A A A A A
×

Hausa Bible 2013

Mattiyu 26

1
Saʼad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa,
2
“Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu-za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”
3
Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist da ake kira Kayifas,
4
suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.
5
Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, in ba haka ba mai yiwuwa a yi hargitsi.”
6
Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu,
7
wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.
8
Saʼad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!
9
Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.”
10
Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.
11
Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba.
12
Saʼad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don janaʼizata.
13
Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi waʼazin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”
14
Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan-wanda ake kira Yahuda Iskariyot-ya je wurin manyan firistoci
15
ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin.
16
Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.
17
A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya, “Ina kake so mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
18
Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka’ ”
19
Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.
20
Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun.
21
Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
22
Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Ubangiji?”
23
Yesu ya amsa, ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni.
24
Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”
25
Saʼan nan Yahuda, wanda zai bashe shi, ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa, ya ce, “I, kai ne.”
26
Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”
27
Saʼan nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku.
28
Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.
29
Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”
30
Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
31
Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya sabili da ni, gama a rubuce yake cewa: “ ‘Zan bugi makiyayin, tumakin garken kuwa za su fasu.’
32
Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”
33
Bitrus ya amsa, ya ce, “Ko da duka sun ja da baya sabili da kai, ba zan taɓa ja da baya ba.”
34
Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
35
Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.
36
Saʼan nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi adduʼa.”
37
Ya ɗauki Bitrus da ʼyaʼya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu.
38
Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”
39
Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi adduʼa, ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”
40
Saʼan nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus, ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na saʼa guda ba?
41
Ku yi tsaro, ku kuma yi adduʼa, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”
42
Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi adduʼa, ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”
43
Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci.
44
Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi adduʼa sau na uku, yana maimaita iri abu guda.
45
Saʼan nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, saʼa ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi.
46
Ku tashi, mu tafi! Ga mai bashe ni nan yana zuwa!”
47
Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su.
48
To, mai bashe shi ɗin, ya riga ya shirya alama da su: “Wanda na yi masa sumba, shi ne mutumin; ku kama shi.”
49
Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Saʼan nan ya yi masa sumba.
50
Yesu ya amsa, ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.” Saʼan nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi.
51
Ganin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne.
52
Sai Yesu ya ce, masa, “Mai da takobinka kube, gama duk masu zare takobi, a takobi za su mutu.
53
Kuna tsammani ba zan iya kira Ubana, nan take kuwa yǎ aiko mini fiye da rundunar malaʼiku goma sha biyu ba?
54
Amma ta yaya za a cika Nassin da ya ce dole haka yǎ faru?”
55
A wannan lokaci sai Yesu ya ce wa taron, “Ina jagorar wani tawaye ne, da kuka fito da takuba da kuma sanduna don ku kama ni? Kowace rana ina zama a filin haikali ina koyarwa, ba ku kuwa kama ni ba.
56
Amma wannan duka ya faru ne don a cika rubuce rubucen annabawa.” Saʼan nan dukan almajiran suka yashe shi suka gudu.
57
Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru.
58
Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yǎ ga ƙarshen abin.
59
Sai manyan firistoci da ʼyan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.
60
Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito. A ƙarshe, biyu suka zo gaba,
61
suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”
62
Saʼan nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”
63
Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai: Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”
64
Sai Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka: Nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”
65
Saʼan nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon.
66
Me kuka gani?” Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”
67
Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi
68
suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”
69
To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu Bagalile.”
70
Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.”
71
Saʼan nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”
72
Ya sāke mūsu har da rantsuwa: yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”
73
Bayan ɗan lokaci, sai na tattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.”
74
Sai ya fara laʼantar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!” Nan da take, sai zakara ya yi cara.
75
Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.
Mattiyu 26:1
Mattiyu 26:2
Mattiyu 26:3
Mattiyu 26:4
Mattiyu 26:5
Mattiyu 26:6
Mattiyu 26:7
Mattiyu 26:8
Mattiyu 26:9
Mattiyu 26:10
Mattiyu 26:11
Mattiyu 26:12
Mattiyu 26:13
Mattiyu 26:14
Mattiyu 26:15
Mattiyu 26:16
Mattiyu 26:17
Mattiyu 26:18
Mattiyu 26:19
Mattiyu 26:20
Mattiyu 26:21
Mattiyu 26:22
Mattiyu 26:23
Mattiyu 26:24
Mattiyu 26:25
Mattiyu 26:26
Mattiyu 26:27
Mattiyu 26:28
Mattiyu 26:29
Mattiyu 26:30
Mattiyu 26:31
Mattiyu 26:32
Mattiyu 26:33
Mattiyu 26:34
Mattiyu 26:35
Mattiyu 26:36
Mattiyu 26:37
Mattiyu 26:38
Mattiyu 26:39
Mattiyu 26:40
Mattiyu 26:41
Mattiyu 26:42
Mattiyu 26:43
Mattiyu 26:44
Mattiyu 26:45
Mattiyu 26:46
Mattiyu 26:47
Mattiyu 26:48
Mattiyu 26:49
Mattiyu 26:50
Mattiyu 26:51
Mattiyu 26:52
Mattiyu 26:53
Mattiyu 26:54
Mattiyu 26:55
Mattiyu 26:56
Mattiyu 26:57
Mattiyu 26:58
Mattiyu 26:59
Mattiyu 26:60
Mattiyu 26:61
Mattiyu 26:62
Mattiyu 26:63
Mattiyu 26:64
Mattiyu 26:65
Mattiyu 26:66
Mattiyu 26:67
Mattiyu 26:68
Mattiyu 26:69
Mattiyu 26:70
Mattiyu 26:71
Mattiyu 26:72
Mattiyu 26:73
Mattiyu 26:74
Mattiyu 26:75
Mattiyu 1 / Matt 1
Mattiyu 2 / Matt 2
Mattiyu 3 / Matt 3
Mattiyu 4 / Matt 4
Mattiyu 5 / Matt 5
Mattiyu 6 / Matt 6
Mattiyu 7 / Matt 7
Mattiyu 8 / Matt 8
Mattiyu 9 / Matt 9
Mattiyu 10 / Matt 10
Mattiyu 11 / Matt 11
Mattiyu 12 / Matt 12
Mattiyu 13 / Matt 13
Mattiyu 14 / Matt 14
Mattiyu 15 / Matt 15
Mattiyu 16 / Matt 16
Mattiyu 17 / Matt 17
Mattiyu 18 / Matt 18
Mattiyu 19 / Matt 19
Mattiyu 20 / Matt 20
Mattiyu 21 / Matt 21
Mattiyu 22 / Matt 22
Mattiyu 23 / Matt 23
Mattiyu 24 / Matt 24
Mattiyu 25 / Matt 25
Mattiyu 26 / Matt 26
Mattiyu 27 / Matt 27
Mattiyu 28 / Matt 28