya, sai ya ƙarfafa mana zuciya da zuwan Titus,


2 Korintiyawa 7:7
ba kuwa da zuwan Titus kawai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyar nan da ya samu a wurinku, a yayin da ya gaya mana yadda kuke begena, kuna nadama, kuna kuma himmantuwa ga goyan bayana, har ma na ƙara farin ciki ƙwarai.


2 Korintiyawa 8:16
Godiya tā tabbata ga Allah wanda ya sa tsananin kula da ku a zuciyar Titus, kamar yadda nake yi.


2 Korintiyawa 10:15
Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba ta kuma shafi aikin waɗansu ba. Amma muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku ya riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske,


Galatiyawa 1:10
To, wato ni son mutane nake nema ne, ko kuwa na Allah? Ko kuwa ƙoƙari nake yi in faranta wa mutane zuciya? Da har yanzu mutane nake faranta wa zuciya, ai, da ban zama bawan Almasihu ba.


Galatiyawa 2:8
(domin shi da ya yi aiki a zuciyar Bitrus ya sa shi manzo ga masu kaciya, shi ne kuma ya yi aiki a zuciyata, ya sa ni manzo ga al'ummai),


Galatiyawa 4:19
Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har Almasihu ya siffatu a zuciyarku!


Galatiyawa 6:8
Wanda ya yi shuka a kwaɗayin son zuciyarsa, ta wurin son zuciya zai girbi ruɓa. Wanda ya yi shuka a Ruhu, ta wurin Ruhu zai girbi rai madawwami.


Afisawa 2:2
waɗanda dā kuke a ciki, kuna biye wa al'amarin duniyar nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskar nan da take zuga zuciyar kangararru a yanzu.


Afisawa 2:3
Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha'awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi'a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran 'yan adam.


Afisawa 3:16
ina addu'a ya yi muku baiwa bisa ga yalwar ɗaukakarsa, ku ƙarfafa matuƙa a birnin zuciyarku ta wurin Ruhunsa,


Afisawa 3:20
Ɗaukaka tā tabbata ga wannan da yake da ikon aikatawa fiye da dukkan abin da za mu roƙa, ko za mu zata nesa, wato, aikatawa ta ƙarfin ikonsa da yake aiki a zuciyarmu.


Afisawa 4:18
Duhun zuciya yake a gare su, bare suke ga rai wanda Allah yake bayarwa, sabili da jahilcin da yake a gare su, saboda taurin kansu.


Afisawa 4:19
Zuciyarsu ta yi kanta, sun dulmiya a cikin fajirci, sun ɗokanta ido a rufe ga yin kowane irin aikin lalata.


Afisawa 6:5
Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya, da hali bangirma tare da matsananciyar kula da zuciya ɗaya, Almasihu kuke yi wa ke nan,


Afisawa 6:6
ba aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai kamar bayin Almasihu masu aikata abin da Allah yake so, da zuciya ɗaya,


Afisawa 6:22
Na aiko shi gare ku musamman domin ku san yadda muke, ya kuma ƙarfafa muku zuciya.


Filibbiyawa 1:7
Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.


Filibbiyawa 1:17
Waɗancan kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin ɗaurina.


Filibbiyawa 1:20
Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata.


Filibbiyawa 2:19
Ina sa zuciya ga Ubangiji Yesu in aika muku da Timoti da wuri, don ni ma in ƙarfafa da samun labarinku.


Kolossiyawa 2:2
Sona a ƙarfafa musu zuciya, ƙauna tana haɗa su, har su sami dukkan mayalwaciyar fahimta tabbatacciya, da sanin asirin nan na Allah, wato Almasihu,


Kolossiyawa 2:18
Kada ku yarda kowane mutum ya ɓata ku, da cewa shi wani abu ne saboda, ya ga wahayi, ya kuma lazamta da yin tawali'un ƙarya, in ji shi kuma yana yi wa mala'iku sujada. Irin wannan mutum kumbura kansa yake yi ba dalili, sai ta son zuciya irin na halin mutuntaka,


Kolossiyawa 3:15
Salamar Almasihu kuma tă mallaki zuciyarku, domin lalle ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah.


Kolossiyawa 3:16
Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.


Kolossiyawa 3:22
Ku bayi, ku yi biyayya ga waɗanda suke iyayengijinku na duniya ta kowace hanya, ba da aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji.


Kolossiyawa 4:8
Na aiko shi a gare ku musamman, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.


Kolossiyawa 4:11
Yasuwa kuma da ake kira Yustus yana gaishe ku. Wato, cikin abokan aikina ga Mulkin Allah, waɗannan su kaɗai ne daga cikin Yahudawa masu bi, sun kuwa sanyaya mini zuciya.


1 Tessalonikawa 2:13
Saboda wannan ne kuma muke gode wa Allah ba fasawa, domin sa'ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, Maganar Allah, wadda take aiki a cikin zuciyarku, ku masu ba da gasikya.


1 Tessalonikawa 2:19
Su wane ne abin sa zuciyarmu, da abin farin cikinmu, da kuma abin taƙamarmu a gaban Ubangiji Yesu a ranar komowarsa, in ba ku ba?


1 Tessalonikawa 3:7
Saboda haka 'yan'uwa, cikin dukan wahala da ƙuncin da muka sha, an sanyaya mana zuciya a game da ku, albarkacin bangaskiyarku.


1 Tessalonikawa 5:11
Saboda haka, sai ku ƙarfafa wa juna zuciya, kuna riƙa inganta juna, kamar dai yadda kuke yi.


1 Tessalonikawa 5:14
Muna kuma yi muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa.


1 Timoti 1:5
Alhali kuwa manufar gargaɗinmu ƙauna ce, wadda take bulbulowa daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya.


1 Timoti 3:14
Ina sa zuciya in zo a wurinka ba da daɗewa ba, amma ina rubuto maka waɗannan abubuwa.


1 Timoti 5:11
Amma kada ka lasafta gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu, a cikin gwaurayen, don in zuciyarsu ta kasa daurewa a game da wa'adin da suka yi da Almasihu, sai su so yin aure,


2 Timoti 1:14
Kyakkyawan abin nan da aka ba ka amana, ka kiyaye shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, wanda yake zaune a zuciyarmu.


2 Timoti 1:16
Ubangiji yă yi wa iyalin Onisifaras jinƙai, don sau da yawa yake sanyaya mini zuciya, bai kuwa ji kunyar ɗaurina da aka yi ba.


2 Timoti 2:22
Don haka, sai ka guje wa mugayen sha'awace-sha'awacen ƙuruciya, ka dimanci aikin adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma salama, tare da waɗanda suke roƙon Ubangiji da zuciya tsarkakakkiya.


2 Timoti 4:22
Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.


Titus 1:9
mai riƙe da tabbatacciyar maganar nan kankan, daidai yadda aka koya masa, domin yă iya ƙarfafa wa waɗansu zuciya da sahihiyar koyarwa, ya kuma ƙaryata waɗanda suka yi musunta.


Titus 1:15
Ga masu tsarkin rai duk al'amarinsu mai tsarki ne, marasa tsarkin rai kuwa marasa ba da gaskiya, ba wani al'amarinsu da yake mai tsarki, da zuciyarsu da lamirinsu duka marasa tsarki ne.


Filemon 1:7
Na yi farin ciki ƙwarai, zuciyata kuma ta ƙarfafa saboda ƙaunar da kake yi, yă kai 'dan'uwana, domin zukatan tsarkaka sun wartsake ta dalilinka.


Filemon 1:12
Ga shi nan, na komo maka da shi kamar gudan zuciyata.


Filemon 1:20
Ya ɗan'uwana, ka yarda in sami wata fa'ida a gare ka saboda Ubangiji! Ka sanyaya mini zuciya saboda Almasihu.


Filemon 1:22
Har wa yau kuma, ka shirya mini masauki, domin ina sa zuciya a ba ni yarjin zuwa gare ku albarkacin addu'arku.


Ibraniyawa 3:1
Saboda haka, ya ku 'yan'uwa tsarkaka, ku da kuke da rabo a kiran nan basamaniya, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa,


Ibraniyawa 3:10
Saboda haka ne, na yi fushi da mutanen wannan zamani, Har na ce, ‘A kullum zuciyarsu a karkace take, Ba su kuwa san hanyoyina ba.’


Ibraniyawa 3:12
Ku kula fa, 'yan'uwa, kada wata muguwar zuciyar marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗar da ku daga wurin Allah Rayayye.


Ibraniyawa 3:13
Sai dai kowace rana ku ƙarfafa wa juna zuciya muddin akwai “Yau”, don kada kowannenku ya taurare, ta yaudarar zunubi.


Ibraniyawa 4:12
Domin Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane irin takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gaɓoɓi, har ya zuwa cikin ɓargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufarta.


Ibraniyawa 8:10
Wannan shi ne alkawarin da zan yi da jama'ar Isra'ila, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Wato, zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu. Zan kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.


Ibraniyawa 10:16
“Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu,”


Ibraniyawa 10:22
sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa.


Ibraniyawa 10:25
Kada mu bar yin taronmu, yadda waɗansu suke yi, sai dai mu ƙarfafa wa juna zuciya, tun ba ma da kuka ga ranar nan tana kusatowa ba.


Ibraniyawa 13:9
Kada baƙuwar koyarwa iri iri ta bauɗar da ku, ai, abu ne mai kyau alherin Allah ya zamana shi yake ƙarfafa zuciya, ba abinci iri iri ba, waɗanda ba su amfani ga masu dogara da su.


Yaƙub 1:7
Kada irin mutumin nan mai zuciya biyu, wanda bai tsai da zuciyarsa a gu ɗaya a dukan al'amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.


Yaƙub 1:21
Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na'am da ita a cikin halin tawali'u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.


Yaƙub 3:6
Harshe ma wuta ne fa! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata dukan jiki, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa Gidan Wuta ne yake zuga shi.


Yaƙub 3:14
Amma in kuna da matsanancin kishi da sonkai a zuciyarku, kada ku yi alwashi da haka, kuna saɓa wa gaskiya.


Yaƙub 3:15
Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga Sama ba ce, ta duniya ce, ta son zuciya, ta Shaiɗan kuma.


Yaƙub 4:8
Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.


Yaƙub 4:9
Ku yi nadama, ku yi baƙin ciki, ku yi ta kuka. Dariyarku tă zama baƙin ciki, murnarku tă koma ɓacin zuciya.


1 Bitrus 1:11
suna bincike ko wane ne, ko kuma wane lokaci ne, Ruhun Almasihu da yake a zuciyarsu yake ishara, sa'ad da ya yi faɗi a kan wuyar da Almasihu zai sha, da kuma ɗaukakar da take biye.


1 Bitrus 1:13
Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu.


1 Bitrus 1:22
Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.


1 Bitrus 2:11
Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha'awace-sha'awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku.


1 Bitrus 4:2
domin a nan gaba yă ƙarasa sauran zamansa na jiki ba tare da biye wa muguwar sha'awar zuciya ba, sai dai nufin Allah.


2 Bitrus 2:8
(don kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa'ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci),


1 Yohanna 2:14
Ya ku dattawa, na rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil'azal. Ya ku samari, na rubuto muku ne domin kuna da ƙarfi, Maganar Allah tana zauna a zuciyarku, kun kuma ci nasara a kan Mugun nan.


1 Yohanna 2:24
Ku kam, abin da kuka ji tun da farko, sai ya zauna a zuciyarku. In abin da kuka ji tun farko ya zauna a zuciyarku, ku ma sai ku zauna cikin Ɗan, da kuma Uban.


1 Yohanna 2:27
Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.


1 Yohanna 3:3
Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.


1 Yohanna 3:20
duk sa'ad da zuciyarmu ta ba mu laifi, saboda Allah ya fi ta, ya kuma san kome.


1 Yohanna 3:21
Ya ku ƙaunatattuna, in zuciyarmu ba ta ba mu laifi ba, sai mu je gaban Allah amincewa.


1 Yohanna 4:4
Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kun kuma ci nasara a kan waɗannan, domin shi wanda yake zuciyarku ya fi wanda yake duniya ƙarfi.


2 Yohanna 1:12
Ko da yake ina da abin da zan faɗa muku da yawa, na gwammace ba a wasiƙa ba, amma na sa zuciya in ziyarce ku, mu yi magana baka da baka. don farin cikinmu ya zama cikakke.


3 Yohanna 1:14
Ina sa zuciya mu sadu ba da daɗewa ba, sa'an nan ma yi magana baka da baka.


Yahuda 1:19
Waɗannan su ne masu raba tsakani, masu son zuciya, marasa Ruhu.


Ruʼuya ta Yohanna 2:23
Zan kashe 'ya'yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.


Ruʼuya ta Yohanna 18:7
Yadda ta ɗaukaka kanta, ta yi almubazzaranci, Haka ku ma ku saka mata da azaba, da baƙin ciki gwargwadon haka. Tun da yake a birnin zuciyarta ta ce, ‘Ni sarauniya ce, a zaune nake, Ni ba gwauruwa ba ce, Ba ni da baƙin ciki kuma har abada!’


Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010