A A A A A
×

Hausa Bible 2013

2 Bitrus 1

1
Wasiƙa daga Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kiristi. Zuwa ga waɗanda ta wurin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi sun sami bangaskiya mai daraja irin tamu:
2
Alheri da salama su zama naku a yalwace ta wurin sanin Allah da Yesu Ubangijinmu.
3
Ikonsa na Allahntaka ya ba mu kome da muke bukata don rayuwa da kuma tsoron Allah ta wurin sanin wanda ya kira mu ta wurin ɗaukakarsa da nagartarsa.
4
Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen shaʼawace-shaʼawace suke jawowa.
5
Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani;
6
ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara masa ɗaurewa; ga ɗaurewa kuwa ku ƙara mata tsoron Allah;
7
ga tsoron Allah kuma ku ƙara masa nuna alheri ga ʼyanʼuwa; ga nuna alheri ga ʼyanʼuwa kuma ku ƙara masa ƙauna.
8
Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi.
9
Amma in wani ba shi da su, ba shi da hangen nesa ke nan kuma makaho ne, ya kuma manta cewa an tsarkake shi daga zunubansa na dā.
10
Saboda haka ʼyanʼuwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba,
11
za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.
12
Saboda haka kullum zan tuna muku da waɗannan, ko da yake kun sansu kun kuma kahu ƙwarai cikin gaskiyar da kuke da ita yanzu.
13
A ganina ya dace in tunashe ku muddin ina raye cikin tentin wannan jiki,
14
domin na sani na kusa in ajiye shi a gefe, yadda Ubangijinmu Yesu Kiristi ya nuna mini a sarari.
15
Zan kuwa yi iyakacin ƙoƙari in ga cewa bayan rabuwata kullum za ku iya tuna da waɗannan abubuwa.
16
Ba mu bi tatsuniyoyin da aka ƙaga da wayo saʼad da muka gaya muku game da ikon Ubangijinmu Yesu Kiristi da zuwansa ba, sai dai mu shaidu ne na ɗaukakarsa mai girma da muka gani da ido.
17
Gama ya sami girma da ɗaukaka daga Allah Uba saʼad da murya ta zo masa daga Mafificiyar Ɗaukaka, cewa, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; da shi nake jin daɗi ƙwarai.”
18
Mu kanmu mun ji wannan muryar da ta zo daga sama saʼad da muke tare da shi a kan dutse mai tsarki.
19
Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yǎ zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku.
20
Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa.
21
Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.
2 Bitrus 1:1
2 Bitrus 1:2
2 Bitrus 1:3
2 Bitrus 1:4
2 Bitrus 1:5
2 Bitrus 1:6
2 Bitrus 1:7
2 Bitrus 1:8
2 Bitrus 1:9
2 Bitrus 1:10
2 Bitrus 1:11
2 Bitrus 1:12
2 Bitrus 1:13
2 Bitrus 1:14
2 Bitrus 1:15
2 Bitrus 1:16
2 Bitrus 1:17
2 Bitrus 1:18
2 Bitrus 1:19
2 Bitrus 1:20
2 Bitrus 1:21
2 Bitrus 1 / 2Bit 1
2 Bitrus 2 / 2Bit 2
2 Bitrus 3 / 2Bit 3