A A A A A


Bincika

Mattiyu 7:11
To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?


Mattiyu 11:26
Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.


Mattiyu 12:12
Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja? Domin haka ya halatta a yi alheri a ran Asabar.”


Mattiyu 20:15
Ashe, ba ni da ikon yin abin da na ga dama da abin da yake mallakata? Ko kuwa kana jin haushin alherina ne?’


Mattiyu 26:10
Yesu kuwa da ya lura da haka, sai ya ce musu, “Don me kuke damun matar nan? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.


Markus 3:4
Ya ce musu, “Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko kuwa mugunta? A ceci rai, ko kuwa a kashe shi?” Amma sai suka yi shiru.


Markus 14:6
Amma Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta. Don me kuke damunta? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.


Markus 14:7
Kullum kuna tare da gajiyayyu, ko yaushe kuma kuke so, kwa iya yi musu alheri, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.


Luka 1:43
Ta yaya wannan alheri ya same ni, har da uwar Ubangijina za ta zo gare ni?


Luka 1:53
Mayunwata ya ƙosar da abubuwan alheri, Mawadata kuwa ya sallame su hannu wofi.


Luka 2:40
Ɗan yaron kuwa ya girma, ya kawo ƙarfi, yana mai matuƙar hikima. Alherin Allah kuwa yana tare da shi.


Luka 4:22
Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”


Luka 6:9
Yesu ya ce musu, “Ina yi muku tambaya. Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko mugunta? A ceci rai, ko a hallaka shi?”


Luka 6:27
“Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri.


Luka 6:33
In kuma sai waɗanda suke muku alheri kawai kuke yi wa alheri, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma haka suke yi.


Luka 6:35
Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.


Luka 10:21
A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.


Luka 19:44
su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan'uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”


Yohanna 1:14
Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.


Yohanna 1:16
Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri.


Yohanna 1:17
Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance.


Ayyukan Manzanni 4:9
in dai ana tuhumarmu ne yau a kan alherin da aka yi wa gajiyayyen mutumin nan, ta yadda aka warkar da shi,


Ayyukan Manzanni 4:33
Manzanni kuma suka yi shaida da tabbatarwa mai ƙarfi a kan tashin Ubangiji Yesu daga matattu. Alheri mai yawa yana tare da kowannensu,


Ayyukan Manzanni 6:8
To, Istifanas, cike da alheri da iko, ya yi ta yin manyan al'ajabai da mu'ujizai a cikin jama'a.


Ayyukan Manzanni 10:38
wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.


Ayyukan Manzanni 11:23
Da ya iso ya kuma ga alherin da Allah ya yi musu, ya yi farin ciki, ya gargaɗe su duka su tsaya ga Ubangiji da dukan zuciyarsu,


Ayyukan Manzanni 13:43
Da jama'a suka watse, Yahudawa da yawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, masu ibada, suka bi Bulus da Barnaba. Su kuma suka yi musu magana, suna yi musu gargaɗi su zauna a cikin alherin Allah.


Ayyukan Manzanni 14:3
Sai Bulus da Barnaba suka daɗe a nan ƙwarai, suna wa'azi gabagaɗi bisa ga ikon Ubangiji, shi da ya shaida maganar alherinsa ta yarjin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi ta hannunsu.


Ayyukan Manzanni 14:17
Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa, ba shaida ba, domin yana yin alheri, shi da yake yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosar da ku da abinci, yana kuma faranta muku rai.”


Ayyukan Manzanni 14:26
Daga nan kuma suka shiga jirgin ruwa sai Antakiya, inda tun dā aka yi musu addu'a alherin Allah ya kiyaye su cikin aikin nan da yanzu suka gama.


Ayyukan Manzanni 15:11
Amma mun gaskata, cewa, albarkacin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”


Ayyukan Manzanni 15:40
amma Bulus ya zaɓi Sila, bayan 'yan'uwa sun yi masa addu'a alherin Allah ya kiyaye shi, ya tafi.


Ayyukan Manzanni 18:27
Da ya so hayewa zuwa ƙasar Akaya, 'yan'uwa suka taimake shi, suka rubuta wa masu bi wasiƙa su karɓe shi hannu biyu biyu. Da kuwa ya isa, ya yi matuƙar taimako ga waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin alherin Ubangiji,


Ayyukan Manzanni 20:24
Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.


Ayyukan Manzanni 20:32
To, yanzu na danƙa ku ga Ubangiji, maganar alherinsa kuma tă kiyaye ku, wadda ita take da ikon inganta ku, ta kuma ba ku gādo tare da dukan tsarkaka.


Ayyukan Manzanni 27:3
Kashegari ga mu a Sidon. Yuliyas kuwa ya yi wa Bulus alheri, ya ba shi izini ya je ya gano abokansa, su yi masa taimako.


Ayyukan Manzanni 28:2
Mutanen garin kuwa sun yi mana alheri matuƙar alheri, don sun hura wuta sun karɓe mu, mu duka, saboda ana ruwa, ga kuma sanyi.


Romawa 1:5
Ta wurinsa ne muka sami alheri da kuma manzanci, saboda sunansa dukan al'ummai su gaskata su yi biyayya,


Romawa 1:7
Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu. Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.


Romawa 2:4
Ko kuwa kana raina yalwar alherinsa, da jimirinsa, da kuma haƙurinsa ne? Ashe, ba ka sani ba alherin Allah yana jawo ka zuwa ga tuba?


Romawa 3:24
Amma ta wurin alherin da Allah ya yi musu kyauta, sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi.


Romawa 4:16
Saboda haka al'amarin ya dogara ga bangaskiya, domin yă zama bisa ga alheri, don kuma a tabbatar da alkawarin nan ga dukkan zuriyar Ibrahim, ba ga masu bin Shari'a kaɗai a cikinsu ba, har ma ga waɗanda suke da bangaskiya irin Ibrahim, shi da yake ubanmu duka.


Romawa 5:2
Ta wurinsa kuma muka sami shiga alherin nan da muke a ciki, saboda bangaskiyarmu, muna kuma taƙama da sa zuciyarmu ga samun ɗaukakar nan ta Allah.


Romawa 5:15
Amma fa baiwar nan dabam take ƙwarai da laifin nan. Ai, in laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa masu ɗumbun yawa mutuwa, ashe ma, alherin Allah, da kuma baiwar nan, albarkacin alherin Mutum ɗaya, Yesu Almasihu, sai su yalwata ga masu ɗumbun yawa fin haka ƙwarai.


Romawa 5:17
In kuwa saboda laifin mutum ɗayan nan ne mutuwa ta yi mallaka ta wurinsa, ashe kuwa, waɗanda suke samun alherin nan mayalwaci, da kuma baiwar nan ta adalcin Allah, sai su yi mallaka fin haka ƙwarai a cikin rai, ta wurin ɗayan nan, wato Yesu Almasihu.


Romawa 5:20
Shari'a fa, an shigo da ita ne, don laifi yă haɓaka. Amma a inda zunubi ya haɓaka, alherin Allah ma ya fi haɓaka ƙwarai da gaske.


Romawa 5:21
Wato kamar yadda mallakar zunubi mutuwa ce, haka mallakar Allah ta wurin alheri adalci ce, da take bi da mu zuwa rai madawwami ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu.


Romawa 6:1
To, me kuma za mu ce? Ma ci gaba da yin zunubi ne domin alherin Allah yă haɓaka?


Romawa 6:14
Domin zunubi ba zai mallake ku ba, tun da yake ba shari'a take iko da ku ba alherin Allah ne.


Romawa 6:15
To, ƙaƙa? Wato, sai mu yi zunubi don shari'a ba ta iko da mu, sai alherin Allah? A'a, ko kusa!


Romawa 8:28
Mun kuma sani al'amura duka suna aikatawa tare, zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, wato, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa.


Romawa 11:5
Haka ma a wannan zamani akwai ragowa, waɗanda aka zaɓa saboda alherinsa.


Romawa 11:6
In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.


Romawa 11:22
Dubi fa alherin Allah da kuma tsananinsa, wato, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, alherinsa kuwa a gare ka, muddin ka ɗore a cikin alherin. In ba haka ba, kai ma sai a datse ka.


Romawa 12:3
Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.


Romawa 12:6
Da yake muna da baiwa iri iri, gwargwadon alherin da aka yi mana, to, sai mu yi amfani da su. In ta annabci ce, sai mu yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarmu,


Romawa 12:13
Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.


Romawa 15:15
Duk da haka, a kan waɗansu batatuwan da na rubuto muku, na ƙara ƙarfafawa ƙwarai, domin tuni, saboda alherin da Allah ya yi mini


Romawa 16:20
Allah mai ba da salama kuwa, zai sa ku tattake Shaiɗan da hanzari. Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.


Romawa 16:24
Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku duka. Amin, Amin.


1 Korintiyawa 1:3
Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.


1 Korintiyawa 1:4
Kullum nakan gode wa Allah dominku, saboda alherin Allah da aka yi muku baiwa ta hanyar Almasihu Yesu,


1 Korintiyawa 3:10
Kamar gwanin magini, haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma yana ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutum, yă lura da irin ginin da yake ɗorawa a kai.


1 Korintiyawa 15:10
Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake, alherin da ya yi mini kuwa ba a banza yake ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, alherin Allah ne da yake zuciyata.


1 Korintiyawa 16:23
Alherin Ubangijinmu Yesu yă tabbata a gare ku.


2 Korintiyawa 1:2
Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.


2 Korintiyawa 1:12
Fariyarmu ke nan, lamirinmu yana ba da shaida, cewa mun yi zaman tsarki a duniya da zuciya ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa ga wayo irin na ɗan adam ba, sai dai bisa ga alherin Allah.


2 Korintiyawa 4:15
Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin Allah ya yaɗu ga mutane masu yawa, ta haka ya zama sanadin yawaita godiya ga Allah, domin a ɗaukaka Allah.


2 Korintiyawa 6:1
Da yake kuma muna aiki tare da Allah, muna roƙonku kada ku yi na'am da alherin Allah a banza.


2 Korintiyawa 8:1
To, 'yan'uwa, muna so mu sanar da ku alherin Allah da ya bayar a cikin ikilisiyoyin Makidoniya,


2 Korintiyawa 8:2
wato, ko da yake an gwada su da matsananciyar wahala, suna kuma a cikin baƙin talauci, duk da haka, yawan farin cikinsu, har ya kai su ga yin alheri ƙwarai da gaske.


2 Korintiyawa 8:4
Sun roƙe mu ƙwarai da gaske mu yi musu alheri su ma, a sa su a cikin masu yi wa tsarkaka gudunmawa,


2 Korintiyawa 8:6
Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi.


2 Korintiyawa 8:7
To, da yake kun fifita a kowane abu, wato, a cikin bangaskiya, da magana, da sani, da matuƙar himma, da kuma ƙaunar da kuke yi mana, to, sai ku fifita a wannan aikin alheri ma.


2 Korintiyawa 8:9
Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.


2 Korintiyawa 8:19
ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikilisiyoyi sun zaɓe shi ya riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu.


2 Korintiyawa 9:9
Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, Ayyukansa na alheri madawwama ne.”


2 Korintiyawa 9:10
Shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, ya riɓanya shi, ya kuma yawaita albarkar ayyukanku na alheri.


2 Korintiyawa 9:12
Domin aikin nan na alheri, ba biyan bukatar tsarkaka kaɗai yake yi ba, har ma yana ƙara yawaita godiya ga Allah ƙwarai da gaske.


2 Korintiyawa 9:13
Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na'am da bisharar Almasihu, saboda kuma gudunmawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.


2 Korintiyawa 9:14
Su kuwa za su yi muku addu'a, su yi ɗokin ganinku saboda alherin Allah marar misaltuwa da ya yi muku.


2 Korintiyawa 12:9
amma ya ce mini, “Alherina yā isa, domin ta wajen rashin ƙarfi ake ganin cikar ikona.” Saboda haka sai ma in ƙara yin alfarma da raunanata da farinciki fiye da na da, domin ikon Almasihu ya zauna a tare da ni.


2 Korintiyawa 13:14
Alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su tabbata a gare ku duka.


Galatiyawa 1:3
Alheri da salama na Allah Uba su tabbata a gare ku, da na Ubangijinmu Yesu Almasihu,


Galatiyawa 1:6
Na yi mamaki yadda nan da nan kuke ƙaurace wa wanda ya kira ku, bisa ga alherin Almasihu, har kuna koma wa wata baƙuwar bishara,


Galatiyawa 1:15
Amma sa'ad da shi wannan da ya keɓe ni tun kafin a haife ni, ya kuma kira ni bisa ga alherinsa, ya ji daɗin


Galatiyawa 2:9
sai Yakubu da Kefas da Yahaya, su da suke shahararrun ginshiƙan ikkilisiya, da suka ga alherin da Allah ya yi mini, sai suka karɓe mu, ni da Barnaba, hannu biyu biyu, domin mu mu je wurin al'ummai, su kuwa gun masu kaciya.


Galatiyawa 2:21
Ba na tozarta alherin Allah. Don da ta wurin bin Shari'a ake samun adalcin Allah, ashe, da Almasihu ya mutu a banza ke nan.”


Galatiyawa 5:4
Ku da kuke neman kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, kun katse daga Almasihu ke nan, kun noƙe daga alherin Allah.


Galatiyawa 6:6
Duk wanda aka koya wa Maganar, yă ci moriyar abubuwansa na alheri tare da mai koyarwa.


Galatiyawa 6:18
Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku, 'yan'uwa. Amin.


Afisawa 1:2
Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.


Afisawa 1:5
Ya ƙaddara mu mu zama 'ya'yansa ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga nufinsa na alheri,


Afisawa 1:6
domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa.


Afisawa 1:7
Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah,


Afisawa 2:5
ko a sa'ad da muke matattu ma ta wurin laifofinmu, sai ya rayar da mu tare da Almasihu (ta wurin alheri an cece ku),


Afisawa 2:7
Allah ya yi wannan kuwa domin a zamani mai zuwa ya bayyana yalwar alherinsa marar misaltuwa, ta wajen nuna mana alheri ta wurin Almasihu Yesu.


Afisawa 2:8
Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah,


Afisawa 3:2
in dai kun ji labarin mai da ni mai hidimar alherin Allah wanda aka yi mini baiwa saboda ku,


Afisawa 3:7
An kuwa sa ni mai hidimar wannan bishara, a bisa ga baiwar alherin Allah da aka yi mini ta ƙarfin ikonsa.


Afisawa 3:8
Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


Afisawa 4:7
Amma an ba kowannenmu alheri gwargwadon baiwar Almasihu.


Afisawa 4:29
Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.


Afisawa 6:8
Kun sani, kowane alherin da mutum ya yi, ko shi ɗa ne ko bawa, Ubangiji zai sāka masa shi.


Afisawa 6:24
Alheri yă tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu da ƙauna marar ƙarewa.


Filibbiyawa 1:2
Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu, su tabbata a gare ku.


Filibbiyawa 1:7
Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.


Filibbiyawa 1:29
Gama an yi muku alheri, cewa ba gaskatawa da Almasihu kawai za ku yi ba, har ma za ku sha wuya dominsa,


Filibbiyawa 4:23
Alherin Ubangiji Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.


Kolossiyawa 1:2
zuwa ga tsarkaka da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi. Alheri da salamar Allah Ubanmu su tabbata a gare ku.


Kolossiyawa 1:6
wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.


Kolossiyawa 4:18
Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna. Ku tuna da ɗaurina. Alheri yă tabbata a gare ku.


1 Tessalonikawa 1:1
Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikkilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah uba da Ubangiji Yesu Almasihu. Alheri da salama su tabbata a gare ku.


1 Tessalonikawa 3:6
Amma ga shi, a yanzu da Timoti ya dawo daga wurinku, ya yi mana albishir a kan bangaskiyarku da ƙaunarku, da kuma yadda kuke tunawa da mu da alheri a koyaushe, har kuna begen ganinmu, kamar yadda mu ma muke yi.


1 Tessalonikawa 5:28
Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.


2 Tessalonikawa 1:2
Alheri da salama na Allah Uba, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.


2 Tessalonikawa 1:12
don a ɗaukaka sunan Ubangijinmu Yesu a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu.


2 Tessalonikawa 2:16
To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta'aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa,


2 Tessalonikawa 3:18
Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku duka.


1 Timoti 1:2
zuwa ga Timoti, ɗana na hakika, ta wajen bangaskiya. Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.


1 Timoti 1:14
Alherin Ubangijinmu kuma ya kwararo mini ƙwarai da gaske, a game da bangaskiya, da kuma ƙaunar da take ga Almasihu Yesu.


1 Timoti 3:2
To, lalle ne mai kula da ikkilisiya yă zama marar abin zargi, yă zama mai mace ɗaya, mai kamunkai, natsattse, kintsattse, mai yi wa baƙi alheri, gwanin koyarwa kuma.


1 Timoti 5:4
In wata gwauruwa tana da 'ya'ya ko jikoki, sai su koya, ya wajaba su fara nuna wa danginsu bautar Allah da suke yi, su kuma sāka wa iyayensu da alheri. Wannan abin karɓa ne a gun Allah.


1 Timoti 6:18
Sai dai su yi nagarta da bijinta a wajen aiki nagari, su kasance masu hannu sake, suna alheri.


1 Timoti 6:21
Waɗansu kuwa, a garin taƙama, da haka har sun kauce wa bangaskiya. Alheri yă tabbata a gare ku.


2 Timoti 1:2
zuwa ga Timoti ƙaunataccen ɗana. Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.


2 Timoti 1:9
wanda ya cece mu, ya kuma kira mu da kira mai tsarki, ba don wani aikin lada da muka yi ba, sai dai domin nufinsa, da kuma alherinsa, da aka yi mana baiwa tun fil'azal, a cikin Almasihu Yesu,


2 Timoti 2:1
Saboda haka, ya kai ɗana, sai ka ƙarfafa da alherin da yake ga Almasihu Yesu.


2 Timoti 4:22
Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.


Titus 1:4
zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen bangaskiyarmu mu duka. Alheri da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Mai Cetonmu su tabbata a gare ka.


Titus 1:8
Amma yă kasance mai yi wa baƙi alheri, mai son abu nagari, natsattse, mai kirki, tsarkakakke, mai kamunkai,


Titus 2:5
su kuma kasance natsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah.


Titus 2:11
Alherin Allah ya bayyana saboda ceton dukkan mutane,


Titus 3:4
Amma sa'ad da alherin Allah Mai Cetonmu da ƙaunarsa ga 'yan adam suka bayyana,


Titus 3:7
Wannan kuwa domin a kuɓutar da mu bisa ga alherinsa ne, mu kuma zama magāda masu bege ga rai madawwami.


Titus 3:15
Duk waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gayar mini da masoyanmu, masu bangaskiya. Alheri yă tabbata a gare ku, ku duka.


Filemon 1:3
Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.


Filemon 1:14
Amma ba na so in yi kome ba tare da yardarka ba, don kada alherinka yă zamana na tilas ne, ba na ganin dama ba.


Filemon 1:25
Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.


Ibraniyawa 2:9
Amma muna ganin Yesu, wanda a ɗan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, an naɗa shi da ɗaukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa. Wannan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa.


Ibraniyawa 4:16
Saboda haka, sai mu kusaci kursiyin Allah na alheri da amincewa, domin a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari.


Ibraniyawa 10:29
To mutumin da ya raina Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka tsarkake shi da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani kuke tsammani ya cancanta fiye da wancan?


Ibraniyawa 12:15
Ku kula fa, kada kowa yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka,


Ibraniyawa 13:2
Kada ku daina yi wa baƙi alheri, gama ta haka ne waɗansu suka sauki mala'iku ba da sani ba.


Ibraniyawa 13:9
Kada baƙuwar koyarwa iri iri ta bauɗar da ku, ai, abu ne mai kyau alherin Allah ya zamana shi yake ƙarfafa zuciya, ba abinci iri iri ba, waɗanda ba su amfani ga masu dogara da su.


Ibraniyawa 13:16
Kada kuwa ku daina yin alheri da gudunmawa, domin irin waɗannan su ne suke faranta wa Allah rai.


Yaƙub 3:17
Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.


Yaƙub 4:6
Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali'u alheri.”


1 Bitrus 1:2
su da suke zaɓaɓɓu bisa ga rigyasanin Allah Uba, waɗanda Ruhu kuma ya tsarkake, domin su yi wa Yesu Almasihu biyayya, su kuma tsarkaka da jininsa. Alheri da salama su yawaita a gare ku.


1 Bitrus 1:10
Annabawan da suka yi annabci a kan alherin da zai zama naku, sun tsananta bin diddigi a kan wannan ceto,


1 Bitrus 1:13
Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu.


1 Bitrus 2:3
in dai kun ɗanɗana alherin Ubangiji.


1 Bitrus 2:12
Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.


1 Bitrus 3:10
Domin, “Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri, Sai ya kame bakinsa daga ɓarna, Ya kuma hana shi maganar yaudara.


1 Bitrus 4:10
Duk baiwar da mutum ya samu, yă yi amfani da ita ga kyautata wa ɗan'uwansa, a kan amintaccen mai riƙon amanar alherin Allah iri iri ne.


1 Bitrus 5:5
Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”


1 Bitrus 5:10
Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku.


1 Bitrus 5:12
Na rubuto muku wasiƙar nan a taƙaice ta hannun Sila, ɗan'uwa mai aminci, a yadda na ɗauke shi, domin in yi muku gargaɗi, in kuma sanar da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske, ku tsaya a gare shi da ƙarfi.


2 Bitrus 1:2
Alheri da salama su yawaita a gare ku, a wajen sanin Allah da Yesu Ubangijinmu


2 Bitrus 3:18
Amma ku ƙaru da alherin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu da kuma saninsa. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a yanzu, da kuma har abada. Amin! Amin!


2 Yohanna 1:3
Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uban, da kuma na Yesu Almasihu Ɗan Uban, za su tabbata a gare mu, da gaskiya da ƙauna.


Yahuda 1:4
Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Ruʼuya ta Yohanna 1:4
Daga Yahaya zuwa ga ikilisiyoyin nan bakwai da suke a ƙasar Asiya. Alheri da salama su tabbata a gare ku daga wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma a nan gaba, da kuma Ruhohin nan bakwai da suke a gaban kursiyinsa,


Ruʼuya ta Yohanna 22:21
Alherin Ubangiji Yesu yă tabbata ga dukkan tsarkaka. Amin!


Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010