A A A A A
×

Hausa Bible 2013

Mattiyu 20

1
“Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yǎ yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa.
2
Ya yarda yǎ biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.
3
“Wajen saʼa ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome.
4
Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’
5
Saboda haka suka tafi. “Ya sāke fita a saʼa ta shida da kuma saʼa ta tara, ya sāke yin haka.
6
Wajen saʼa ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’
7
“Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ “Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’
8
“Saʼad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira maʼaikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara da waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’
9
“Maʼaikatan da ka ɗauka wajen saʼa ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda.
10
Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda.
11
Saʼad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar.
12
Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin saʼa ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’
13
“Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba?
14
Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka.
15
Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’
16
“Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.”
17
To, da Yesu yana haurawa zuwa Urushalima, sai ya ja almajiran nan goma sha biyu gefe, ya ce musu,
18
“Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa
19
za su kuma bashe shi ga Alʼummai su yi masa baʼa, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”
20
Sai mahaifiyar ʼyaʼyan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ʼyaʼyanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yǎ yi mata wani abu.
21
Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?” Ta ce, “Ka sa daga cikin ʼyaʼyan nan nawa biyu, ɗaya yǎ zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.”
22
Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?” Suka amsa, “Za mu iya.”
23
Yesu ya ce musu, “Hakika za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”
24
Da goman suka ji haka, sai suka yi fushi da ʼyanʼuwan nan biyu.
25
Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Alʼummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko.
26
Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yǎ zama bawanku,
27
kuma duk mai son zama shugaba, dole yǎ zama bawanku,
28
kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yǎ yi bauta, yǎ kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
29
Saʼad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi.
30
Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”
31
Mutane suka tsauta musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”
32
Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”
33
Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.”
34
Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.
Mattiyu 20:1
Mattiyu 20:2
Mattiyu 20:3
Mattiyu 20:4
Mattiyu 20:5
Mattiyu 20:6
Mattiyu 20:7
Mattiyu 20:8
Mattiyu 20:9
Mattiyu 20:10
Mattiyu 20:11
Mattiyu 20:12
Mattiyu 20:13
Mattiyu 20:14
Mattiyu 20:15
Mattiyu 20:16
Mattiyu 20:17
Mattiyu 20:18
Mattiyu 20:19
Mattiyu 20:20
Mattiyu 20:21
Mattiyu 20:22
Mattiyu 20:23
Mattiyu 20:24
Mattiyu 20:25
Mattiyu 20:26
Mattiyu 20:27
Mattiyu 20:28
Mattiyu 20:29
Mattiyu 20:30
Mattiyu 20:31
Mattiyu 20:32
Mattiyu 20:33
Mattiyu 20:34
Mattiyu 1 / Matt 1
Mattiyu 2 / Matt 2
Mattiyu 3 / Matt 3
Mattiyu 4 / Matt 4
Mattiyu 5 / Matt 5
Mattiyu 6 / Matt 6
Mattiyu 7 / Matt 7
Mattiyu 8 / Matt 8
Mattiyu 9 / Matt 9
Mattiyu 10 / Matt 10
Mattiyu 11 / Matt 11
Mattiyu 12 / Matt 12
Mattiyu 13 / Matt 13
Mattiyu 14 / Matt 14
Mattiyu 15 / Matt 15
Mattiyu 16 / Matt 16
Mattiyu 17 / Matt 17
Mattiyu 18 / Matt 18
Mattiyu 19 / Matt 19
Mattiyu 20 / Matt 20
Mattiyu 21 / Matt 21
Mattiyu 22 / Matt 22
Mattiyu 23 / Matt 23
Mattiyu 24 / Matt 24
Mattiyu 25 / Matt 25
Mattiyu 26 / Matt 26
Mattiyu 27 / Matt 27
Mattiyu 28 / Matt 28