A A A A A
×

Hausa Bible 2013

Markus 15

1
Da sassafe, sai manyan firistoci tare da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka ɗaure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus.
2
Bilatus ya yi tambaya, ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”
3
Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa.
4
Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa, ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.”
5
Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.
6
Yanzu fa, alʼada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa.
7
Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ʼyan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.
8
Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yǎ yi musu abin da ya saba yi.
9
Bilatus ya yi tambaya, ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”
10
Don ya san saboda kishi ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.
11
Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.
12
Bilatus ya tambaye su, ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”
13
Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”
14
Bilatus ya yi tambaya, ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”
15
Don son yǎ faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, saʼan nan ya ba da shi a gicciye.
16
Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya.
17
Suka sa masa wata riga mai launin shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa.
18
Sai suka fara ce masa, “Ranka yǎ daɗe sarkin Yahudawa!”
19
Suka dinga bugunsa a ka da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa ban girma na baʼa.
20
Bayan da suka gama yin masa baʼa, suka tuɓe rigar mai launin shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.
21
Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yǎ ɗauki gicciyen.
22
Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai.)
23
Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yǎ rage zafi, amma bai sha ba.
24
Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuriʼa a kansu don su ga abin da kowa zai samu.
25
Saʼa ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi.
26
Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, “SARKIN YAHUDAWA.”
27
Suka gicciye ʼyan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.
28
***
29
Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku,
30
sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”
31
Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa baʼa a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa!
32
Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Israʼila, yǎ sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.
33
Daga saʼa ta shida har zuwa saʼa ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar.
34
A daidai saʼa ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” Wanda yake nufin, “Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?”
35
Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Eliya.”
36
Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yǎ sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Eliya zai zo yǎ saukar da shi.”
37
Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.
38
Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa.
39
Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”
40
Waɗansu mata suna ƙallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yosi, da kuma Salome.
41
A Galili waɗannan mata ne suka riƙa binsa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can.
42
Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye, (wato, ana washegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai
43
Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
44
Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu.
45
Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin.
46
Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, saʼan nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin.
47
Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yosi sun ga inda aka kwantar da shi.
Markus 15:1
Markus 15:2
Markus 15:3
Markus 15:4
Markus 15:5
Markus 15:6
Markus 15:7
Markus 15:8
Markus 15:9
Markus 15:10
Markus 15:11
Markus 15:12
Markus 15:13
Markus 15:14
Markus 15:15
Markus 15:16
Markus 15:17
Markus 15:18
Markus 15:19
Markus 15:20
Markus 15:21
Markus 15:22
Markus 15:23
Markus 15:24
Markus 15:25
Markus 15:26
Markus 15:27
Markus 15:28
Markus 15:29
Markus 15:30
Markus 15:31
Markus 15:32
Markus 15:33
Markus 15:34
Markus 15:35
Markus 15:36
Markus 15:37
Markus 15:38
Markus 15:39
Markus 15:40
Markus 15:41
Markus 15:42
Markus 15:43
Markus 15:44
Markus 15:45
Markus 15:46
Markus 15:47
Markus 1 / Mar 1
Markus 2 / Mar 2
Markus 3 / Mar 3
Markus 4 / Mar 4
Markus 5 / Mar 5
Markus 6 / Mar 6
Markus 7 / Mar 7
Markus 8 / Mar 8
Markus 9 / Mar 9
Markus 10 / Mar 10
Markus 11 / Mar 11
Markus 12 / Mar 12
Markus 13 / Mar 13
Markus 14 / Mar 14
Markus 15 / Mar 15
Markus 16 / Mar 16