A A A A A


Bincika

Mattiyu 4:2
Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi.


Mattiyu 6:16
“In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan.


Mattiyu 6:17
Amma in kana azumi, ka shafa mai a ka, ka kuma wanke fuska,


Mattiyu 6:18
don kada mutane su ga alama kana azumi, sai dai Ubanku da yake ɓoye ya gani. Ubanku kuma da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”


Mattiyu 9:14
Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, “Don me mu da Farisiyawa mukan yi azumi, amma naka almajiran ba sa yi?”


Mattiyu 9:15
Sai Yesu ya ce musu, “Abokan ango sa yi baƙin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.


Mattiyu 17:21
Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a da azumi.]”


Markus 2:18
To, almajiran Yahaya da na Farisiyawa suna azumi, sai aka zo aka ce masa, “Don me almajiran Yahaya da na Farisiyawa suke azumi, amma naka almajirai ba sa yi?”


Markus 2:19
Sai Yesu ya ce musu, “Ashe, abokan ango sa iya azumi tun ango na tare da su? Ai, muddin suna tare da angon, ba za su yi azumi ba.


Markus 2:20
Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.


Luka 2:37
da mijinta ya mutu kuma ta yi zaman gwauranci har shekara tamanin da huɗu. Ba ta rabuwa da Haikalin, tana bauta wa Allah dare da rana ta wurin yin addu'a da azumi.


Luka 5:33
Sai suka ce masa, “Almajiran Yahaya suna azumi a kai a kai, suna kuma addu'a, haka kuma almajiran Farisiyawa, amma naka suna ci suna sha.”


Luka 5:34
Sai Yesu ya ce musu, “Wato kwa iya sa abokan ango su yi azumi tun angon yana tare da su?


Luka 5:35
Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.”


Luka 18:12
Duk mako ina azumi sau biyu. Kome na samu nakan fitar da zakka.’


Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010