English
A A A A A
×

Hausa Bible 2013

Mattiyu 6
1
“Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukan adalcinku’ a gaban mutane, domin su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba.
2
“Saboda haka saʼad da kake ba wa masu bukata, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majamiʼu da kuma kan tituna, don mutane su ba su girma. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun karɓi ladarsu cikakke.
3
Amma saʼad da kake ba wa masu bukata, kada ka yarda hannun hagunka yǎ ma san abin da hannun damarka yake yi,
4
don bayarwarka ta zama a ɓoye. Saʼan nan Ubanka mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
5
“Saʼad da kuma kuke adduʼa, kada ku zama kamar munafukai, gama sun cika son yin adduʼa a tsaye a cikin majamiʼu da kuma a bakin titi, don mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun karɓi ladarsu cikakke.
6
Amma saʼad da kake adduʼa, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi adduʼa ga Ubanka wanda ba a gani. Saʼan nan, Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
7
Saʼad da kuma kuke adduʼa, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu.
8
Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.
9
“To fa, ga yadda ya kamata ku yi adduʼa: “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama, a tsarkake sunanka,
10
mulkinka yǎ zo a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a sama.
11
Ka ba mu yau abincin yininmu.
12
Ka gafarta mana laifofinmu, kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.
13
Kada ka kai mu cikin jaraba, amma ka cece mu daga mugun nan. ’
14
Gama in kuna yafe wa mutane saʼad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku.
15
Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.
16
“Saʼad da kuma kuna azumi, kada ku ɓata fuska, yadda munafukai suke yi. Sukan ɓata fuskokinsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke.
17
Amma saʼad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka,
18
domin kada mutane su ga alama cewa kana azumi, sai dai ga Ubanka kaɗai wanda ba a gani; Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
19
“Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan yi fashi, su yi sata.
20
Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata, inda kuma ba ɓarayin da za su yi fashi, su yi sata.
21
Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za ta kasance.
22
“Ido shi ne fitilar jiki. In idanunka suna da kyau, dukan jikinka zai cika da haske.
23
Amma in idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma zai cika da duhu. To, in hasken da yake a cikinka duhu ne, duhun ya wuce misali ke nan!
24
“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yǎ ƙi ɗaya, yǎ ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yǎ yi aminci ga ɗaya, saʼan nan yǎ rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah ku kuma bauta wa Kuɗi gaba ɗaya.”
25
“Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba?
26
“Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba?
27
Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko saʼa ɗaya?
28
“Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa.
29
Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba.
30
In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, Ya ku masu ƙarancin bangaskiya?
31
Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’
32
Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu.
33
Sai dai da farko, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.
34
Saboda haka kada ku damu game da gobe, domin gobe zai damu da kansa. Kowace rana tana da isashiyar damuwarta.