A A A A A


Bincika

Markus 9:50
Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sane, dame za a daɗaɗa shi? Sai ku kasance da gishiri a zuciyarku, ku yi zaman lafiya da juna.”


Ayyukan Manzanni 12:20
To, Hirudus ya yi fushi ƙwarai da mutanen Taya da na Sidon. Suka zo wurinsa da nufi ɗaya. Bayan sun rinjayi Bilastasa, sarkin fāda, suka nemi zaman lafiya, domin ga ƙasar sarkin nan suka dogara saboda abincinsu.


Ayyukan Manzanni 24:2
Da aka kirawo Tartulus, ya shiga kai ƙarar Bulus, ya ce, “Ya mafifici Filikus, tun da yake ta gare ka ne muke zaman lafiya ƙwarai, ta tsinkayarka ne kuma ake kyautata zaman jama'armu,


Romawa 12:16
Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali'u. Kada ku aza kanku masu hikima ne.


Romawa 12:18
In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.


Romawa 15:5
Allah mai ba da haƙuri da ta'aziyya, yă ba ku zaman lafiya da juna bisa halin Almasihu Yesu,


1 Korintiyawa 7:15
In kuwa shi, ko ita, marar ba da gaskiya ɗin yana son rabuwa, to, sai su rabu. A wannan hali, ɗan'uwa ko 'yar'uwa mai bi, ba tilas a kansu, domin Allah ya kira mu ga zaman lafiya.


2 Korintiyawa 13:11
Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku.


Filibbiyawa 4:2
Na gargaɗi Afodiya, na kuma gargaɗi Sintiki, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.


1 Tessalonikawa 4:11
kuna himmantuwa ga zaman lafiya, kuna kula da sha'anin gabanku kawai, kuna kuma aiki da hannunku, kamar yadda muka umarce ku,


1 Tessalonikawa 5:3
Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira.


1 Tessalonikawa 5:13
Ku riƙe su da mutunci ƙwarai game da ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.


Ibraniyawa 12:14
Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, ku kuma zama a tsarkake, in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji.


1 Bitrus 3:11
Ya rabu da mugunta, ya kama nagarta, Ya himmantu ga zaman lafiya, ya kuma dimance ta.


3 Yohanna 1:2
Ya ƙaunataccena, ina addu'a kă sami zaman lafiya ta kowace hanya da kuma lafiya jiki, kamar yadda ruhunka yake a zaune lafiya.


Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010