A A A A A
×

Hausa Bible 2013

Mattiyu 2

1
Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima
2
suka tambaya, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”
3
Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai shi da dukan Urushalima suka damu.
4
Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi.
5
Suka amsa suka ce, “A Betlehem a Yahudiya, gama ga abin da annabi ya rubuta:
6
“ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda, ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba, gama daga cikinki mai mulki zai zo, wanda zai zama makiyayin mutanena Israʼila.’ ”
7
Sai Hiridus ya kira Masanan a ɓoye, yǎ gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana.
8
Sai ya aike su Betlehem, ya ce, “Ku je ku bincika a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.”
9
Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake.
10
Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai.
11
Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Saʼan nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.
12
Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.
13
Bayan sun tafi, sai malaʼikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku tsere zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yǎ kashe.”
14
Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar,
15
inda zai zauna sai mutuwar Hiridus. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi cewa, “Daga Masar na kirawo ɗana.”
16
Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ʼyan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan.
17
Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa:
18
“An ji murya a Rama, tana kuka da makoki mai tsanani, Rahila ce take kuka domin ʼyaʼyanta, an kāsa taʼazantar da ita, don ba su.”
19
Bayan Hiridus ya mutu, sai malaʼikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki a Masar,
20
ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku tafi ƙasar Israʼila, domin waɗanda suke nema su kashe yaron sun mutu.”
21
Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa suka tafi ƙasar Israʼila.
22
Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wand ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi mafarki, sai ya janye zuwa gundumar Galili,
23
ya je ya zauna a wani garin da ake kira Nazaret. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa: “Za a ce da shi Banazare.”
Mattiyu 2:1
Mattiyu 2:2
Mattiyu 2:3
Mattiyu 2:4
Mattiyu 2:5
Mattiyu 2:6
Mattiyu 2:7
Mattiyu 2:8
Mattiyu 2:9
Mattiyu 2:10
Mattiyu 2:11
Mattiyu 2:12
Mattiyu 2:13
Mattiyu 2:14
Mattiyu 2:15
Mattiyu 2:16
Mattiyu 2:17
Mattiyu 2:18
Mattiyu 2:19
Mattiyu 2:20
Mattiyu 2:21
Mattiyu 2:22
Mattiyu 2:23
Mattiyu 1 / Matt 1
Mattiyu 2 / Matt 2
Mattiyu 3 / Matt 3
Mattiyu 4 / Matt 4
Mattiyu 5 / Matt 5
Mattiyu 6 / Matt 6
Mattiyu 7 / Matt 7
Mattiyu 8 / Matt 8
Mattiyu 9 / Matt 9
Mattiyu 10 / Matt 10
Mattiyu 11 / Matt 11
Mattiyu 12 / Matt 12
Mattiyu 13 / Matt 13
Mattiyu 14 / Matt 14
Mattiyu 15 / Matt 15
Mattiyu 16 / Matt 16
Mattiyu 17 / Matt 17
Mattiyu 18 / Matt 18
Mattiyu 19 / Matt 19
Mattiyu 20 / Matt 20
Mattiyu 21 / Matt 21
Mattiyu 22 / Matt 22
Mattiyu 23 / Matt 23
Mattiyu 24 / Matt 24
Mattiyu 25 / Matt 25
Mattiyu 26 / Matt 26
Mattiyu 27 / Matt 27
Mattiyu 28 / Matt 28