A A A A A
×

Hausa Bible 2013

Markus 10

1
Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba.
2
Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya, cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yǎ saki matarsa?”
3
Ya amma ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”
4
Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yǎ rubuta takardar saki, yǎ kuma kore ta.”
5
Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka.
6
Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’
7
‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yǎ manne wa matarsa,
8
su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’ Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya.
9
Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yǎ raba.”
10
Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan.
11
Ya amma ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki.
12
In kuma ta saki mijinta ta auri wani, zina take yi.”
13
Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yǎ taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su.
14
Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.
15
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”
16
Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.
17
Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa, ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?”
18
Yesu ya amsa, ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari sai Allah kaɗai.
19
Ka dai san dokokin: ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”
20
Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.”
21
Yesu ya kalle shi da ƙauna, ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Saʼan nan ka zo ka bi ni.”
22
Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, domin yana da arziki sosai.
23
Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!”
24
Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “ʼYaʼyana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah!
25
Ya fi sauƙi raƙumi yǎ shiga ta kafar allura, da mai arziki yǎ shiga mulkin Allah.”
26
Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?”
27
Yesu ya kalle su, ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.”
28
Bitrus ya ce, “Mun bar kome domin mu bi ka!”
29
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ʼyanʼuwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ʼyaʼya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara,
30
saʼan nan yǎ kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, (na gidaje, da ʼyanʼuwa mata, da ʼyanʼuwa maza, da uwaye, da ʼyaʼya, da gonaki— amma tare da tsanani), a lahira kuma yǎ sami rai madawwami.
31
Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshen kuma za su zama na farko.”
32
Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna binsa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi.
33
Ya ce, “Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Alʼummai,
34
waɗanda za su yi masa baʼa, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yǎ tashi.”
35
Sai Yaƙub da Yohanna, ʼyaʼyan Zebedi maza suka zo wurinsa suka ce, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙa.”
36
Ya tambaye su, ya ce, “Me kuke so in yi muku?”
37
Suka amsa suka ce, “Ka bar ɗayanmu yǎ zauna a damarka, ɗayan kuma a hagunka, a cikin ɗaukakarka.”
38
Yesu ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya shan kwaf da zan sha, ko a yi muku baftisma da baftismar da aka yi mini?”
39
Suka ce, “Za mu iya.” Yesu ya ce musu, “Za ku sha kwaf da zan sha, kuma yi muku baftisma da aka yi mini,
40
amma zama a damana ko haguna, ba ni nake ba da izinin ba. Waɗannan wurare na waɗanda aka riga aka shirya musu ne.”
41
Da sauran goman suka ji wannan, sai suka yi fushi da Yaƙub da Yohanna.
42
Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin alʼummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko.
43
Ba haka ya kamata yǎ zama da ku ba. A maimakon, duk wanda yake so yǎ zama babba a cikinku, dole yǎ zama bawanku.
44
Duk wanda kuma yake so yǎ zama na farko, dole yǎ zama bawan kowa.
45
Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yǎ yi bauta, yǎ kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
46
Sai suka iso Yeriko. Saʼad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa, (wato, Ɗan Timawus), yana zaune a gefen hanya yana bara.
47
Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, “Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
48
Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yǎ yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana, cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
49
Yesu ya tsaya, ya ce, “Ku kira shi.” Sai suka kira makahon suka ce, “Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka.”
50
Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu.
51
Yesu ya tambaye shi, ya ce, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce, “Rabbi, ina so in sami ganin gari.”
52
Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.
Markus 10:1
Markus 10:2
Markus 10:3
Markus 10:4
Markus 10:5
Markus 10:6
Markus 10:7
Markus 10:8
Markus 10:9
Markus 10:10
Markus 10:11
Markus 10:12
Markus 10:13
Markus 10:14
Markus 10:15
Markus 10:16
Markus 10:17
Markus 10:18
Markus 10:19
Markus 10:20
Markus 10:21
Markus 10:22
Markus 10:23
Markus 10:24
Markus 10:25
Markus 10:26
Markus 10:27
Markus 10:28
Markus 10:29
Markus 10:30
Markus 10:31
Markus 10:32
Markus 10:33
Markus 10:34
Markus 10:35
Markus 10:36
Markus 10:37
Markus 10:38
Markus 10:39
Markus 10:40
Markus 10:41
Markus 10:42
Markus 10:43
Markus 10:44
Markus 10:45
Markus 10:46
Markus 10:47
Markus 10:48
Markus 10:49
Markus 10:50
Markus 10:51
Markus 10:52
Markus 1 / Mar 1
Markus 2 / Mar 2
Markus 3 / Mar 3
Markus 4 / Mar 4
Markus 5 / Mar 5
Markus 6 / Mar 6
Markus 7 / Mar 7
Markus 8 / Mar 8
Markus 9 / Mar 9
Markus 10 / Mar 10
Markus 11 / Mar 11
Markus 12 / Mar 12
Markus 13 / Mar 13
Markus 14 / Mar 14
Markus 15 / Mar 15
Markus 16 / Mar 16