A A A A A
×

Hausa Bible 2013

Romawa 11

1
To, ina da tambaya: Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Israʼila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin.
2
Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Eliya ba-yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Israʼila ya ce:
3
“Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma nema su kashe ni”?
4
Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Baʼal sujada ba.”
5
Haka ma, a wannan zamani akwai ragowar da aka zaɓa ta wurin alheri.
6
In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga ayyuka ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.
7
To, sai me? Abin da Israʼila suka nema da himma ba su samu ba, amma zaɓaɓɓun suka samu. Sauran suka taurare,
8
kamar yadda yake a rubuce cewa: “Allah ya ba su ruhun ruɗewa, idanu don su kāsa gani, da kuma kunnuwa don su kāsa ji, har yǎ zuwa yau.”
9
Dawuda kuma ya ce: “Bari teburin cin abincinsu yǎ zama musu tarko, sanadin fāɗuwa da dutsen sa tuntuɓe da kuma ramuwa a kansu.
10
Bari idanunsu su duhunta don kada su iya gani, bayansu kuma yǎ tanƙware har abada.”
11
Har yanzu ina da tambaya: Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Alʼummai don a sa mutanen Israʼila su ji kishi.
12
Amma in laifinsu yana nufin albarka ga duniya, hasararsu kuma albarka ga Alʼummai, ina misalin yalwar da albarkunsu za su kawo!
13
Ina magana da ku ne fa Alʼummai. Tun da yake ni manzo ne ga Alʼummai, ina taƙama da aikin nan nawa,
14
da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yǎ sa in ceci waɗansunsu.
15
Gama in ƙinsu da aka yi ya zama sulhu ga duniya, me karɓarsu za ta zama in ba rai daga matattu ba?
16
In sashen da aka miƙa a matsayin nunan fari tsattsarka ne, to, sauran ma tsattsarka ne; in saiwar tsattsarka ce, to, sauran rassan ma tsattsarka ne.
17
In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan niʼimar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,
18
kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi laʼakari da wannan: Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka.
19
To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.”
20
Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro.
21
Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.
22
Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah: tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka.
23
In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su.
24
Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?
25
Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ʼyanʼuwa, domin kada ku ɗaga kai: Israʼila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Alʼummai masu yawa ya cika.
26
Ta haka kuwa za a ceci dukan Israʼila, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Mai ceto zai zo daga Sihiyona; zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.
27
Wannan kuwa shi ne alkawarina da su saʼad da na ɗauke musu zunabansu.”
28
Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu,
29
gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa.
30
Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu,
31
haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku.
32
Gama Allah ya ɗaure dukan mutane ga rashin biyayya don yǎ nuna jinƙai ga kowa.
33
Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace! Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike, hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!
34
“Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa yǎ ba shi shawara?”
35
“Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu, da Allah zai sāka masa?”
36
Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance. Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.
Romawa 11:1
Romawa 11:2
Romawa 11:3
Romawa 11:4
Romawa 11:5
Romawa 11:6
Romawa 11:7
Romawa 11:8
Romawa 11:9
Romawa 11:10
Romawa 11:11
Romawa 11:12
Romawa 11:13
Romawa 11:14
Romawa 11:15
Romawa 11:16
Romawa 11:17
Romawa 11:18
Romawa 11:19
Romawa 11:20
Romawa 11:21
Romawa 11:22
Romawa 11:23
Romawa 11:24
Romawa 11:25
Romawa 11:26
Romawa 11:27
Romawa 11:28
Romawa 11:29
Romawa 11:30
Romawa 11:31
Romawa 11:32
Romawa 11:33
Romawa 11:34
Romawa 11:35
Romawa 11:36
Romawa 1 / Rom 1
Romawa 2 / Rom 2
Romawa 3 / Rom 3
Romawa 4 / Rom 4
Romawa 5 / Rom 5
Romawa 6 / Rom 6
Romawa 7 / Rom 7
Romawa 8 / Rom 8
Romawa 9 / Rom 9
Romawa 10 / Rom 10
Romawa 11 / Rom 11
Romawa 12 / Rom 12
Romawa 13 / Rom 13
Romawa 14 / Rom 14
Romawa 15 / Rom 15
Romawa 16 / Rom 16