1 |
Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ʼyaʼya |
2 |
ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu ya kuma ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah. |
3 |
Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da tsarkaka ba. |
4 |
Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya. |
5 |
Ku dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah. |
6 |
Kada wani yǎ ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya. |
7 |
Saboda haka kada ku haɗa kai da su. |
8 |
Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku cika da haske daga Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ʼyaʼyan haske |
9 |
(domin amfanin haske ya kunshi nagarta, adalci da kuma gaskiya) |
10 |
ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji. |
11 |
Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su. |
12 |
Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye. |
13 |
Amma haske zai tona yadda ainihin waɗannan abubuwa suke, |
14 |
gama haske ne yake sa kome yǎ bayyana. Shi ya sa aka ce: “Ka farka, Ya kai mai barci, ka tashi daga matattu, Kiristi kuwa zai haskaka ka.” |
15 |
Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku yi zama irin na marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. |
16 |
Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin mugaye ne. |
17 |
Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. |
18 |
Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. |
19 |
Ku yi zance da juna cikin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya. Ku rera ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. |
20 |
Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi kuna gode wa Allah Uba a ko mene ne. |
21 |
Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke yi wa Kiristi. |
22 |
Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku kamar ga Ubangiji. |
23 |
Gama miji shi ne kan mace yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. |
24 |
To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome. |
25 |
Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. |
26 |
Ya mai da ikkilisiya mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. |
27 |
Kiristi ya yi haka don yǎ miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma tsarki, marar aibi, marar tabo ko wani lahani. |
28 |
Ta haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa yana ƙaunar kansa ne. |
29 |
Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yǎ ciyar da shi, yǎ kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya— |
30 |
gama mu gaɓoɓin jikinsa ne. |
31 |
“Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yǎ manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.” |
32 |
Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya. |
33 |
Duk da haka, dole kowannenku yǎ ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar ta yi biyayya ga mijinta.
|
Hausa Bible 2013 |
Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc |
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
Afisawa 5:1 |
Afisawa 5:2 |
Afisawa 5:3 |
Afisawa 5:4 |
Afisawa 5:5 |
Afisawa 5:6 |
Afisawa 5:7 |
Afisawa 5:8 |
Afisawa 5:9 |
Afisawa 5:10 |
Afisawa 5:11 |
Afisawa 5:12 |
Afisawa 5:13 |
Afisawa 5:14 |
Afisawa 5:15 |
Afisawa 5:16 |
Afisawa 5:17 |
Afisawa 5:18 |
Afisawa 5:19 |
Afisawa 5:20 |
Afisawa 5:21 |
Afisawa 5:22 |
Afisawa 5:23 |
Afisawa 5:24 |
Afisawa 5:25 |
Afisawa 5:26 |
Afisawa 5:27 |
Afisawa 5:28 |
Afisawa 5:29 |
Afisawa 5:30 |
Afisawa 5:31 |
Afisawa 5:32 |
Afisawa 5:33 |
|
|
|
|
|
|
Afisawa 1 / Afi 1 |
Afisawa 2 / Afi 2 |
Afisawa 3 / Afi 3 |
Afisawa 4 / Afi 4 |
Afisawa 5 / Afi 5 |
Afisawa 6 / Afi 6 |