A A A A A
Facebook Instagram Twitter
Hausa Bible 2013

Luka 51
Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah,
2
sai ya hangi jiragen ruwa biyu a bakin tafkin, waɗanda masu kamun kifi suka bari suna wankin tarunsu.
3
Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yǎ tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki.
4
Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da tarunka ka kama kifi.”
5
Siman ya amsa, ya ce, “Ranka yǎ daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki tarun.”
6
Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har tarunsu suka fara tsintsinkewa.
7
Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa.
8
Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu, ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!”
9
Gama mamaki ya kama shi da abokansa duka, saboda yawan kifin da suka kama.
10
Yaƙub da Yohanna, ʼyaʼyan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.”
11
Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi.
12
Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi, ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtace ni.”
13
Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin, ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.
14
Sai Yesu ya umarce shi, ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.”
15
Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu.
16
Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yǎ yi adduʼa.
17
Wata rana, da yake cikin koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki waɗanda suka zo daga kowane ƙauye a Galili, Yahudiya da Urushalima kuwa suna zaune. Ikon Ubangiji yana nan don yǎ warkar da masu ciwo.
18
Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu.
19
Da suka ga babu hanyar da za su yi bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu.
20
Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Aboki, an gafarta maka zunubanka.”
21
Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”
22
Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya, ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku?
23
Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?
24
Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”
25
Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.
26
Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.”
27
Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.”
28
Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi.
29
Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su.
30
Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da ‘masu zunubi’?”
31
Yesu ya amsa musu, ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
32
Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”
33
Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da adduʼa, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.”
34
Yesu ya amsa, ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su?
35
Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.”
36
Sai ya faɗa musu wannan misali, ya ce, “Ba wanda yakan yage ƙyale daga sabuwar riga ya yi wa tsohuwar riga faci. In ya yi haka, zai yage sabuwar rigar, kuma facin daga sabuwar ba zai dace da tsohuwar rigar ba.
37
Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yǎ zube, salkunan kuma su lalace.
38
Aʼa, sai dai a zuba sabon ruwan inabi a sababbin salkuna.
39
Kuma ba wanda yakan so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, don yakan ce, ‘Ai, tsohon ya fi kyau.’ ”Luka 5:1
Luka 5:2
Luka 5:3
Luka 5:4
Luka 5:5
Luka 5:6
Luka 5:7
Luka 5:8
Luka 5:9
Luka 5:10
Luka 5:11
Luka 5:12
Luka 5:13
Luka 5:14
Luka 5:15
Luka 5:16
Luka 5:17
Luka 5:18
Luka 5:19
Luka 5:20
Luka 5:21
Luka 5:22
Luka 5:23
Luka 5:24
Luka 5:25
Luka 5:26
Luka 5:27
Luka 5:28
Luka 5:29
Luka 5:30
Luka 5:31
Luka 5:32
Luka 5:33
Luka 5:34
Luka 5:35
Luka 5:36
Luka 5:37
Luka 5:38
Luka 5:39


Luka 1 / Luk 1
Luka 2 / Luk 2
Luka 3 / Luk 3
Luka 4 / Luk 4
Luka 5 / Luk 5
Luka 6 / Luk 6
Luka 7 / Luk 7
Luka 8 / Luk 8
Luka 9 / Luk 9
Luka 10 / Luk 10
Luka 11 / Luk 11
Luka 12 / Luk 12
Luka 13 / Luk 13
Luka 14 / Luk 14
Luka 15 / Luk 15
Luka 16 / Luk 16
Luka 17 / Luk 17
Luka 18 / Luk 18
Luka 19 / Luk 19
Luka 20 / Luk 20
Luka 21 / Luk 21
Luka 22 / Luk 22
Luka 23 / Luk 23
Luka 24 / Luk 24