A A A A A


Bincika

Mattiyu 3:17
Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.”


Mattiyu 12:18
“Ga barana wanda na zaɓa! Ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Zan sa masa Ruhuna, zai kuma sanar da al'ummai hanyar gaskiya.


Mattiyu 17:5
Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”


Markus 1:11
Aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai.”


Markus 9:7
Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena. Ku saurare shi.”


Luka 3:22
Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa da wata kama, kamar kurciya. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai,”


Luka 20:13
Sai mai garkar ya ce, ‘Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa.’


Romawa 16:5
Ku kuma gai da ikilisiyar da take taruwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccena Abainitas, wanda yake shi ne ya fara bin Almasihu a ƙasar Asiya.


Romawa 16:8
Ku gai da Amfiliyas, ƙaunataccena a cikin Ubangiji.


Romawa 16:9
Ku gai da Urbanas abokin aikinmu a cikin Almasihu, da kuma ƙaunataccena Istakis.


1 Korintiyawa 4:17
Saboda haka, na aika muku da Timoti, wanda yake shi ne ɗana ƙaunatacce, amintacce kuma a cikin Ubangiji, zai kuwa tuna muku da ka'idodina na bin Almasihu, kamar yadda nake koyarwa a ko'ina, a kowace ikkilisiya.


Afisawa 1:6
domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa.


Afisawa 6:21
A yanzu kuwa, don ku ma ku san lafiyata, da kuma halin da nake a ciki, ga Tikikus, ƙaunataccen ɗan'uwa, amintaccen mai hidimar Ubangiji, zai sanar da ku kome.


Kolossiyawa 1:7
Haka ma kuka koya wurin Abafaras, ƙaunataccen abokin bautarmu. Shi amintaccen mai hidima ne na Almasihu a madadinmu,


Kolossiyawa 1:13
Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,


Kolossiyawa 4:7
Tikikus zai sanar da ku duk abin da nake ciki. Shi ƙaunataccen ɗan'uwa ne, amintaccen mai hidima, abokin bautarmu kuma a cikin Ubangiji.


Kolossiyawa 4:9
Ga kuma Unisimas a nan tare da shi, amintaccen ɗan'uwa ƙaunatacce, wanda shi ma a cikinku yake. Su za su gaya muku duk abin da ya faru a nan.


Kolossiyawa 4:14
Luka, ƙaunataccen likitan nan, da Dimas suna gaishe ku.


2 Timoti 1:2
zuwa ga Timoti ƙaunataccen ɗana. Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.


Filemon 1:1
Daga Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu, da kuma Timoti ɗan'uwanmu, zuwa ga Filiman ƙaunataccen abokin aikinmu,


2 Bitrus 1:17
Domin sa'ad da Allah Uba ya girmama shi, ya kuma ɗaukaka shi, sai murya ta zo masa daga mafificiyar ɗaukaka cewa, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai,”


2 Bitrus 3:15
Ku ɗauki haƙurin Ubangijinmu, ceto ne. Haka ma, ƙaunataccen ɗan'uwanmu Bulus ya rubuto muku, bisa ga hikimar da aka ba shi,


3 Yohanna 1:1
Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga Gayus, ƙaunatacce, wanda nake ƙauna da gaske.


3 Yohanna 1:2
Ya ƙaunataccena, ina addu'a kă sami zaman lafiya ta kowace hanya da kuma lafiya jiki, kamar yadda ruhunka yake a zaune lafiya.


3 Yohanna 1:5
Ya ƙaunataccena, duk abin da kake yi wa 'yan'uwa, aikin bangaskiya kake yi, tun ba ma ga baƙi ba.


3 Yohanna 1:11
Ya ƙaunataccena, kada ka kwaikwayi mugun aiki, sai dai nagari. Kowa da yake aikin nagari na Allah ne. Mai mugun aiki kuwa bai san Allah ba sam.


Ruʼuya ta Yohanna 20:9
Sai kuma su bazu, su mamaye duk duniya, su yi wa sansanin tsarkaka da ƙaunataccen birni ƙawanya, sai wuta ta zubo daga sama ta lashe su.


Hausa Bible 2010
Bible Society of Nigeria © 1932/2010