A A A A A


Bincika

Mattiyu 3:15
Amma Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin haka ne ya dace mu cika dukan adalci.” Sa'an nan Yahaya ya yardar masa.


Mattiyu 5:6
“Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.


Mattiyu 5:10
“Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin Sama nasu ne.


Mattiyu 5:20
Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”


Mattiyu 5:45
domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.


Mattiyu 6:33
Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.


Mattiyu 9:13
Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba.’ Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi.”


Mattiyu 13:43
Sa'an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”


Mattiyu 13:49
Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala'iku za su fito, su ware mugaye daga masu adalci,


Mattiyu 21:32
Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”


Mattiyu 25:37
Sa'an nan ne masu adalci za su amsa masa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa muka cishe ka, ko kuwa da ƙishirwa muka shayar da kai?


Mattiyu 25:46
Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”


Mattiyu 27:24
Da Bilatus ya ga bai rinjaye su ba, sai dai hargitsi yana shirin tashi, sai ya ɗibi ruwa ya wanke hannunsa a gaban jama'a, ya ce, “Ni kam, na kuɓuta daga alhakin jinin mai adalcin nan. Wannan ruwanku ne.”


Markus 2:17
Da Yesu ya ji haka, ya ce musu, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai masu zunubi.”


Luka 1:6
Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.


Luka 1:75
Sai dai da tsarki da adalci a gabansa, Dukan iyakar kwanakin nan namu.


Luka 5:32
Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi, su tuba.”


Luka 7:29
Da duk jama'a da masu karɓar haraji suka ji haka, suka tabbata Allah mai adalci ne, aka yi musu baftisma da baftismar Yahaya.


Luka 14:14
za ka kuwa sami albarka, da yake ba su da hanyar sāka maka. Sai kuwa a sāka maka ranar tashin masu adalci.”


Luka 18:9
Sai kuma ya ba da misalin nan ga waɗansu masu amince wa kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, ya ce,


Luka 18:11
Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu'a ga kansa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan.


Luka 20:20
Sai suka yi ta haƙwansa, suka aiki 'yan rahoto, su kuwa suka nuna kamar su masu adalci ne, da nufin su kama shi a maganarsa, su kuma ba da shi ga mai mulki ya hukunta shi.


Yohanna 5:30
“Ba na iya yin kome ni kaɗai. Yadda nake ji, haka nake yin hukunci. Hukuncina kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.


Yohanna 7:24
Kada ku yi hukunci da zato, amma ku yi hukunci da adalci.”


Yohanna 16:8
Sa'ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.


Yohanna 16:10
a kan adalci, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba.


Yohanna 17:25
Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta san ka ba, amma ni na san ka, waɗannan kuma sun sani kai ne ka aiko ni.


Ayyukan Manzanni 3:14
Amma ku kuka ƙi Mai Tsarkin nan, mai adalci kuka roƙa a saukar muku da mai kisankai,


Ayyukan Manzanni 7:52
A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,


Ayyukan Manzanni 10:35
amma a kowace al'umma duk mai tsoronsa, mai kuma aikata adalci, abin karɓuwa ne a gare shi.


Ayyukan Manzanni 13:10
ya ce, “Kai babban maha'inci, munafiƙi, ɗan Iblis, magabcin adalci duka, ba za ka daina karkata miƙaƙƙun hanyoyin Ubangiji ba?


Ayyukan Manzanni 17:31
tun da yake ya tsai da ranar da zai yi wa duniya shari'a, shari'a adalci, ta wurin mutumin nan da ya sa, wannan kuwa ya tabbatar wa dukan mutane, da ya tashe shi daga matattu.”


Ayyukan Manzanni 22:14
Sai ya ce, ‘Allahn kakanninmu ya zaɓe ka don kă san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji jawabi daga bakinsa.


Ayyukan Manzanni 24:15
Ina sa zuciya ga Allah, yadda su waɗannan ma suke sawa, wato za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.


Ayyukan Manzanni 24:25
Bulus yana ba da bayani a kan adalci, da kamunkai, da kuma hukuncin nan mai zuwa, Filikus ya kaɗu, ya kāda baki ya ce, “Yanzu kam, sai ka koma. In na sami zarafi nā kira ka.”


Romawa 1:17
Gama bishara ɗin ta bayyana wata hanyar samun adalci a gaban Allah, hanyar nan kuwa ta bangaskiya ce, tun daga farko har zuwa ƙarshe, yadda yake a rubuce cewa, “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.”


Romawa 1:29
Su masu aikata rashin adalci ne ƙwarai, da mugunta, da kwaɗayi, da ƙeta. Masu hassada ne, da kisankai, da jayayya, da ha'inci, da kuma nukura gaya matuƙa. Macizan ƙaiƙayi ne,


Romawa 2:8
Waɗanda suke masu sonkai, da waɗanda suke ƙin bin gaskiya, da masu bin rashin adalci, zai saka musu da fushi da hasala.


Romawa 3:4
A'a, ko kusa! A dai tabbata Allah mai gaskiya ne, ko da yake kowane mutum maƙaryaci ne, yadda yake a rubuce cewa, “Don maganarka tă tabbatar da adalcinka, Ka kuma yi rinjaye in an binciki al'amarinka.”


Romawa 3:5
In kuwa rashin adalcinmu shi ne yake nuna adalcin Allah a fili, me za mu ce? in Allah ya hore mu, ya yi rashin adalci ke nan? (Misali nake yi kawai.)


Romawa 3:10
Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya,


Romawa 3:21
A yanzu, ba kuwa a game da shari'a ba, an bayyana wata hanyar samun adalcin Allah, wadda ma Attaura da littattafan annabawa suke yi wa shaida.


Romawa 3:22
Adalcin nan na Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya ga Yesu Almasihu, na masu ba da gaskiya ne dukka, ba kuwa wani bambamci,


Romawa 3:25
Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa ya yi haka domin yă nuna adalcinsa ne, domin dā saboda haƙurinsa ya jingine zunuban da aka gabatar,


Romawa 3:26
domin a nuna adalcinsa a wannan zamani, wato a bayyana shi kansa mai adalci ne, mai kuɓutar da duk mai gaskatawa da Yesu kuma.


Romawa 4:3
To, me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi.”


Romawa 4:5
Wanda ba ya aikin lada, amma yana dogararsa ga Allah, wanda yake kuɓutar da masu laifi, akan lasafta bangaskiyar nan tasa adalci ce.


Romawa 4:6
Haka kuma Dawuda ya yi maganar albarkar da aka yi wa mutumin da Allah yake lasafta adalci a gare shi, ba don ya yi aikin lada ba,


Romawa 4:9
To, wannan albarka, masu kaciya ne kawai ake yi wa, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Gama abin da muke cewa shi ne, “Aka lasafta bangaskiyar Ibrahim adalci ce a gare shi.”


Romawa 4:11
Kaciyar da aka yi masa alama ce, wato tabbatacciyar shaida ce ta samun adalci, albarkacin bangaskiyar da yake da ita tun ba a yi masa kaciya ba. Wannan kuwa, domin yă zama uban dukkan masu ba da gaskiya ne, domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba,


Romawa 4:13
Alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa, cewa zai zama magājin duniya, ba ta Shari'a aka yi masa ba, amma domin ya ba da gaskiya ne, shi ya sa Allah ya karɓe shi mai adalci ne.


Romawa 4:22
Shi ya sa aka lasafta bangaskiyarsa adalci ce a gare shi.


Romawa 5:7
Da ƙyar za a sami wanda zai ba da ransa, saboda mutum mai adalci, ko da yake watakila saboda mutum mai nagarta wani ma sai yă yi kasai da ransa.


Romawa 5:17
In kuwa saboda laifin mutum ɗayan nan ne mutuwa ta yi mallaka ta wurinsa, ashe kuwa, waɗanda suke samun alherin nan mayalwaci, da kuma baiwar nan ta adalcin Allah, sai su yi mallaka fin haka ƙwarai a cikin rai, ta wurin ɗayan nan, wato Yesu Almasihu.


Romawa 5:18
To, kamar yadda laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa dukan mutane hukunci, haka kuma aikin adalci na Mutum ɗayan nan ya zama wa dukan mutane sanadin kuɓuta zuwa rai.


Romawa 5:19
Kamar yadda masu ɗumbun yawa suka zama masu zunubi ta wurin rashin biyayyar mutum ɗaya, haka kuma ta wurin biyayyar Mutum ɗaya za a mai da masu ɗumbun yawa masu adalci.


Romawa 5:21
Wato kamar yadda mallakar zunubi mutuwa ce, haka mallakar Allah ta wurin alheri adalci ce, da take bi da mu zuwa rai madawwami ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu.


Romawa 6:13
Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna miƙa gaɓoɓinku ga Allah kayan aikin adalci.


Romawa 6:16
Ba ku sani ba, shi wanda kuke miƙa kanku a gare shi domin yi wa biyayya, lalle ku bayi ne na wanda kuke yi wa biyayya ɗin (ko bautar zunubi wanda ƙarshensa mutuwa ne, ko bautar biyayya wadda ƙarshenta adalci ce)?


Romawa 6:18
Da aka 'yanta ku kuma daga bautar zunubi, kun zama bayin aikin adalci.


Romawa 6:19
Mai da magana nake yi irin ta yau da kullum, saboda rarraunar ɗabi'arku. Wato, kamar yadda dā can kuka miƙa gaɓoɓinku ga bautar rashin tsarki, da mugun aiki a kan mugun aiki, haka kuma a yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar aikin adalci, domin aikata tsarkakan ayyuka.


Romawa 6:20
Sa'ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci.


Romawa 8:10
In kuwa Almasihu yana a zuciyarku, ba ruwan jikinku da zunubi ke nan, Ruhu kuwa rai ne a gare ku saboda kun sami adalcin Allah.


Romawa 9:14
To, me kuma za mu ce? Allah ya yi rashin adalci ke nan? a'a, ko kusa!


Romawa 9:30
To, me kuma za mu ce? Ga shi, al'ummai da ba su nace da neman adalcin Allah ba, sun samu, wato, sun sami adalcin da yake daga bangaskiya.


Romawa 9:31
Isra'ila kuwa da suka nace da neman hanyar adalcin Allah, suka kasa samunta.


Romawa 10:3
Don saboda rashin fahimtar hanyar samun adalci, wadda Allah ya tanadar, da kuma neman kafa tāsu hanya, sai suka ƙi bin ita wannan hanya ta samun adalci wadda Allah ya tanadar.


Romawa 10:4
Domin Almasihu shi ne cikamakin Shari'a, domin kowane mai ba da gaskiya yă sami adalcin Allah.


Romawa 10:5
Gama Musa ya rubuta zancen adalcin da yake samuwa ta wurin bin Shari'a, cewa mai iya aikata ta zai rayu ta wurinta.


Romawa 10:6
Amma, a game da samun adalcin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya ya ce, Kada ka ce a ranka, “Wa zai hau zuwa sama?” Wato, yă sauko da Almasihu.


Romawa 10:10
Domin da zuci mutum yake gaskatawa yă sami adalcin Allah, da baki yake shaidawa yă sami ceto.


Romawa 14:17
Ai, Mulkin Allah ba ga al'amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


1 Korintiyawa 1:30
Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.


1 Korintiyawa 6:1
In waninku yana da wata ƙara a game da ɗan'uwansa, ashe, zai yi ƙurun kai maganar a gaban marasa adalci, ba a gaban tsarkaka ba?


1 Korintiyawa 6:9
Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,


1 Korintiyawa 15:34
Ku farka daga magagi, ku kama aikin adalci, ku daina yin zunubi. Waɗansu kam, ba su da sanin Allah. Na faɗi wannan ne don ku kunyata.


2 Korintiyawa 3:9
Gama idan hidimar da take jawo hukunci abar ɗaukakawa ce, to, lalle hidimar da take jawo samun adalcin Allah ta fi ta ɗaukaka nesa.


2 Korintiyawa 5:21
Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


2 Korintiyawa 6:7
da maganar gaskiya, da kuma ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu.


2 Korintiyawa 6:14
Kada ku yi cuɗanya marar dacewa da marasa ba da gaskiya. To, me ya haɗa aikin adalci da na mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?


2 Korintiyawa 11:15
Don haka, ba abin mamaki ba ne in bayinsa ma sun mai da kansu kamar su bayi ne na aikin adalci. A ƙarshe za a saka musu gwargwadon ayyukansu.


Galatiyawa 2:21
Ba na tozarta alherin Allah. Don da ta wurin bin Shari'a ake samun adalcin Allah, ashe, da Almasihu ya mutu a banza ke nan.”


Galatiyawa 3:6
Haka ma Ibrahim “ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma, aka lasafta ta adalci ce a gare shi.”


Galatiyawa 3:11
To, a fili yake, ba mai samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, domin “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.”


Galatiyawa 3:21
Wato, Shari'a ta zama saɓanin alkawaran Allah ke nan? A'a, ko kusa! Domin da an ba da wata shari'a mai iya ba da rai, da sai a sami adalcin Allah ta hanyar bin Shari'ar nan.


Galatiyawa 5:5
Gama mu, ta wurin ikon Ruhu, muke ɗokin cikar begen nan namu na samun adalcin Allah saboda bangaskiya.


Afisawa 4:24
ku ɗauki sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.


Afisawa 5:9
domin haske shi ne yake haifar duk abin da yake nagari, na adalci, da na gaskiya.


Afisawa 6:14
Saboda haka fa ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku,


Filibbiyawa 1:11
kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.


Filibbiyawa 3:6
a wajen himma kuwa mai tsananta wa Ikkilisiya ne ni, wajen aikin adalci kuwa bisa ga tafarkin Shari'a, marar abin zargi nake.


Filibbiyawa 3:9
a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina ba, wanda ya danganta da bin Shari'a, sai dai da adalcin nan wanda yake tsirowa daga bangaskiya ga Almasihu, wato, da adalcin nan wanda yake samuwa daga Allah ta wurin bangaskiya.


1 Tessalonikawa 2:10
Ku shaidu ne, haka kuma Allah, game da irin halin da muka nuna muku, ku masu ba da gaskiya, wato halin tsarki da na adalci da na rashin aibu.


2 Tessalonikawa 1:5
Wannan kuwa ita ce tabbatar hukunci mai adalci na Allah, domin a lasafta ku a cikin waɗanda suka cancanci zama a Mulkin Allah, wanda kuke shan wuya dominsa,


2 Tessalonikawa 1:6
domin kuwa Allah ya ga adalci ne, yă yi sakamokon ƙunci ga waɗanda suke ƙuntata muku,


1 Timoti 1:9
yana kuma tunawa, cewa ita Shari'a ba a kafa ta domin masu adalci ba, sai dai kangararru, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,


1 Timoti 6:11
Amma, ya kai, bawan Allah, ka guje wa waɗannan abubuwa, ka dimanci aikin adalci, da bin Allah, da bangaskiya, da ƙauna, da jimiri, da kuma tawali'u.


2 Timoti 2:22
Don haka, sai ka guje wa mugayen sha'awace-sha'awacen ƙuruciya, ka dimanci aikin adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma salama, tare da waɗanda suke roƙon Ubangiji da zuciya tsarkakakkiya.


2 Timoti 3:16
Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci,


2 Timoti 4:8
Saura kuwa, sai sakamakon nan na aikin adalci, da aka tanadar mini, wanda Ubangiji, mahukunci mai adalci, zai ba ni a ranar nan, ba kuwa ni kaɗai ba, har da duk waɗanda suke ɗokin ganin bayyanarsa.


Titus 2:12
yana koya mana mu ƙi rashin bin Allah da mugayen sha'awace-sha'awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyar nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah,


Titus 3:5
sai ya cece mu, ba don wani aikin adalci da mu muka yi ba, a'a, sai dai domin jinƙan nan nasa, albarkacin wankan nan na sāke haihuwa, da kuma sabuntawar nan ta Ruhu Mai Tsarki,


Ibraniyawa 1:9
Kā ƙaunaci aikin adalci, kā ƙi aikin sāɓo. Saboda haka Allah, wato, Allahnka, ya shafe ka Da man farin ciki fiye da tsararrakinka.”


Ibraniyawa 5:13
Ai, duk wanda yake nono ne abincinsa, bai ƙware da maganar adalci ba, kamar jariri yake.


Ibraniyawa 6:10
Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.


Ibraniyawa 7:2
Shi ne kuwa Ibrahim ya ba shi ushirin kome. Da farko dai, kamar yadda ma'anar sunansa take, shi sarkin adalci ne, sa'an nan kuma Sarkin Urushalima ne, wato, sarkin salama.


Ibraniyawa 11:4
Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadaya mafi kyau a kan Kayinu, ta wurin wannan bangaskiya ce ya kuma sami yardar Allah a kan shi mai adalci ne domin Allah ma ya shaide shi, da ya karɓi abubuwan da ya bayar. Ya mutu kam, amma ta wurin bangaskiyar nan tasa har ya zuwa yanzu yana magana.


Ibraniyawa 11:7
Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.


Ibraniyawa 11:33
waɗanda ta wurin bangaskiya suka ci masarautai, suka aikata adalci, suka sami cikar alkawarai, suka rurrufe bakunan zakoki,


Ibraniyawa 12:11
Ai, kowane irin horo, a lokacin shansa, abu ne mai baƙin ciki, ba na farin ciki ba. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.


Ibraniyawa 12:23
Kun iso taron farin ciki na kirayayyun 'ya'yan fari na Allah, waɗanda sunayensu suke a rubuce a Sama. Kun iso wurin Allah, wanda yake shi ne mai yi wa kowa shari'a, da kuma wurin ruhohin mutane masu adalci, waɗanda aka kammala.


Yaƙub 1:20
don fushin mutum ba ya aikata adalci.


Yaƙub 2:23
Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi,” aka kuma kira shi aminin Allah.


Yaƙub 3:18
Daga irin salama wanda masu sulhuntawa suke shukawa akan girbe adalci.


Yaƙub 5:6
Kun hukunta mai adalci, kun kuma kashe shi, bai kuwa yi muku tsayayya ba.


Yaƙub 5:16
Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.


1 Bitrus 2:23
Da aka zage shi bai rama ba, da ya sha wuya kuma bai yi kashedi ba, sai dai ya dogara ga mai shari'ar adalci.


1 Bitrus 2:24
Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.


1 Bitrus 3:12
Gama Ubangiji yana lura da masu aikata adalci, Yana kuma sauraron roƙonsu. Amma Ubangiji yana gāba da masu aikata mugunta.”


1 Bitrus 3:18
Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.


2 Bitrus 1:1
Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.


2 Bitrus 2:5
tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa'azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa'ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,


2 Bitrus 2:8
(don kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa'ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci),


2 Bitrus 2:9
ashe kuwa, Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa daga gwaje-gwaje, ya kuma tsare marasa adalci a kan jiran hukunci, har ya zuwa ranar shari'a,


2 Bitrus 2:21
Da ba su taɓa sanin hanyar adalci tun da fari ba, da ya fiye musu, bayan sun san ta, sa'an nan su juya ga barin umarnin nan mai tsarki.


2 Bitrus 3:13
Amma bisa ga alkawarinsa muna jiran sababbin summai da sabuwar ƙasa a inda adalci zai yi zamansa.


1 Yohanna 1:9
In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci.


1 Yohanna 2:1
Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina rubuto muku wannan ne domin kada ku yi zunubi. In kuwa wani ya yi zunubi, muna da Mai Taimako a gun Uba, wato, Yesu Almasihu mai adalci.


1 Yohanna 2:29
Da yake kun san shi mai adalci ne, ku dai tabbata duk mai aikata adalci haifaffensa ne.


1 Yohanna 3:7
Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada fa kowa ya ɓad da ku. Shi wanda yake aikata adalci, mai adalci ne, kamar yadda Almasihu mai adalci ne.


1 Yohanna 3:10
Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.


1 Yohanna 5:17
Duk rashin adalci zunubi ne. Akwai kuma zunubin da ba na mutuwa ba.


Ruʼuya ta Yohanna 15:3
Suna raira waƙar da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda ake yi wa Ɗan Ragon nan, suna cewa, “Ayyukanka manya ne, masu banmamaki, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki! Hanyoyinka na adalci ne, na gaskiya ne kuma, Ya Sarkin al'ummai.


Ruʼuya ta Yohanna 15:4
Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji, Ya kuma ɗaukaka sunanka? Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki. Dukkan al'ummai za su zo su yi maka sujada, Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”


Ruʼuya ta Yohanna 16:5
Na kuwa ji mala'ikan ruwa yana cewa, “Kai mai adalci ne a hukuncin nan naka, Ya kai Mai Tsarki, wanda kake a yanzu, kake kuma a dā.


Ruʼuya ta Yohanna 16:7
Sai na ji wata murya a bagadin ƙona turare, tana cewa, “Hakika, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Hukuncinka daidai yake, na adalci ne kuma!”


Ruʼuya ta Yohanna 19:2
Don hukuncinsa daidai yake, na adalci ne, Ya hukunta babbar karuwar nan wadda ta ɓata duniya da fasikancinta, Ya kuma ɗauki fansar jinin bayinsa a kanta.”


Ruʼuya ta Yohanna 19:8
An yardar mata ta sa tufafin lallausan lilin mai ɗaukar ido, mai tsabta.” Lallausan lilin ɗin nan, shi ne aikin adalci na tsarkaka.


Ruʼuya ta Yohanna 19:11
Sai na ga sama ta dāre, sai ga wani farin doki! Mahayinsa kuwa ana ce da shi Amintacce, Mai Gaskiya, yana hukunci da adalci, yana kuma yaƙi.


Ruʼuya ta Yohanna 22:11
Marar gaskiya yă yi ta rashin gaskiyarsa, fajiri kuwa yă yi ta fajircinsa, adali kuwa yă yi ta aikata adalcinsa, wanda yake tsattsarka kuwa ya yi ta zamansa na tsarki.”


Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010